ukarofi

12572 Posts
An naɗa Barista El-Marzuq a matsayin Amirul Hajji na jihar Katsina

An naɗa Barista El-Marzuq a matsayin Amirul Hajji na jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin aikin hajji na 2026 ƙarƙashin shugabancin tsohon kwamishinan Shari'a, Barista Ahmed Usman El-Marzuq. 'Yan kwamitin sun haɗa da Ali Isah,Amadu Ahmed Diddiri, Ali Sani Ahmed, Hajara Hajjo Lawal da Murna Ibrahim Duwan. Sauran sun haɗa da Mairo Ibrahim,Abduljalal Haruna Runka, Ahmed Tijjani Abdulkadir, Yusuf Ibrahim Safana Sai Abubakar Yusuf da zai zama sakataren kwamitin. A jawabinsa a wajen taron Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci 'yan kwamitin da su tabbatar da zirga zirga da kula da jin daɗin maniyata ba tare da an sami matsala ba. Ya kuma umurci…
Read More
Malamin addini ya shiga jam’iyyar ADC don magance matsalar tsaro

Malamin addini ya shiga jam’iyyar ADC don magance matsalar tsaro

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Dr. Abdulmudallib Muhammad Gusau, fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Zamfara, ya shiga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar ta ADC. Ya yi wannan sanarwar jim kaɗan bayan yin rijista a matsayin mamba a jam'iyyar ta ADC a sakatariyar jam'iyyar da ke Gusau yau Litinin. A cewarsa, rashin shugabanci mai kyau, rashin aikin yi da rashin jajircewar shugabanni a Jihar su ne manyan abubuwan da suka haifar da ƙaruwar rashin tsaro a jihar. Ya yi alƙawarin canza alƙiblar jihar Zamfara…
Read More
Idan mace na da hankali za ta tashi ta nemi na kanta – Khadija Abdulrasheed 

Idan mace na da hankali za ta tashi ta nemi na kanta – Khadija Abdulrasheed 

"Zamanin gulmace-gulmace ya ƙaura"  Daga AISHA ASAS Hajiya Khadija Abdulrasheed Mahuta mace ce wacce ya kamata mata su yi koyi da ita, saboda kasancewar ta jaruma kuma tsayayya, sannan wacce ta san ciwon kanta. Ta kasance cikin jerin mata da suke tauna taura biyu a lokaci guda. Ma'ana, mace ce wadda ba ta zauna ba don jiran sai wani ya samo ya kawo mata, a'a, ta tashi tsaye ne haiƙan wajen rufa wa kanta asiri. A tattaunawar ta da Manhaja, Mahuta ta bayyana wa masu karatu rayuwarta wadda za ta iya zama makaranta ga mata. Idan kun shirya, Wakiliyar Blueprint…
Read More
Rigimar fili: Wakilin jaridar Pilot a Nasarawa ya koka a kan kai wa iyalansa hari

Rigimar fili: Wakilin jaridar Pilot a Nasarawa ya koka a kan kai wa iyalansa hari

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Wasu miyagun mutane da ba a san ko su wanene ba ko daga ina suka fito ba su kimanin mutum 30 sun yi barazanar kai hari ga iyalan wakilin jaridar Pilot a jihar Nasarawa wato Mr. Augustine Kuza akan rigimar Fili a ƙauyen Kuduku dake ƙaramar hukumar Keana a Nasarawa. Da yake bayyana yadda lamarin ya auku ga 'yan jaridar 'yan uwansa Cif Augustine Kuza yace maharan suna jayayya ne akan wani filin noma dake yankin Iwagu da Kuduku duk a ƙaramar hukumar ta Keana a jihar. Wakilin jaridar Pilot ɗin ya ƙara da…
Read More
Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da cibiyar kula da yara masu tamowa a jihar

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da cibiyar kula da yara masu tamowa a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya Kaddamar da cibiyoyin kula da yara masu tamowa, ya yi gargaɗi Kan karkatar da abincin da ake bada wa. Sabbin cibiyoyin guda biyu a garin Ɓaure, da Daura, da kuma wuraren jinya (OTP) guda 60 a ƙananan hukumomin 12, wani muhimmin mataki na ƙara ƙarfafa yaƙi da matsalar tamowa a faɗin jihar. Shirin samar da cibiyoyin ya gudana ne ƙarƙashin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa wanda zai kula da magance lalurar yara masu fama da karancin abinci mai gina jiki (Tamowa). A jawabin maraba, ahugaban ƙaramar hukumar Baure,…
Read More
Gwamna Sule ya yi wa ɗaliban NSUK 82 da aka yaye ruwan Naira

