10
Apr
Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Katsina ta kammala shirye-shiryen gudanar da auren gata na farko ga amare da angwaye 2,000 da aka zaƙulo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar. Kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta ce idan komai ya tafi daidai, za a gudanar da auren gatan na farko a Jihar Katsina a ranar 25 ga Afrilu, 2026. A yayin wani taron horaswa kan rayuwa da kuma shawarwari da aka shirya wa masu cin gajiyar shirin, shugabar gidauniyar tallafin aure ta al’usra, Malama Murja Ibrahim Duwan, ta bayyana cewa horon na nufin bai wa…
