ukarofi

12572 Posts
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yaba wa shirye-shiryen cigaban Zamfara

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yaba wa shirye-shiryen cigaban Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Mataimakiyar Sakatare Janar a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Amina Mohammed, ta ce Jihar Zamfara a buɗe take kuma mai sauƙin shiga, kuma Majalisar Dinkin Duniya tana son zama abokiyar hulɗa da gaske ga Jihar. Mataimakiyar Sakatare Janar ta MDD ta yi wannan tsokaci ne yayin da ta kai ziyara a Jihar ta Zamfara a ranar Alhamis. Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta lura cewa Mataimakiyar Sakatare Janar ta gudanar da wani bincike a wurin a ƙaramar hukumar Maru da sauran wurare. Sanarwar ta ƙara da cewa…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da kayayyakin wasanni ga ɗalibai masu buƙata ta musamman

Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da kayayyakin wasanni ga ɗalibai masu buƙata ta musamman

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da kayayyakin wasanni domin inganta harkokin wasanni, motsa jiki da kuma bunƙasa hazakar ɗaliban makarantu masu buƙata ta musamman a faɗin jihar. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ɗakin taro na filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina. Babban sakataren ma’aikatar matasa da wasanni, Alhaji Muhammad, ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne a ƙoƙarin gwamnati na bai wa dukkan yara damar nuna ƙwarewarsu, musamman masu buƙata ta musamman. Ya ƙara da cewa samar da kayayyakin zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar ɗaliban tare da ba su damar bunƙasa…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kammala bada horo na kwanaki uku ga ma’aikatan jihar

Gwamnatin Katsina ta kammala bada horo na kwanaki uku ga ma’aikatan jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya rufe taron na kwanaki uku da aka shirya wa ma’aikatan gwamnatin jihar domin ƙara musu ƙwarewa a harkokin gudanar da aiki. Da yake jawabi wajan rufe taron,shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa wannan horo wani muhimmin ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Jihar Katsina na inganta tsarin gudanar da ayyukan gwamnati tare da ƙara wa ma’aikata ƙwarewa da nagarta a aikinsu. Ya jaddada cewa horon zai taimaka wajen samar da ingantaccen aiki, gaskiya da riƙon amana a ofisoshin gwamnati. Alhaji Falalu Bawale ya kuma yaba wa ma’aikatan da…
Read More
Sanata Marafa ya koma ADC

Sanata Marafa ya koma ADC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sanata Kabir Garba Marafa ya shiga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, a matsayin wani ɓangare na tafiyarsa ta siyasa don tsayawa takarar kujerar gwamna a Zamfara a shekarar 2027. Ya yi kira ga magoya bayansa da su yi rijista da jam'iyyar.Shiga Jam'iyyar ta ADC da Sanatan ya yi ta haifar da sha'awa sosai, inda magoya baya da yawa suke yin gaggawar yin rijista da Jam'iyyar ta ADC a Jihar Zamfara gabanin zaɓen da ke tafe. A cewar Shugaban ƙungiyar magoya bayan Sanata Marafa, Alh. Surajo Garba Maikatako, Marafa ya jaddada muhimmancin zama memba…
Read More
Tarihi: Yadda wasu manyan ƙungiyoyi 10 suka faɗi suna daf da lashe kofuna uku

Tarihi: Yadda wasu manyan ƙungiyoyi 10 suka faɗi suna daf da lashe kofuna uku

Tarihin ƙwallon ƙafa ya cika da lokutan da ƙungiyoyi suka fara kakar wasa da burin samun ɗaukaka, amma daga ƙarshe suka ƙare cikin takaici da baƙin ciki. Ga manyan ƙungiyoyin duniya, neman lashe kofuna biyu (Double), uku (Treble), ko ma huɗu (ƙuadruple) shi ne babban gwaji na ƙarfi, juriya da tsari. Amma tarihi ya nuna cewa, yadda hawa ƙololuwa ke da wahala, haka fa faɗuwa daga can ke zama mai raɗaɗi. A halin yanzu, wannan gaskiya na bayyana a filin wasan Arsenal. Rahotanni sun nuna cewa kakar wasan 2025/2026 ta ƙungiyar ta shiga wani mawuyacin hali, inda burinsu na lashe…
Read More
FIFA na nazarin faɗaɗa gasar Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64 domin bikin cikarta shekara 100

