ukarofi

12572 Posts
Nijeriya ce kan gaba a Afirka wajen ɓarnar abinci – Tarayyar Turai

Nijeriya ce kan gaba a Afirka wajen ɓarnar abinci – Tarayyar Turai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Nijeriya ce ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen ɓarnar abinci, inda ake asarar kusan tan miliyan 38 na abinci a duk shekara, kamar yadda ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bayyana. An bayyana wannan adadi mai tayar da hankali ne yayin bikin ranar Ranar Rage Shara ta Duniya (International Zero Waste Day) da aka gudanar a birnin Abuja, inda masu ruwa da tsaki suka yi kira da a ɗauki matakai cikin gaggawa da haɗin gwiwa domin rage ɓarnar abinci da kuma inganta yadda ake amfani da albarkatu yadda ya kamata. Taron,…
Read More
Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankaɗo ma’aikatan bogi 45,000 ta hanyar BVN

Yadda Gwamnatin Tarayya ta bankaɗo ma’aikatan bogi 45,000 ta hanyar BVN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohuwar Ministar Kuɗi ta Tarayyar Nijeriya, Kemi Adeosun, ta bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta gano dubban ma’aikatan bogi a cikin tsarin albashi, bayan haɗa bayanan Lambar Tantance Asusun Banki (BVN) da tsarin biyan albashi na gwamnati. Ta yi wannan bayani ne yayin wani taron tattaunawa na makarantar shugabanci da aka gudanar a Legas, inda ta yi ƙarin haske kan yadda aka yi amfani da fasaha wajen gyara kura-kurai da suka daɗe suna addabar tsarin biyan albashi na gwamnati. A cewarta, kafin aiwatar da wannan gyara, kuɗin albashi na ma’aikata shi ne mafi girman kaso a kashe-kashen…
Read More
Nijeriya na da damar mamaye kasuwar manja a duniya nan da 2050 – NPPAN

Nijeriya na da damar mamaye kasuwar manja a duniya nan da 2050 – NPPAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Masu Sarrafa Kwakwan Manja ta ƙasa (NPPAN), ta bayyana cewa Nijeriya na da burin kaiwa ga cikakkiyar wadatar manja tare da samun gagarumar kason kasuwar duniya nan da shekarar 2050. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alphonsus Inyang, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NANS) a gefen taron tantance Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa da aka gudanar a Abuja. Ya ce wannan buri zai tabbata ne ta hanyar aiwatar da Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa yadda ya kamata, wanda zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin da…
Read More
Jami’ar Sule Lamiɗo ta yaye ɗalibai 4,109 a karo na biyu tun bayan kafa ta

Jami’ar Sule Lamiɗo ta yaye ɗalibai 4,109 a karo na biyu tun bayan kafa ta

Daga ABUBAKAR M TAHEER Ilimi shine babban abinda Gwamnatin Jigawa take saka hannu jari mafi tsoka inji Gwamna Umar Namadi. Jami'ar Sule Lamido dake Kafin Hausa ta gudanar da taron yaye ɗalibai a karo na biyu tun bayan buɗe jami'arba shekarar 2013. Taro da ya haɗe ɗaliban da suka kammala jami'ar tun daga 2018 zuwa 2025 wanda ya ƙunshi ɗalibai 4,109 a shekaru 6 ya samu halartar manyan yan siyasa, jami'an gwamnatin, Farfesoshi da sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar nan. Da yake gabatar da jawabinsa Gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi Ɗan Modi ya bayyana cewa gwamnatin…
Read More
2027: Masu ruwa da tsaki a APC sun zaɓi Farfesa Sani Haruna a matsayin wanda zai gaji Gwamna Sule

2027: Masu ruwa da tsaki a APC sun zaɓi Farfesa Sani Haruna a matsayin wanda zai gaji Gwamna Sule

Daga JOHN D WADA a Keffi Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Kudancin jihar Nasarawa sun bayyana tsohon shugaban NASENI Farfesa Injiniya Mohammed Sani Haruna a matsayin wanda yafi dacewa ya gaji gwamnan jihar mai barin gado wato Injiniya Abdullahi Sule a zaɓen 2027 dake zuwa. Da yake jawabi a wajen wani babban gangami da masu ruwa da tsakin daga shiyar suka shirya wa Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna a birnin Lafiya wanda ya haɗa gangamin Alhaji Ibrahim Hamza ya bayyana tabbacinsu cewa Farfesa Injiniya Mohamed Sani Haruna shine mafi dacewa da zai gaji gwamna Abdullahi Sule a…
Read More
Cocin Grace Baptist Church Sabon-Gari ya yi bikin cika shekaru 15 a Nasarawa

