26
Sep
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ’yan Nijeriya sun fara ganin saukar farashin sufuri sakamakon matakan da gwamnati ke ɗauka na amfani da makamashi mai rahusa wajen rage kuɗin zirga-zirga. Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da rahoto kan alƙawarin da ya yi na ganin an rage farashin sufuri daga ranar 1 ga Oktoban 2026. A ranar 27 ga Agusta, Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi 36, inda suka tattauna matakan da za su taimaka wajen rage farashin sufuri a faɗin ƙasar domin rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin matsin tattalin arziki. A…
