ukarofi

12575 Posts
Yadda sulhun da Pantami ya yi tsakanin El-Rufai da Uba Sani ya janyo cece-kuce

Yadda sulhun da Pantami ya yi tsakanin El-Rufai da Uba Sani ya janyo cece-kuce

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan Nijeriya na ci gaba da tafka muhawara musamman a shafukan sada zumunta game da sulhu da fitaccen malamin Addinin Musulunci Sheikh Ali Isa Pantami ya yi wa El-Rufai da Uba Sani. Al'amarin ya ɗauki hankalin mutane da dama musamman waɗanda ke bibiyar abubuwan da suka shiga tsakanin tsohon gwamna da gwamnan jihar na yanzu. Mutanen biyu dai sun jima ba sa ga maciji da juna, sakamakon rashin jituwa da ta shiga tsakaninsu, jim kaɗan bayan saukar El-Rufai daga mulkin jihar Kaduna. Malamin ya yi musu sulhu ne a lokacin jana'izar mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma ranar…
Read More
Tinubu ya naɗa Sanata Ida shugabancin Hukumar CAC

Tinubu ya naɗa Sanata Ida shugabancin Hukumar CAC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Sanata (Dr.) Ibrahim Ida a matsayin Shugaban Hukumar Rijistar Kamfanoni (CAC), tare da gabatar da sunayen wasu mutum bakwai domin cike guraben kwamishinoni a Hukumar ƙidayar Jama’a ta ƙasa. A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Dakta Ibrahim Ida ya kammala digirin digirgir (MSc) a fannin Banking da Kuɗi a Jami’ar Ibadan tun shekarar 1983, sannan ya samu digirin lauya (LLB) daga Jami’ar Abuja a 2003. Kafin shigarsa Majalisar Dattawa a…
Read More
Trump ya sassauta takunkumin mai ga Cuba, ya buɗe ƙofa ga Rasha

Trump ya sassauta takunkumin mai ga Cuba, ya buɗe ƙofa ga Rasha

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya nuna alamar sauya matsayinsa kan hana kai mai zuwa ƙasar Cuba, inda ya bayyana cewa ba shi da wata matsala idan kowace ƙasa ta aika da man fetur zuwa ƙasar, duk da kasancewar wani jirgin mai na Rasha ke daf da isa tashar jiragen ruwa na Cuba. Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin mai na Rasha da aka sanya wa takunkumi, wanda ke cikin abin da ake kira “jiragen inuwa” na ƙasar, yana bakin gabar gabashin Cuba, kuma ana sa ran zai isa tashar jirgin ruwa. Wannan jigilar mai na…
Read More
NELFUND ta musanta jita-jitar ƙarin alawus ga ɗalibai

NELFUND ta musanta jita-jitar ƙarin alawus ga ɗalibai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND) ya bayyana cewa har yanzu alawus na kulawa da rayuwa da ake bai wa ɗalibai masu cin gajiyar shirin yana nan a kan Naira 20,000 a kowane wata, yana mai ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ƙara shi zuwa N25,000. A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren ranar Litinin, wadda Daraktar Sadarwa ta Tsare-tsare ta asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ta sanya wa hannu, NELFUND ya gargaɗi ɗalibai da su yi watsi da duk wani bayani da ya saɓa da wannan, tare da…
Read More
Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da asusun tsaro na Naira biliyan ɗaya a kowane wata

Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da asusun tsaro na Naira biliyan ɗaya a kowane wata

* Sun sake kira ga ‘yan sandan jihohi Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun sake jaddada bukatar yin garambawul cikin harkar tsaro, ƙarfafa haɗin gwiwar yankin, da kuma zuba jari mai ɗorewa domin ci gaba. A wani taro da suka gudanar a Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Northern States Goɓernors’ Forum (NSGF), shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa an samu “ingantaccen ci gaba” a harkar tsaro tun bayan taron da suka yi a watan Disambar 2025. Sai dai ya gargaɗi cewa wannan ci gaba bai kamata ya sa a yi sakaci ba.…
Read More
Nijeriya ta fitar da hanyoyin dogaro da kanta a fannin lafiya, inji Minista

