10
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi watsi da iƙirarin da ake yi na cewa wai Nijeriya na daf da rugujewa, yana mai jaddada cewa ƙasar tana nan daram kuma tana samun cigaba mai ɗorewa. Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a lokacin Babban Taron ƙasa na 81 da Taron Shekara-shekara na 23 na ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Nijeriya (BON). Ya ce: “Ba gaskiya ba ne cewa Nijeriya na daf da rugujewa. A maimakon haka, muna ci gaba da nuna juriya tare da ɗaukar…
