08
Apr
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya tallafawa mutanen da hare haren 'yan bindiga ya shafa a garin Sayaya a ƙaramar hukumar Matazu da Naira miliyan 31. Da yake miƙa tallafin kuɗin ga mutanen da harin ya shafa , Gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya sami wakilcin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Abdulkadir Nasir Andaje ya ce ba wai ƙudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyar al'umma ba har da taimakawa mutanen da hare haren ya shafa domin rage raɗaɗi. Andaje ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya sami bayanin hare haren 'yan bindiga a yankin bayan dawowarsa…