Cocin Grace Baptist Church Sabon-Gari ya yi bikin cika shekaru 15 a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA Keffi Ɗan takarar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam'iyyar PDP Dr. David Martins Umbugadu ya yaba wa cocin Grace Baptist Church da ke Sabon-gari a karamar hukumar Keffi a jihar dangane da jajircewa wajen yaɗa bisharar Isa Almasihu cikin shekaru 15 da kafuwar cocin. Dr. David Umbugadu ya bayyana haka ne ta bakin wani na kusa dashi maisuna Samurai Danjuma da ya wakilceshi a wajen wani babban bikin cika shekaru 15 da kuma neman tallafin naira miliyan 40 da cocin ya gudanar don kammala aikin gininta wanda aka yi jiya Asabar a cocin. Yace dole ne…
Read More
Kungiyoyi sun gargaɗi gwamnati kan barazanar matsalar tsaro da talauci

Kungiyoyi sun gargaɗi gwamnati kan barazanar matsalar tsaro da talauci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyoyin farar hula (CSO) da dama sun bayyana cewa Nijeriya na daf da faɗawa cikin matsananciyar matsala, inda suka yi kira ga shugabanni da al’umma gaba ɗaya da su tashi tsaye domin ceto ƙasar daga halin da take ciki.  Wannan kira na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka bayyana damuwa kan yadda matsalolin tsaro, talauci da taɓarɓarewar ɗabi’a ke ƙara tsananta a ƙasar. ƙungiyoyin sun ce suna magana ne a matsayin masu kare dimokiraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam da kuma kyakkyawan shugabanci, ba tare da nuna son kai ga wata jam’iyya ba.…
Read More
NANS ta rushe shugabancin ɗalibai a Ogun

NANS ta rushe shugabancin ɗalibai a Ogun

Daga WAKILINMU Kungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta rusa shugabancin ƙungiyar ɗalibai mazauna makarantu ta jihar Ogun sakamakon rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa. NANS ta kuma kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin gudanar da sabon zaɓe cikin kwanaki 30 masu zuwa Matakin ya biyo bayan abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin “bincike mai zurfi, adalci da kuma bin tsarin doka” kan jerin ƙorafe-ƙorafe da suka biyo bayan shugabancin ƙungiyar na tsawon watanni. A cikin wata sanarwa da Shugaban NANS, Olushola Oladoja, ya sanya hannu a ranar Talata ƙungiyar ta ce rikicin ya samo asali ne daga…
Read More
Sule Lamiɗo ya goyi bayan INEC kan rikicin ADC

Sule Lamiɗo ya goyi bayan INEC kan rikicin ADC

* Ya kira Atiku, Obi da Kwankwaso ‘’yan siyasar da suka rasa matsuguni’ Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya goyi bayan matakin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗauka na janye amincewa da shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya bayyana manyan ‘yan adawar da ke alaƙa da jam’iyyar a matsayin “’yan siyasar da suka rasa matsuguni.” Rahotanni sun nuna cewa Lamido ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Dutse,…
Read More
Matasan Yobe sun tara miliyan N188 domin tallafa wa Ahmad Lawan a takarar gwamna

Matasan Yobe sun tara miliyan N188 domin tallafa wa Ahmad Lawan a takarar gwamna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata ƙungiya mai suna Coalition of Yobe-East Progressiɓe Youths ta tara jimillar Naira miliyan 188 domin tallafawa burin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, na tsayawa takarar gwamnan Jihar Yobe a zaɓen 2027. Shugaban ƙungiyar, Dakta Yerima Goni, ne ya bayyana hakan a wurin taron tara kuɗin da aka gudanar a ranar Litinin a Damaturu. Goni ya ce manufar wannan shiri ita ce ƙarfafa shigar matasa da sauran masu ruwa da tsaki cikin harkokin siyasa da shugabanci. A cewarsa, an samu kuɗin ne ta hanyar alƙawuran bayarwa, tura kuɗi ta banki da kuma…
Read More