12
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya gargaɗi Nafiu Bala, shugaban wani ɓangare na jam’iyyar ADC, cewa matakansa na iya kawo illa ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Jaridar TheCable ta rawaito cewa Kwankwaso, wanda ya koma ADC daga NNPP a watan Maris 2026, ya bayyana haka ne yayin wata hira, inda ya ce ya gayyaci Bala domin sasanta rikicin jam’iyyar amma bai halarci ganawar ba. Jam’iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci tun 2025, inda ɓangarorin Bala da na Daɓid Mark ke iƙirarin shugabanci, lamarin da ya kai ga kotu da kuma INEC soke amincewa da ɓangarorin biyu.…
