ukarofi

12572 Posts
Rikicin ADC: Bangaren Nafiu Bala ya yi zanga-zangar neman INEC ta amince da shi

Rikicin ADC: Bangaren Nafiu Bala ya yi zanga-zangar neman INEC ta amince da shi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rikicin shugabanci da yake addabar jam’iyyar adawa ta ADC ya ƙara ɗaukar sabon salo a ranar Alhamis, yayin da wani ɓangare ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya gudanar da zanga-zanga a hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ke Abuja, inda suka nemi a amince da shugabancinsa a hukumance. Rahotanni sun nuna cewa Nafiu Gombe, tare da haɗin gwiwar ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Kogi, Leke Abejide, da ɗaruruwan magoya baya, sun zargi ɓangaren da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark ke jagoranta da yunƙurin ƙwace ikon jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba,…
Read More
Sauya sheƙa: Gwamna Bala ya gana da shugabannin APC na Bauchi a Abuja

Sauya sheƙa: Gwamna Bala ya gana da shugabannin APC na Bauchi a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Laraba ya karɓi bakuncin mambobin jam’iyyar APC da ke Majalisar Wakilai daga jihar, a wani mataki da ake ganin yana da alaƙa da sauye-sauyen siyasa da ke gudana a halin yanzu. Rahotanni sun bayyana cewa taron ya gudana ne a gidan gwamnan da ke Abuja, a daidai lokacin da ake ƙara jin rade-radin cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP. Da yake magana da ‘yan jarida bayan taron, Dabo Ismail, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Toro, ya bayyana cewa gwamnan ne ya gayyace su domin tattauna…
Read More
Fadar Shugaban ƙasa ta warware shakku kan shirin biyan bashin tiriliyan N3.3 ga kamfanonin lantarki

Fadar Shugaban ƙasa ta warware shakku kan shirin biyan bashin tiriliyan N3.3 ga kamfanonin lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan cece-kuce da suka taso bayan amincewar da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na shirin biyan bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya na kusan Naira tiriliyan 3.3 ga kamfanonin samar da wutar lantarki, wato GenCos. A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an tsara wannan shiri ne domin warware matsalolin kuɗi da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki, tare da tabbatar da daidaito da inganta samar da wuta a ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta bayyana…
Read More
An samu hare-haren bom 1,934 a Arewa cikin shekaru bakwai – Bincike

An samu hare-haren bom 1,934 a Arewa cikin shekaru bakwai – Bincike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni sun nuna cewa yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya na ci gaba da fuskantar babbar barazana daga hare-haren bom, inda aka rubuta jimillar hare-hare 1,934 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024. Binciken da aka fitar a cikin rahoton '2025 Nigeria Mine Action Reɓiew' ya bayyana cewa mafi yawan hare-haren sun kasance ne ta hanyar dasa bama-bamai a kan hanyoyi, wato IEDs, wanda ya zama ruwan dare fiye da sauran hanyoyin kai hari. A cewar rahoton, irin waɗannan bama-bamai na kan hanyoyi sun kasance mafi hatsari kuma mafi yawan faruwa a tsawon shekaru bakwai da aka nazarta, abin…
Read More
Yawan man da Nijeriya ke haƙowa ya ƙaru saboda ingantuwar tsaro – NNPC

Yawan man da Nijeriya ke haƙowa ya ƙaru saboda ingantuwar tsaro – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya ce, yawan da Nijeriya ke samarwa ya ƙaru zuwa aƙalla ganga miliyan 1.7 a kullum. Wannan ya nuna ci gaban da aka samu daga shekarar 2022. NNPC ya alakanta ci gaban da aka samu da inganta tsaron bututun man fetur da kuma ƙoƙarin yaƙi da masu satar mai da lalata bututun mai a yankin Neja Delta. A yayin da yake magana a wani zaman tattaunawa game da samar da tsaro kan bututun man fetur ɗin Nijeriya da aka yi a majalisa a Abuja, shugaban kamfanin man fetur…
Read More
Farashin fetur ya faɗi da kashi 15 sakamakon tsagaita wutar Amurka da Iran

Farashin fetur ya faɗi da kashi 15 sakamakon tsagaita wutar Amurka da Iran

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Farashin man fetur ya faɗi da kusan kashi 15 a ranar Laraba, bayan sanar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Amurka da Iran, wadda ake ganin za ta buɗe ƙofar tattaunawa domin rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya. Farashin Brent ya sauka ƙasa da dala $100 a kowace ganga a kasuwannin duniya da misalin ƙarfe 12:00 na dare (GMT), bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu da Iran, da sharadin cewa za a buɗe mashigar ruwa ta Hormuz gaba ɗaya. Bayan…
Read More
2027: Babu shirin maida APC ita kaɗai a takarar zaɓe – Fadar Shugaban ƙasa

2027: Babu shirin maida APC ita kaɗai a takarar zaɓe – Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mai bai wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya yi watsi da zargin da jam’iyyun adawa ke yi cewa jam’iyyar APC na ƙoƙarin zama ita kaɗai za a gani a takardar zaɓen 2027. Dare ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa babu wani shiri—na ɓoye ko na fili—da nufin takaita zaɓe ga jam’iyyar APC kaɗai. “Babu wani tsari, ko a ɓoye ko a fili, na sanya APC…
Read More
BON ta karrama Gwamnan Zamfara da lambar yabo a fannin ababen more rayuwa

BON ta karrama Gwamnan Zamfara da lambar yabo a fannin ababen more rayuwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar kula da kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (BON), ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara a Fannin Ababen More Rayuwa,” sakamakon gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu musamman a shirin sabunta birane a faɗin jihar. An miƙa wa gwamnan wannan babbar karramawa ne a yayin bugu na biyu na taron BON da aka gudanar a cibiyar taro ta NAF Conference Centre da ke birnin Abuja, inda manyan mutane daga sassa daban-daban suka halarta. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya…
Read More
Matatar Dangote ta rage farashin fetur bayan sauyin kasuwar ɗanyen mai

Matatar Dangote ta rage farashin fetur bayan sauyin kasuwar ɗanyen mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin fetur daga ma’aunin sayarwa, inda ta sauke farashin zuwa Naira 1,200 kan kowace lita daga Naira 1,275 da aka sanar a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026. Sabon mataki na rage farashi ya zo ne kwana guda kacal bayan ƙarin Naira 75 da aka yi a baya, wanda ya kai kusan ƙarin kashi 5.02 cikin 100. Matatar ta bayyana cewa sauyin ya biyo bayan canje-canjen da ake samu a kasuwar ɗanyen mai ta duniya. Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa matatar ta ƙara farashin man dizal da…
Read More
A guji karɓar rance daga manhajojin bayar da lamuni

A guji karɓar rance daga manhajojin bayar da lamuni

A cikin shekarun baya-bayan nan, karɓar bashi ta hanyar manhajojin yanar gizo ya zama ruwan dare a Nijeriya, musamman a tsakanin matasa da masu sana’o’i. Duk da ƙorafe-ƙorafe da ake yawan ji kan tsananin ruwa da kuma matsin lamba daga masu ba da lamunin, har yanzu mutane da dama na ci gaba da rungumar wannan hanya domin warware matsalolin rayuwa na gaggawa. Wannan lamari na nuna cewa akwai babbar matsala da ke buƙatar a duba ta da idon basira. Babu shakka, bunƙasar harkar fasahar kuɗi, wato fintech, ta kawo sauƙi wajen samun bashi cikin sauri. Amma a gefe guda, wannan…
Read More