25
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayyana cewa tsawaita zaman Ibrahim Magu a matsayin Muƙaddashin Shugaban Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arziƙi Zagon ƙasa (EFCC) ya saɓa wa doka, inda ta soke wani hukuncin Babbar Kotun Tarayya da a baya ya amince da ci gaba da riƙe shi a matsayin mukaddashin shugaban hukumar. Kwamitin alkalai uku na Kotun ɗaukaka ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, bayan sauraron ƙarar da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar kan ci gaba da zaman Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC, bayan da Majalisar Dattawa ta…
