06
Apr
"Jarumta ba ta da jinsi, kishin ƙasa ne ke bayyana ta" Daga AISHA ASAS A tarihi mata ba su da yawa da aka rubuta su da sunan jarumai da suka yi namijin ƙoƙari wurin fitar da al'umma daga wani ƙunci da suke ciki ta ƙarfin tuwo, masu kishin ƙasa da suka sadaukar da rayuwarsu don samar wa ƙasarsu damar walwala da 'yanci. Sai dai daga kaɗan da ake samun su a wannen fage sukan yi ƙoƙari na ban mamaki da har za a fara tunanin anya mace ce ta yi hakan. Wannan zai sa ba ɓata lokaci za su samu…
