ukarofi

12572 Posts
Sheikh Abduljabbar ya nemi kotu ta dawo da shi Kano daga Gidan Yarin Kuje 

Sheikh Abduljabbar ya nemi kotu ta dawo da shi Kano daga Gidan Yarin Kuje 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, wanda aka yanke wa hukuncin kisa kan ɓatanci ga Manzon Allah (SAW), ya shigar da sabon korafi yana neman a dauke shi daga Gidan Yarin Kuje da ke Abuja a mayar da shi gidan yarin Kurmawa da ke Kano. A cikin takardar korafi da aka shigar gaban Kotun Daukaka Kara, reshen Jihar Kano, mai dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, Abduljabbar Kabara ya ce tsare shi Abuja ya hana shi samun muhimman takardun shari’a da yake bukata wajen daukaka kara. Ya bayyana cewa takardun, wadanda suka haura shafuka…
Read More
Gwamnatin Nijeriya za ta kashe biliyan 135 kan shari’o’in bayan zaɓen 2027

Gwamnatin Nijeriya za ta kashe biliyan 135 kan shari’o’in bayan zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Nijeriya ta ware naira biliyan 135.22 domin shari’o’in da suka shafi bayan zaɓen 2027. Wannan buƙatar na daga cikin abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar tarayyar ƙasar a ranar 31 ga watan Maris, 2026 a lokacin da aka karɓi rahoton kasafin kuɗin 2026. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, gwamnatin ƙasar ta sanya wannan buƙatar a cikin kasafin kuɗin, inda suke cikin rukunin kuɗaɗen da ake kashewa na ko ta kwana, amma ba a alaƙanta su da ko wace ma'aikata ko hukuma ba. Masana tattalin arziki da shari’a sun bayyana cewa irin…
Read More
JUSUN: Tattaunawa ce mafita, ba yajin aiki ba — Dan Marayan Judiciary

JUSUN: Tattaunawa ce mafita, ba yajin aiki ba — Dan Marayan Judiciary

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Daya daga cikin masu neman kujerar Mataimakin Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a ta ƙasa (JUSUN), reshen Jihar Kano, Said Idris Maiturare, wanda aka fi sani da “Dan Marayan Judiciary”, ya bayyana cewa tattaunawa ce hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin ma’aikata, maimakon shiga yajin aiki. Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a yammacin ranar Alhamis, inda ya ce idan aka ba shi dama, zai fifita tattaunawa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin ma’aikata. A cewarsa, “Ni a ra’ayina, duk…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin kai hari a hanyar Sabuwa zuwa Kaya

‘Yan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin kai hari a hanyar Sabuwa zuwa Kaya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Bayani ya nuna cewa 'yan bindigan sun tare matafiya a babban hanyar a ƙauyen Liman da ke ƙaramar hukumar Sabuwa. Jami'an tsaron sun samu nasarar ƙubutar da mutanen da yan bindigan su kai garkuwa da su. Kamar yadda bayani ya nuna jami'an tsaron sun yi wa ƙauyen Liman ƙawanya a yayin da suke gudanar da binciken gano yan ta'addan da suka aikata wannan ɓarna da maido da zaman lafiya a yankin.
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta kafa cibiyar CNG a Katsina

Gwamnatin Tarayya za ta kafa cibiyar CNG a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na kafa cibiyar iskar gas (CNG) a kan hanyar Funtua–Gusau cikin garin Funtua a jihar Katsina, a wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi mai tsafta da kuma inganta harkokin sufuri mai ɗorewa a Arewacin Najeriya. Shugaban hukumar shirin shugaban ƙasa kan CNG da motoci masu amfani da lantarki, Presidential Initiative on CNG and EVs (PiCNG & EVs), Barrista Ismaeel Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da tawagarsa ta kai wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a gidan gwamnatin Jihar Katsina. An tsara…
Read More
Kwankwaso jagora ne na samun nasara — Shugaban ADC na Kano

