ukarofi

12572 Posts
Gwamnatin Katsina ta amince da tallafa wa gidauniyar tsaro da Naira biliyan ɗaya

Gwamnatin Katsina ta amince da tallafa wa gidauniyar tsaro da Naira biliyan ɗaya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da buƙatar gwamnatin jihar na bayar da gudummawar naira biliyan ɗaya domin tallafawa gidauniyar tsaro ta jihohin Arewa, da nufin inganta tsaro a yankin. Wannan mataki ya biyo bayan wata buƙata da Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar wa majalisar, inda ya nemi amincewarta bisa tanadin doka. A zaman majalisar wanda Kakakin Majalisa Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya jagoranta, an tattauna batun tare da amincewa da shi baki ɗaya. Takardar wadda shugaban masu rinjaye, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ya gabatar, ta nuna cewa gwamnatin jihar za ta…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutane 188 bisa zargin aikata laifuka daban-daban a Katsina

‘Yan sanda sun kama mutane 188 bisa zargin aikata laifuka daban-daban a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda a Katsina ta sanar da kama mutane 188 bisa zargin aikata laifuka da suka shafi ta'addanci,fyaɗe da dallancin miyagun ƙwayoyi a jihar Katsina. Mai magana da yawun rundunar a katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a bayanin da yake wa manema labarai kan nasarorin da suka samu a cikin watan da ya wuce. Ya ce rundunar 'yan sandan sun kama mutanen da aikata laifuka daban daban har guda 120 a faɗin jihar. DSP Sadiq Aliyu ya bayyana cewa laifuka 98 na gaban kotu da suka haɗa da laifuffukan fashi da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirinsa na ƙarfafa tsaro a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirinsa na ƙarfafa tsaro a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bunƙasa yaƙi da rashin tsaro, musamman a yankunan da a baya suka fuskanci matsalar ‘yan bindiga. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake karɓar baƙuncin sabon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 14, Bello Shehu, wanda tsohon kwamishinan ‘yan sanda da kuma wanda ya maye gurbinsa, CP Umar Fagge a fadar gwamnatin jihar. CP Umar Fagge na da sama da shekaru 30 yana aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya, inda ya…
Read More
Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Daga FARFESA AHMAD MURTALA MANSUR Ci gaba daga makon jiya. iii- Bitcoin ba shi da zubi da tsari irin na katinan da ake ajiye kuɗaɗe a cikinsu kamar katina irin su ɓisa Card, Master Card da sauransu. Saboda su wadannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulda da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane! 8- Bisa irin bayanai da aka kawo a karkashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a karkashin lamba ta 7, duka wadannan suna nuna…
Read More
Dimukraɗiyyar Nijeriya tangal-tangal take yi?

Dimukraɗiyyar Nijeriya tangal-tangal take yi?

Daga SANI AHMAD GIWA A cikin tsarin mulkin dimukraɗiyya, ana ɗaukar adalci, bin doka da kuma bai wa kowane ɗan ƙasa damar bayyana ra’ayinsa a matsayin ginshiƙai na ci gaba da zaman lafiya. Dimukraɗiyya ba wai kawai tsarin zaɓe ba ne bisa doron siyasa, a'a, illa wata hanya ce ta tabbatar da cewa ikon mulki yana hannun jama’a, tare da damar sauya shugabanni cikin lumana da gaskiya. Sai dai a ’yan shekarun da suka yi ƙasa da uku, ana ci gaba da tayar da ƙura game da yadda wasu ke ganin gwamnatin jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki ke…
Read More
Karfafa gwiwar matasa kan ci gaban fasahar zamani 

