07
Apr
Ku karanta wannan wasiƙa cikin natsuwa. Wannan wasiƙa ce ga duk wani mutum — ko da ma’aikaci ne, ko malami, ko limami, ko ɗan kasuwa, ko jami’in gwamnati, ko ɗan siyasa — wanda ya zama mai neman mata, musamman matan aure, ta hanyoyi marasa daraja: ta hanyar yaudara, amfani da matsayin addini, amfani da iko, turo saƙonni marasa kyau, neman hotuna, ko karya amana. Wannan wasiƙa ba wai ta nuna-hannu ce ga mutum guda ba; kira ce ga al’umma baki ɗaya da kuma gargaɗi ga masu irin wannan hali su daina nan take, su gyara, ko su fuskanci sakamakon abin…
