ukarofi

12458 Posts
An gudanar da taron wayar da kan ‘yan soshiyal midiya a ƙarkashin ADC a Argungu

An gudanar da taron wayar da kan ‘yan soshiyal midiya a ƙarkashin ADC a Argungu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi An yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani (Social Media) da ke ƙarƙashin jam'iyyar ADC da su tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗawa da kare mutuncin juna.An gudanar da wannan taron wayar da kai ne a ƙarƙashin jagoranci Argungu New Media Actors.Taron wanda ya haɗa masu amfani da kafafen sada zumunta na kafafen sada zumunta da ke aiki ƙarƙashin jam'iyyar ADC domin ƙara fahimtar juna da wayar da kai kan muhimmancin amfani da kafafen sadarwa.A wajen taron mai taken “Gaskiya da mutunta ra'ayin siyasa”, Shugaban yaƙin neman zaɓe na ƙaramar hukumar…
Read More
AGILE ta ƙara wa ’yan mata damar karatu a Gombe

AGILE ta ƙara wa ’yan mata damar karatu a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Shirin ƙarfafa ilimin ’yan mata da ƙarfafa su (AGILE) ya miƙa sabon aikin gine-gine ga makarantar sakandaren ƙaramar hukuma ta gwamnati (GJSS) da ke Akko Gari, a Jihar Gombe, domin inganta yanayin karatu da ƙara wa ’yan mata damar samun ilimi mai inganci. An miƙa aikin ne bayan hukumomin da abin ya shafa sun tabbatar da kammalawa da ingancin aikin, inda aka bayyana cewa an tsara shi ne domin samar da muhalli mai aminci da dacewa da koyarwa da koyo. Kodinetan AGILE na Jihar Gombe, Dr Amina Haruna Abdul, ce ta jagoranci tawagar da ta…
Read More
2027: City Boys ta yi taron gangamin goyon bayan Tinubu a Zamfara

2027: City Boys ta yi taron gangamin goyon bayan Tinubu a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗaruruwan magoya bayan APC sun gudanar da wani gagarumin gangamin goyon baya don Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Kashim Shettima a karo na biyu. Taron gangamin Grassroots Mobilizers ne suka shirya a yau Asabar domin nasarar Tinubu/Shettima a 2027. Haka zalika taron ya nuna goyon bayan Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen shugaba Tinubu. Taron gangamin, wanda Ahmad Abdulaziz Yari, memba na kwamitin gudanarwa na majalisar gudanarwa ta ƙungiyar yaran birni watau City Boy da kuma ƙungiyar Grassroots Mobilizers ta shirya don Tinubu da Shettima, ya jawo…
Read More
‘Yan kwamitin KT1T sun taya Usman Isyaku murnar samun lambar yabo

‘Yan kwamitin KT1T sun taya Usman Isyaku murnar samun lambar yabo

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mambobin kwamitin shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T) na Shiyyar Katsina ta tsakiya sun taya Alhaji Usman Isyaku, mai bai wa Gwamna Shawara kan Civil Servicre Reforms, murnar samun lambar yabo ta “Outstanding Special Adviser of the Year 2026.” An bai wa Alhaji Usman Isyaku lambar yabon ne a bikin cikar Jihar Katsina shekaru 39 da kafuwa, wanda aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Katsina Alhaji Farouk Lawal Joɓe. Mambobin kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mohammed Al-Amin, tare da Hon. Bishir Tanimu Gambo Dtm, Hon. Lawal Rufa’i Safana da sauran mambobin kwamitin, sun bayyana farin cikinsu,…
Read More
Sojoji sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Sojoji sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar Operation Fansan Yamma na rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Arewa maso yamma sun kama wasu mutane uku da ake zargi da tallafawa ’yan ta’adda da kuɗaɗe. Rundunar ta kuma ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina. Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Satumba 2026, dakarun Sector 2 sun tare wasu mutane uku da ke kan babur, inda aka gano suna ɗauke da Naira miliyan 2.7 da ake zargin kuɗin fansa ne, da wayoyin hannu guda uku, domin…
Read More
Ma’aikatar lafiya ta Nasarawa ta amince da tsarin daidaituwar lafiya domin magance sauyin yanayi kan lafiyar al’umma