Karfafa gwiwar matasa kan ci gaban fasahar zamani 

Masana ɗabi'ar ɗan adam sun bambanta tsakanin mai canjin tunani da wanda tunaninsa ba ya sauyawa. Duk wanda tunaninsa ba ya sauyawa shi ne mai dogara akan wani, domin samun tallafin gudanar rayuwa. Ko kuma wani abin tinƙaho da kowacce dama da yake da ita. Wannan halin ya ƙara tsawaita ne a shekarun da ake fama da lalacewar harkokin siyasa, da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da kuma gurɓacewar ɗabi'u da al'adu. Cigaba a canjin tunani na nufin burin mutum ya canza daga yanayin da yake ciki ko kuma ya bunƙasa yanayin aikinsa daga natsuwa zuwa ga wani sabon yanayin da mutum…
Read More
Mai ƙabilanci zai riga rana faɗuwa

Mai ƙabilanci zai riga rana faɗuwa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Masu iya magana na cewa gaskiya ba ta neman ado kuma duk daren daɗewa ko an kaucewa gaskiya sai an dawo kanta. Kazalika ita kuma ƙarya fure ta ke yi ba ta ’ya’ya. Wani salon, wai saƙo na isa inda a ke buƙata, a a waye waye sai ya mulki kansa ko za a kori wasu mutane daga ƙasar su koma inda su ka fito, duk na fitowa ne daga ‘yan bazata maƙiya Hausawa, Musulunci da Arewa. Na sha haska mu ku mutanen nan kuma akasarinsu ma ba su taba taka jihohin da a ke samun…
Read More
Yadda ya kamata ƙungoyin addini su tallafawa mabiyansu

Yadda ya kamata ƙungoyin addini su tallafawa mabiyansu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na karanta wani nazari da wani ya yi game sa ƙoƙarin da wata ƙungiyar Kirista take yi don inganta rayuwar mabiyanta da bunƙasa samar da hanyoyin shigar kuɗaɗenta. Wannan tsari nasu ya ja hankalina matuƙa, kuma na ga dacewar in kawo batun nan, domin ni da ku mu yi nazarinsa. Mu kuma duba yiwuwar kawo wani sauyi makamancinsa a cikin ƙungiyoyin mu na addini da cibiyoyin ilimi da nazari, ta yadda za mu samu hanyoyin inganta rayuwarmu. Al'ummar mu ta Arewa na cikin wani mawuyacin hali na talauci, jahilci da rashin tsaro, musamman a tsakanin musulmi.…
Read More
Muna gudanar da sauye-sauye a aikin gwamnati ne domin tsaftace tsarin – Dikko Raɗɗa

Muna gudanar da sauye-sauye a aikin gwamnati ne domin tsaftace tsarin – Dikko Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Muna aiwatar da sauye-sauye a fannin aikin gwamnati ne domin tsaftace tsarin gudanar da aiki, inganta ƙwarewa, da ƙara ingancin aiki a dukkan matakan gwamnati.” Gwamna Dikko Raɗɗa Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana haka a yayin da ya karɓi tawagar shugabannin gudanar da ƙananan Hukumomi, masu rajista, daraktoci, da shugabannin NULGE ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar kula da ayyukan ƙananan hukumomi, Alhaji Usman Aliyu Maska, a fadar gwamnatin jihar Katsina. Gwamna Raɗɗa ya sake tabbatar da aniyarsa ta samar da ingantaccen aikin gwamnati a matakin jiha da ƙananan hukumomi, inda ya bayyana…
Read More
Gwamnan Katsina ya bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga ƙungiyar ‘yan wasan guragu

Gwamnan Katsina ya bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga ƙungiyar ‘yan wasan guragu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bai wa ’yan wasa da jami’an da suka wakilci jihar a gasar National Para Games karo na uku da aka kammala a Abuja kyautar Naira miliyan 10. Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar ne lokacin da ya karɓi tawagar a gidan gwamnati da ke Katsina, bayan rawar da suka taka inda jihar ta zo a matsayi na 13 a faɗin ƙasa. Da yake gabatar da tawagar, kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ya bayyana cewa jihar Katsina ta fafata a fannoni daban-daban…
Read More