Kwankwaso jagora ne na samun nasara — Shugaban ADC na Kano

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Jihar Kano, Hon. Haruna Musa Ungoggo, ya bayyana cewa sun gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya shiga jam’iyyar, ganin cewa ya dace da manufofinta kuma jagora ne mai kawo nasara. Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai, inda ya ce Kwankwaso na da kwarewa da hangen nesa a fannonin tsaro, ilimi, noma da sauran bangarori na ci gaban al’umma. A cewarsa, “Kwankwaso jagora ne da ke kawo nasara a kowace jam’iyya. ADC ma tamkar gidansa ne, domin manufofinsa sun yi daidai da na jam’iyyar.”…
Read More
Har yanzu burin Tinubu samar da tsaro ne a Nijeriya – Idris

Har yanzu burin Tinubu samar da tsaro ne a Nijeriya – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fadar Shugaban ƙasa ta nanata cewa batun tsaro na da kan gaba cikin muhimman abubuwan da shugaba Tinubu ke bai wa muhimmanci a yayin da fadar shugaban ƙasa ke ƙara tattaunawa da hukumomin tsaro da abokan hulɗa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan zama da shugaban ƙasa a ranar Lahadi a ranar Lahadi. Ya kuma ce shugaban ƙasa na bai wa duk wani yunƙuri na “ƙwaf ɗaya” domin warware tsaro muhimmanci. A cewar Idris, shugaban ƙasa ya dawo…
Read More
Kwalejin fasaha ta tarayya ta Ƙaura Namoda ta yaye ɗalibai 1,450

Kwalejin fasaha ta tarayya ta Ƙaura Namoda ta yaye ɗalibai 1,450

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara ta yaye ɗalibai 1,450 da aka ɗauka da za su karanci Diploma ta ƙasa da babbar diploma ta ƙasa daban-daban don zaman karatu na shekarar 2025/2026. Shugaban kwalejin Dr. Aminu Yusuf ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai a ƙarshen bikin kammala. An gudanar da bikin a babbar harabar kwalejin da ke garin Ƙaura Namoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a yau Juma'a. Ya jaddada cewa wasu daga cikin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancinsa sun haɗa…
Read More
INEC ta ɗage sabunta bayanan masu kaɗa kuri’a sai bayan zaɓen 2027

INEC ta ɗage sabunta bayanan masu kaɗa kuri’a sai bayan zaɓen 2027

Daga USMAN KAROFI Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da ɗage aikin sabunta bayanan masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar nan zuwa bayan kammala zaɓen gama gari na shekarar 2027. Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin wata takarda da kwamishinan ƙasa kuma ahugaban kwamitin yaɗa labarai da Ilimantar da masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar a ranar Juma’a. A cewar sanarwar, an cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da hukumar ta gudanar tare da Kwamishinonin zaɓe na Jihohi (RECs) a ranar 10 ga Afrilu, 2026, inda aka tattauna batutuwan zaɓe ciki har da wannan…
Read More
Matan gwamnonin Arewa sun sha alwashin kawo sauyi a yankin

Matan gwamnonin Arewa sun sha alwashin kawo sauyi a yankin

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Matan gwamnonin Arewa sun gudanar da taronsu na farko na kwata-kwata a ranar 10 ga Afrilu, 2026, a fadar gwamnatin Jihar Zamfara. Taron, wanda Hajiya Asma'u Inuwa Yahaya, uwargidan gwamnan Jihar Gombe ta jagoranta, ya tattaro matan gwamnonin Arewa domin tattauna shirye-shiryen da aka tsara don inganta walwalar mata, yara, da kuma ƙungiyoyi masu rauni. Wani ɓangare na shawarwarin da aka cimma a ƙarshen taronsu a cikin wata sanarwa ya haɗa da, Ci gaba da aikin haƙa rijiyoyin burtsatse don magance ƙalubalen matsalar ruwan sha tsaftatattce, ƙaddamar da sabin ayyukan tallafawa alumma a 2026. Sauran…
Read More