26
Sep
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo na jam’iyyar APC, Ibrahim Shittu, ya yi kira ga masu zaɓe Musulmi da su ƙi zaɓar ’yan takarar gwamna Kiristoci a zaɓen shekara mai zuwa. Shittu, wanda ke wakiltar mazaɓar Saki ta Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Oyo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa masu zaɓe jawabi a wani taro da aka gudanar a jihar. ɗan majalisar ya buƙaci Musulmi su mara wa ’yan takarar Musulmi baya, yana mai iƙirarin cewa zaɓen Kiristoci zuwa muƙaman gwamnati zai sa a hukunta Musulmi. “Muna roƙonku, ya ku iyayenmu,…