Nijeriya ta fitar da hanyoyin dogaro da kanta a fannin lafiya, inji Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin tarayya ta ce ta ɗauki matakai domin rage dogaro da tallafin kuɗin da ake samu daga ƙasashen waje da ƙarfafa samar da kuɗi a cikin gida da ci gaba da mutunta abokan hulɗa na ƙasashen waje. Muhammed Pate, ministan lafiya da walwalar jama’a, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wurin wani taron tattaunawa na lafiya da ƙasar Sin kan yadda za a shirya wa tunƙarar ɓarkewar annoba. A yayin da yake duba kan irin ƙoƙarin daƙile cutattuka a duniya, Pate ya ce, duk da cewa tallafin ƙasashen waje ya…
Read More
Kotu ta tsare direban matar Sarki Sanusi II kan satar gwala-gwalai na miliyan N60

Kotu ta tsare direban matar Sarki Sanusi II kan satar gwala-gwalai na miliyan N60

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Kotun Majistare da ke Nomansland a ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu kan zargin satar gwala-gwalai da kuɗi da kuma wayar salula.   Masu laifin da ake tuhuma su ne Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini. An gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumar haɗin baki, sata da kuma karɓar kayan sata. Lauyan masu gabatar da ƙara, Barista Abubakar Ibrahim, ya shaida wa kotu cewa Sulaiman Yakubu, wanda shi ne direban matar Sarki…
Read More
Majalisa ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan shida 

Majalisa ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan shida 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Malalisar Dattawa ta amince wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ciyo basin Dala biliyan shida domin rage bashin da ake bin Nijeriya da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa da ke Jihar Legas. Wannan rance zai ƙara yawan bashin da ake bin Nijeriya daga dala biliyan 110.3 zuwa Dala biliyan 115.3. Sauran amfanin da za a yi da kuɗaɗen sun haɗa da ayyukan gine-gine, da kuma cike gibin da aka samu a kasafin kuɗin ƙasar. A ranar Talata Majalisar ta amince da buƙatar ƙasar bayan karanta wasiƙu biyu daban-daban da Shugaban ƙasa ya aika…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da kasafin 2026 ba tare da bincike kan ƙarin buƙatar Tinubu ba

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin 2026 ba tare da bincike kan ƙarin buƙatar Tinubu ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026 a ranar Talata, bayan ƙara Naira tiriliyan 9.3 da Bola Tinubu ya nema, wanda ya kai jimillar kasafin zuwa N68.323 tiriliyan. Baya ga amincewa da buƙatar shugaban ƙasar, majalisar ta ƙara Naira biliyan 623 a kan adadin da aka gabatar, inda aka ɗaga kasafin daga N67.7 tiriliyan zuwa N68.323 tiriliyan. An amince da kasafin ne ta hanyar jefa ƙuri’a ta murya (ɓoice ɓote), inda yawancin sanatoci suka nuna goyon bayansu. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar kasafin bayan kammala ƙuri’ar.…
Read More
Jama’a sun kashe ɓarawon waya a Kano

Jama’a sun kashe ɓarawon waya a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dubun wasu matasa biyu da ake zargi da satar waya ta cika, bayan da taron jama’a ya afka musu a kusa da makarantar Fatima Special Primary School, da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, a gaban ƙofar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano. Shaidu sun ce wata da farko matasan sun far wa wata budurwa da wuka, inda saboda tsoron kada su kai mata hari, ta mika musu wayar salim-alim. Bayan haka, sai suka kai wa wani mutum da ke wucewa hari suka kwace wayarsa. Wannan ne ya jawo hankalin masu wucewa, suka yi ƙarfin hali suka fuskance…
Read More