ukarofi

12458 Posts
’Yan haƙar ma’adanai 37: An karɓi N45,000 a hannuna, inji mahaifiyar ɗaya daga cikinsu

’Yan haƙar ma’adanai 37: An karɓi N45,000 a hannuna, inji mahaifiyar ɗaya daga cikinsu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Malama Hafsat Saidu, mahaifiyar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi masu haƙar ma’adinai, waɗanda suka mutu a Jihar Neja, ta ce a baya ta taɓa shafe kwanaki biyar a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) bayan jami’an hukumar sun kama ta a wani wurin haƙar ma’adinai. NSCDC ta ce, a ranar Alhamis cewa an kama waɗanda ake zargin ne yayin wasu samame da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankin Lt. Gen. Mohammed Inuwa Wushishi Estate, da ke Minna, babban birnin Jihar Neja. Kwamandan NSCDC na Jihar…
Read More
2027: Dan majalisar Oyo na APC ya buƙaci Musulmi su zaɓi Musulmi

2027: Dan majalisar Oyo na APC ya buƙaci Musulmi su zaɓi Musulmi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo na jam’iyyar APC, Ibrahim Shittu, ya yi kira ga masu zaɓe Musulmi da su ƙi zaɓar ’yan takarar gwamna Kiristoci a zaɓen shekara mai zuwa. Shittu, wanda ke wakiltar mazaɓar Saki ta Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Oyo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa masu zaɓe jawabi a wani taro da aka gudanar a jihar. ɗan majalisar ya buƙaci Musulmi su mara wa ’yan takarar Musulmi baya, yana mai iƙirarin cewa zaɓen Kiristoci zuwa muƙaman gwamnati zai sa a hukunta Musulmi. “Muna roƙonku, ya ku iyayenmu,…
Read More
Dangote ya shirya zuba Dala biliyan 10 a fannin lantarkin Afirka

Dangote ya shirya zuba Dala biliyan 10 a fannin lantarkin Afirka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya sanar da shirin zuba sama da dala biliyan 10 a fannin wutar lantarki na nahiyar Afirka cikin shekaru masu zuwa. Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Al Jazeera, inda ya ce samar da ingantacciyar wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin Afirka da ci gaban masana’antu. Ya ce, wannan zuba jari na daga cikin manyan sauye-sauyen da yake sa ran za su gudana a faɗin nahiyar cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa. “Mun shirya zuba…
Read More
Biyan haya ke sa ni ƙara aiki tuƙuru — Ola na Legas

Biyan haya ke sa ni ƙara aiki tuƙuru — Ola na Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shahararren ɗan Nijeriya mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai tallan motocin alfarma, Waris Olayinka Akinwande, wanda aka fi sani da Ola na Legas, ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi zama a gidan haya duk da cewa yana da gidaje na kansa. Ola ya ce biyan kuɗin haya wani ɓangare ne na dabarar da ya ke amfani da ita wajen ci gaba da ƙoƙari da kuma hana kansa samun gamsuwa da abin da ya riga ya cimma. Ola na Legas ya bayyana hakan ne yayin da yake baƙo a shirin KK Show, wanda…
Read More
An saka Zainab Okino ta Blueprint a kwamitin binciken mutuwar masu haƙar ma’adanai 37 a Neja

An saka Zainab Okino ta Blueprint a kwamitin binciken mutuwar masu haƙar ma’adanai 37 a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta naɗa Shugabar Kwamitin Editoci ta kamfanin jaridun Blueprint, Mrs. Zainab Suleiman Okino, a matsayin ɗaya daga cikin mambobin kwamitin mutum 10 mai zaman kansa da aka kafa, domin binciken mutuwar masu hawar ma’adanai 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaron Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) a Jihar Neja. Okino za ta kasance cikin kwamitin da ya ƙunshi ƙwararru daga ɓangarorin tsaro, shari’a, lafiya, haƙar ma’adinai, kare haƙƙin ɗan Adam da harkokin jama’a, yayin da Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin gano abin da ya haddasa mutuwar waɗanda ake tsare da…
Read More
An taɓa yanke wa wakilin Atiku a Amurka hukuncin ɗauri kan laifin cin zarafi

