05
Apr
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙungiyar Makiyaya ta Nijeriya, wato Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 30 a birnin Jos na Jihar Filato, tare da gargaɗin masu amfani da kalamai masu tunzura jama’a. Shugaban ƙungiyar, Baba Othman-Ngelzarma, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan lamari mai muni wani sabon tunatarwa ne na yadda zubar da jini ke ci gaba da addabar jihar. Ya bayyana cewa irin wannan tashin hankali bai kamata a bar shi ya ci gaba ba, yana mai jajantawa…