Ma’aikatar lafiya ta Nasarawa ta amince da tsarin daidaituwar lafiya domin magance sauyin yanayi kan lafiyar al’umma

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ma'aikatar lafiya ta jihar Nasarawa ta amince da tsarin daidaitawa na lafiya na gwamnatin tarayya na 2025-2030 domin magance tasirin sauyin yanayi kan tsarin lafiyar al'ummar jihar. An bayyana amincewar ne a wajen taron bitar masu ruwa da tsaki na kwana ɗaya domin tantance tsarin daidaitawa na lafiya na jihar ta Nasarawa wadda aka gudanar a ranar Juma'a a Lafia babban birnin jihar. Tsarin daidaitawar lafiyar na ƙasa wani tsari ne na haɗa daidaitawa da sauyin yanayi a cikin manufofin lafiya da shirye-shirye da kuma gina ababen more rayuwa a faɗin ƙasar nan. Da…
Read More
Yaran jihar Neja suna barin makaranta don shiga haƙar ma’adinai – Bago

Yaran jihar Neja suna barin makaranta don shiga haƙar ma’adinai – Bago

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ce yara maza na barin makarantun sakandaren matakin JSS a faɗin jihar domin shiga aikin haƙar ma’adinai, saboda suna ganin aikin ya fi kawo kuɗi fiye da karatu. Bago ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana haƙar ma’adinai a matsayin babbar matsala a jihar. Jawabin gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka mutu a hannun Hukumar Tsaro da…
Read More
Dangote ya maida martani yayin da masu sayen hannun jari ke kiran kansu abokan hulɗarsa

Dangote ya maida martani yayin da masu sayen hannun jari ke kiran kansu abokan hulɗarsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya mayar da martani kan barkwancin da wasu ’yan Nijeriya ke yi a kafafen sada zumunta, inda suka fara kiran kansu abokan hulɗarsa bayan sayen hannun jari a Matatar Man Fetur ta Dangote. Dangote ya yi magana ne a wata hira da aka yi da shi a dandalin ƙatar Economic Forum ranar Lahadi, inda ya amince cewa ya ga barkwancin da ake yi a kafafen sada zumunta, ciki har da kiran da wasu sabbin masu hannun jarin ke yi na a ba su damar shiga ɗakin…
Read More
Dalilin da ya sa farashin fetur ke sauyawa a Nijeriya – NMDPRA

Dalilin da ya sa farashin fetur ke sauyawa a Nijeriya – NMDPRA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa daTace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce yanayin kasuwa ne ke ƙayyade farashin fetur a famfo, ba hukumar ce ke ƙayyade farashin kai tsaye ba, kamar yadda Dokar Masana’antun Man Fetur ta 2021 ta tanada. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, yayin da take mayar da martani kan damuwar da aka nuna game da ƙarin farashin man fetur a gidajen mai a faɗin ƙasar. NMDPRA ta amince cewa ƙarin farashin fetur na baya-bayan nan ya ƙara wa ’yan Nijeriya matsin tattalin arziki,…
Read More
Mutuwar masu haƙar ma’adanai 37: Ba Gwamnatin Neja ke da alhakin biyan diyya ba – Bago

Mutuwar masu haƙar ma’adanai 37: Ba Gwamnatin Neja ke da alhakin biyan diyya ba – Bago

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ce gwamnatin jihar ba za ta biya diyya ga iyalan mutane 37 da suka mutu a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) ba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na intanet mai suna Zarar Bunu da ke Minna, wadda aka watsa ranar Lahadi. Ya ce, alhakin biyan diyya bai rataya a wuyan gwamnatin jihar ba, domin mutanen sun mutu ne a hannun wata hukuma ta tsaro da ke ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya. Sai dai Bago ya ce gwamnatin jihar za ta tallafa…
Read More