06
Oct
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara tana cigaba da samun koma baya, yayin da wasu manyan 'ya'yanta guda uku suka fice daga jam'iyyar. Waɗanda suka yi murabus din sune Hon. Shehu Muhammed Faru, tsohon Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Moyi Aliyu Abbas, Sardaunan Magami, da Hon. Ishaka Abubakar (Dan Ila Mai Lemu) Gora. A cikin takardar murabus mai ɗauke da ranar 6 ga Oktoba, 2026, mutanen uku sun sanar da matakin su na ficewa daga jam'iyyar APC nan take. A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa a harkar…
