ukarofi

12467 Posts
’Yan mata huɗu sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Jigawa

’Yan mata huɗu sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan mata huɗu masu shekaru tsakanin 12 zuwa 13 sun mutu bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji takwas ya kife a tafkin Dudduru, da ke ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Laraba, 23 ga Satumba, 2026, yayin da fasinjojin ke tafiya daga ƙauyen Kwadige zuwa Kasuwar Chai Chai Sabuwa. Tafkin Dudduru yana da nisan kusan kilomita uku daga ƙauyen Kwadige. Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) a Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar…
Read More
Farashin fetur a Nijeriya ya fi rahusa akan na Amurka, Ghana da Afirka ta Kudu – Minista

Farashin fetur a Nijeriya ya fi rahusa akan na Amurka, Ghana da Afirka ta Kudu – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya, Heineken Lokpobiri, ya ce matsakaicin farashin man fetur a Nijeriya har yanzu ya fi na Amurka da wasu ƙasashen Afirka rahusa, duk da cire tallafin man fetur. Lokpobiri ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today ranar Talata, inda yake kare tsarin cire kayyade farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsadar man fetur a sassan ƙasar. Jawabin ministan ya zo ne bayan da matatun man fetur, ciki…
Read More
APC ta lashe zaɓen cike gurbin majalisar Kano a Dawakin Kudu

APC ta lashe zaɓen cike gurbin majalisar Kano a Dawakin Kudu

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Dan takarar jam’iyyar APC, Hussaini Yusuf-Datti, ya lashe zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Kudu/Warawa, wanda aka gudanar a ranar Asabar. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Yusuf-Datti a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan kammala tattara sakamakon ƙuri’un da aka kada a mazabun da ke ƙarƙashin mazaɓar. Yusuf-Datti ya samu ƙuri’a 22,890, inda ya doke ɗan takarar PRP, Habib Hamisu, wanda ya samu ƙuri’a 270. ɗan takarar PDP, Abdullahi Adamu, ya samu ƙuri’a 108, yayin da ɗan takarar APP, Bala Mohammed-Sani, ya samu 53,…
Read More
Sarkin Musulmi ya gargaɗi ‘yan siyasa kan kai masu ibada Makka da Kudus da kuɗaɗen sata

Sarkin Musulmi ya gargaɗi ‘yan siyasa kan kai masu ibada Makka da Kudus da kuɗaɗen sata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu riƙe da mukaman gwamnati da su guji amfani da kuɗaɗen jama’a da aka samu ta hanyar rashawa wajen ɗaukar nauyin zuwa wuraren ibada na Makka da Kudus, yana mai cewa Allah ba Ya karɓar ibadar da aka gudanar da kuɗin da aka samu ta hanyar haram. Sultan ya yi wannan gargaɗin ne ranar Laraba a Abuja, yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki da Majalisar ƙasa ta Addinai (NIREC) ta shirya, inda ya buƙaci shugabannin addinai su ƙara haɗa kai…
Read More
Ba mu da shirin ƙara kuɗin wuta yanzu — Ministan Lantarki

Ba mu da shirin ƙara kuɗin wuta yanzu — Ministan Lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a ƙasar. Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a daidai lokacin da yake cika kwanaki 100 da karɓar ragamar muƙamin. Tegbe ya ce ya samu kiraye-kirayen waya da dama a ƙarshen mako bayan yaɗuwar rahotannin cewa Gwamnatin Tarayya na shirin ƙara kuɗin wutar lantarki. Ya ce rahotannin ba su da tushe, inda ya bayyana cewa abin da gwamnatin ta mayar da hankali a kai…
Read More
Satar jarrabawa: Jami’ar Kalaba ta dakatar da ɗalibai tara

Satar jarrabawa: Jami’ar Kalaba ta dakatar da ɗalibai tara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’ar Calabar (UNICAL) ta dakatar da wasu ɗalibai tara bisa zargin aikata satar jarrabawa da kuma wasu munanan ɗabi’u da ake zargin sun aikata tare da yaɗa su ga sauran ɗaliban jami’ar. Hukumar gudanarwar jami’ar ce ta yanke hukuncin dakatar da ɗaliban bayan wani zama da ta gudanar, sakamakon rahoton da Sashen Kula da Munanan ɗabi’u da Satar Jarrabawa na jami’ar (SEMC) ya gabatar. A cewar bayanan da aka samu, an ɗauki matakin ne bayan wani kwamiti da ke binciken lamarin ya gana da hukumar gudanarwar jami’ar. Daga bisani, Magatakardar Jami’ar, Dokta Chikwuka Icha,…
Read More
Makinde ya ƙalubalanci Tinubu kan alƙawarin samar da wutar lantarki

Makinde ya ƙalubalanci Tinubu kan alƙawarin samar da wutar lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan alkawarin da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 na inganta samar da wutar lantarki a Nijeriya. Makinde ya ce bai kamata Tinubu ya nemi wa’adi na biyu ba idan har ba a magance matsalar wutar lantarki ba. Makinde ya ce Tinubu ya taɓa bayyana cewa idan ba a gyara matsalar wutar lantarki ba, bai kamata ’yan Nijeriya su sake zaɓensa a wa’adi na biyu ba, inji shi. Gwamnan ya bayyana hakan ne…
Read More
A wata mai zuwa jirgin sama zai fara jigilar fasinjoji tsakanin Gusau da Abuja

A wata mai zuwa jirgin sama zai fara jigilar fasinjoji tsakanin Gusau da Abuja

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara jigilar fasinjoji kai tsaye tsakanin Gusau da Abuja, inda ake sa ran fara zirga-zirgar jiragen sau biyu a mako daga wata mai zuwa. An sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin a ranar Litinin, a wani mataki da gwamnatin ta ce zai inganta sufuri tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zuba jari da yawon buɗe ido a Zamfara. Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce Mataimakin Gwamnan…
Read More
Tauraruwar Sarkin Baka ta shirya mauludi a karo na farko

Tauraruwar Sarkin Baka ta shirya mauludi a karo na farko

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Sayyada Safiyya Sa’id, wadda aka fi sani da Tauraruwar Sarkin Baka ta Hausawan Afrika, ta shirya babban taron Maulidi a karon farko a farfajiyar ƙofar gidanta da ke birnin Kano a ranar Asabar da ta gabata. An shirya taron ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), tare da tunawa da koyarwarsa da kuma ƙarfafa soyayya da bin ɗabi’un Manzon Allah (SAW). Maulidin da Tauraruwar Sarkin Baka ta shirya ya samu halartar ɗimbin malamai manya da matasa, mawaƙa masu yabon Manzon Allah (SAW), da sauran bayin Allah salihai da masu kishin ganin…
Read More
Bai kamata haƙar ma’adinai ta zama hukuncin kisa ba a Nijeriya

Bai kamata haƙar ma’adinai ta zama hukuncin kisa ba a Nijeriya

Mutuwar waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun jami'an tsaro a Minna, Jihar Neja, da kuma sabon ruftawar ramin haƙar ma’adinai a Jihar Taraba, sun sake tunatar da Nijeriya irin munin matsalar haƙar ma’adinai da har yanzu ba a samu mafita gare ta ba. A Minna, mutane 33 sun mutu yayin da suke hannun jami'an tsaro, yayin da a Taraba ƙasa ta rufta a kan wasu masu haƙar ma’adinai 20 a ƙarƙashin wani rami mai hatsari. Waɗannan masifu guda biyu na buƙatar a gano gaskiyar abin da ya faru tare da ɗaukar alhakin laifin da…
Read More