Gwamna Sule ya yi wa ɗaliban NSUK 82 da aka yaye ruwan Naira

Daga JOHN D. WADA a Keffi Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya yi wa ɗaliban babban jami'ar jihar su 82 da suka kammala karatunsu suka kuma fito da satificate mai darajar farko ruwan naira inda kowannensu ya samu rabin miliyan sa'anan ɗalibai uku da su ka yi zara cikin ɗaliban sun samu miliyan daya kowanne. Gwamnan ya kuma bayyana cewa jami'ar ta tabbatar da bajintar ta na kasancewa ɗaya daga cikin manyan makarantun ƙasar nan da ake alfahari da su. Ya bayyana haka ne a wajen taron yaye tsofin ɗaliban jami'ar karo na 8 da kuma cikar jami'ar shekaru…
Read More
AIG Bello ya bada umarnin murƙushe ‘yan bindiga a Kaduna da Katsina

AIG Bello ya bada umarnin murƙushe ‘yan bindiga a Kaduna da Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, mai kula da shiyya ta huɗu dake kula da jihohin Kaduna da Katsina, wadda ke da helkwata a Katsina a karƙashin jagorancin AIG Bello Shehu ta umurci kwamishinonin 'yan sandan jihohin Kaduna da Katsina da su ƙara ɗaukar matakan sabbin dabarun da za su murƙushe hare-haren 'yan bindiga da kuma sauran laifuffuka. Bayanin hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwar manema labarai da jami'in hulɗa da jama'a na ofishin mataimakin sufeto janar mai kula da shiyya ta sha huɗu dake Katsina, ASP Umar Muhammad ya sanya wa hannu…
Read More
Yawan ba mace kuɗi na ƙara arziki, inji Dr. Farouk

Yawan ba mace kuɗi na ƙara arziki, inji Dr. Farouk

Wani likita kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, Dr. Farouk Adebiyi, ya jawo zazzafar muhawara a yanar gizo bayan furta wasu kalamai masu ɗaukar hankali dangane da kuɗi, rawar da mata ke takawa, da kuma samun arziki. A wasu saƙonni da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Dr. Farouk ya bayyana cewa maza da ke bai wa mata kuɗi suna da damar samun ƙarin arziki a rayuwa. A cewarsa, karamci ga mata na da alaƙa kai tsaye da samun albarka da wadata. Ya rubuta cewa, “Yayin da namiji ke ƙara bai wa mace kuɗi, haka arzikin sa ke…
Read More
Yadda rikicin uwa da ɗa kan zaman matarsa a gaban mota ya girgiza kafafen sada zumunta

Yadda rikicin uwa da ɗa kan zaman matarsa a gaban mota ya girgiza kafafen sada zumunta

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya tayar da ƙura, bayan wani matashi ya shiga zazzafar muhawara da mahaifiyarsa kan wanda ya dace ya zauna a kujerar gaba a mota tsakaninta da matar aurensa. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da iyalin suka shirya fita zuwa wani ibadar coci, inda aka hango mutumin tare da matarsa, mahaifiyarsa da kuma ’yar uwarsa suna ƙoƙarin shiga mota domin tafiya. Da aka zo batun shiga motar, mahaifiyar ta yi yunƙurin zama a kujerar gaba, amma ɗanta ya hana ta, yana mai cewa wannan wuri na matar aurensa…
Read More
’Yan Nijeriya na ci gaba da karɓar rancen manhajoji duk da tsananin kuɗin ruwa – Bincike

’Yan Nijeriya na ci gaba da karɓar rancen manhajoji duk da tsananin kuɗin ruwa – Bincike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Duk da yawaitar koke-koke kan tsananin ruwa da kuma matsin lamba daga masu bayar da lamuni ta yanar gizo, bincike ya nuna cewa har yanzu ’yan Nijeriya da dama na ci gaba da karɓar bashi daga waɗannan manhajoji domin magance matsalolin rayuwa, kasuwanci da kuma buƙatun yau da kullum. Rahoton bincike ya bayyana cewa harkar fasahar kuɗi, wato Fintech, na ci gaba da bunƙasa a Nijeriya, inda wasu kamfanonin lamuni ke amfani da halin ƙuncin jama’a wajen jefa su cikin mawuyacin hali ta hanyar bada bashi mai tsananin ruwa. Baya ga haka, ana zargin wasu daga…
Read More