FIFA na nazarin faɗaɗa gasar Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64 domin bikin cikarta shekara 100

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), ta tabbatar da cewa tana duba wani shiri da aka gabatar na faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2030 zuwa ƙasashe 64, a wani yunƙuri na bikin cika shekara 100 da fara gasar. Rahotanni sun nuna cewa wannan ra’ayi ya samo asali ne daga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Uruguay, Ignacio Alonso, a wani taron majalisar FIFA da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2025. Daga bisani, ƙungiyar ƙasashen Kudancin Amurka ta CONMEBOL ta gabatar da wannan shawara a hukumance, inda shugabanta Alejandro Domínguez ya bayyana cewa hakan zai bai wa duk…
Read More
Neymar ya nemi afuwa bisa cewa alƙalin wasa tana al’ada

Neymar ya nemi afuwa bisa cewa alƙalin wasa tana al’ada

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil, Neymar, ya fuskanci suka mai tsanani daga jama’a da masoya wasanni bayan furucin da ya yi game da alƙalin wasa bayan kammala wasa tsakanin ƙungiyarsa ta Santos da Remo, wanda ya ƙare da ci 2-0. Rahotanni sun bayyana cewa Neymar ya nuna rashin jin daɗinsa ga alƙalin wasa, Savio Sampaio, bayan da aka ba shi katin gargaɗi sakamakon ƙorafi da ya yi kan wani mummunan bugun da ɗan wasan hamayya, Diego Hernandez, ya yi masa. A ƙarshen wasan, Neymar ya yi yunƙurin yaudarar alƙalin wasa yayin bugun freekick, abin da ya sa Hernandez…
Read More
Gwamna Abba na tsaka mai wuya akan naɗin mataimakin gwamnan Kano – Rahoto

Gwamna Abba na tsaka mai wuya akan naɗin mataimakin gwamnan Kano – Rahoto

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, na fuskantar ƙalubalen siyasa mai ƙarfi dangane da zaɓen sabon mataimakin gwamna, yayin da rikici ke ƙaruwa a cikin Jam’iyyar APC gabanin ganawarsa da ‘yan majalisar jihar a fadar gwamnati a daren Litinin. Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da gwamnan ya kai a makon da ya gabata zuwa Abuja domin ganawa da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje, matakin da majiyoyi suka ce an ɗauka ne domin ƙarfafa alaƙa da manyan jiga-jigan jam’iyyar. Majiyoyin daga jam’iyyar sun shaidawa Daily Nigerian cewa Ganduje da fadar shugaban ƙasa na goyon bayan tsohon kwamishinan…
Read More
Rabon shinkafa da taliya ba za su sa ka ci zaɓen 2027 ba – Atiku ga Tinubu 

Rabon shinkafa da taliya ba za su sa ka ci zaɓen 2027 ba – Atiku ga Tinubu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa raba buhunan shinkafa da taliya ba zai taimaka wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba a zaɓen 2027.   A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja ranar Talata, Atiku ya ce dimokuraɗiyyar Nijeriya tana ta raunana sakamakon tattara ƙarfin iko da gwamnatin Tinubu ke yi. Sanarwar ta ce a daidai lokacin da gwamnoni sama da 30 suka shiga cikin jam’iyyar mai mulki, abin da ake tsammani shi ne buɗaɗɗiyar siyasa da gasa ta…
Read More
Hawan jini: NAFDAC na shirin taƙaita gishiri a abincin da ake sarrafawa

Hawan jini: NAFDAC na shirin taƙaita gishiri a abincin da ake sarrafawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), na shirin kafa dokoki domin rage yawan sinadarin gishiri a cikin abincin da ake sarrafawa da kuma wanda aka riga aka shirya a masana’antu, bayan da jami’ai suka bayyana cewa ’yan Nijeriya na cin gishiri fiye da adadin da ƙa’idojin duniya suka amince da shi. Babbar Daraktar Hukumar, Mojisola Adeyeye, ta bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar kan daftarin dokar rage gishiri a abinci na shekarar 2026, inda ta jaddada cewa yawan amfani da gishiri na daga cikin manyan…
Read More