An taɓa yanke wa wakilin Atiku a Amurka hukuncin ɗauri kan laifin cin zarafi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani wakilin Atiku ɗan ƙasar Amurka mai suna Karl Von Batten, wanda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ɗauka aiki, an taɓa samun sa da laifin cin zarafin budurwarsa tare da yanke masa hukuncin ɗaurin watanni shida a watan Disamba na shekarar 2003, kamar yadda takardun kotu da News Point Nigeria ta gani suka bayyana. Hukuncin ya samo asali ne daga wani lamari da ya faru a watan Yulin 2003, wanda daga baya aka ambata a cikin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara ta District of Columbia da ke Amurka. Cikakken bayani kan hukuncin…
Read More
Gwamnatin Kano, NASSI da Stanbic IBTC sun shirya taron bunƙasa ƙananan masana’antu

Gwamnatin Kano, NASSI da Stanbic IBTC sun shirya taron bunƙasa ƙananan masana’antu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Zuba Jari, Ciniki, Kasuwanci da Masana’antu ta Jihar Kano ta bayyana cewa taron yini guda da aka shirya domin bunƙasa ƙananan da matsakaitan masana’antu a jihar ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Kano. Ta bayyana hakan ne yayin wani taro da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Masu ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta ƙasa (NASSI), wanda Bankin Stanbic IBTC ya ɗauki nauyin gudanarwa a Kano. Ta ce babban jigon taron shi ne samar da hanyoyin magance matsalolin da ke fuskantar ƙananan da matsakaitan masana’antu, tare da gina yanayi…
Read More
Kaduna: Uba Sani ya amince da biyan biliyan N3.659 ga ’yan fansho

Kaduna: Uba Sani ya amince da biyan biliyan N3.659 ga ’yan fansho

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da biyan Naira biliyan 3.659 ga ’yan fansho, ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu, inda mutane 1,339 da ke ƙarƙashin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS) da Defined Benefit Scheme (DBS) za su amfana. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sabon biyan ya kawo jimillar kuɗaɗen fanshon da gwamnatin Uba Sani ta biya tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023 zuwa Naira biliyan 21.455, waɗanda…
Read More
Dalilin Shettima na wakilcin Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya – Idris

Dalilin Shettima na wakilcin Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya umarci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya wakilce shi a taron babban zauren Majalisar ɗinkin Duniya karo na 81, UNGA, saboda a halin yanzu Shugaban ƙasar yana hutun shekara. Ministan ya ce Shettima na tafiya ne da cikakken ikon Shugaban ƙasa da kuma wakilcin Tarayyar Nijeriya, yana mai watsi da ra’ayoyin da ke cewa rashin halartar Tinubu da kansa a babban taron na iya rage matsayin Nijeriya a fagen diflomasiyya. A cikin wata…
Read More
Bassam Diagnostic Centre ta samu yabon likitoci kan ingancin gwajin jini

Bassam Diagnostic Centre ta samu yabon likitoci kan ingancin gwajin jini

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Cibiyar gwaje-gwajen kimiyya da na jini, Bassam Diagnostic Centre da ke birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Manaja Shamsudden Usaini, ta samu yabo daga wasu manyan likitoci da asibitoci a Kano da kewaye, bisa irin taimakon da take bayarwa ga al’umma da kuma ingancin ayyukan gwajin jini da sauran binciken lafiya da take gudanarwa. Manajan cibiyar, Shamsudden Usaini, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai da ya yi a tsakiyar makon da ya gabata. Ya ce nasarar da Bassam Diagnostic Centre ta samu ta samo asali ne daga samun ƙwararrun ma’aikata da kuma kayan…
Read More