ukarofi

12467 Posts
Shugaban hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa na Jihar Katsina ya ajiye aikinsa

Shugaban hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa na Jihar Katsina ya ajiye aikinsa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa na jihar Katsina, Barrister Sulaiman Muhammad Namadi, ya ajiye muƙamin sa. Wannan kuwa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ya fitar, domin bayyana wannan mataki da ya ɗauka. Barrister Sulaiman Namadi ya gode wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa damar da ya ba shi ta yin aiki domin cigaban jihar Katsina. Haka zalika ya yi wa Gwamnan da Jam'iyyar APC fatan samun nasara. Wannan dai na zuwa ne kwana guda kacal, bayan da mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara a kan cigaban al'umma, Alhaji Abubakar Tsanni…
Read More
Dalilin kotu na soke tikitin takarar Pantami

Dalilin kotu na soke tikitin takarar Pantami

*Ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Gombe, Babban Birnin Jihar Gombe, ta umarci babbar jam’iyyar adawa a jihar, wato PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, domin tabbatar da tantance ɗan takararta na gwamnan jihar ta Gombe. Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin a jiya Alhamis bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana mai ƙalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na gwamna. Usman…
Read More
Tsanni ya ajiye muƙaminsa a Katsina

Tsanni ya ajiye muƙaminsa a Katsina

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin cigaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye muƙamin sa. Kamar yadda jaridar Katsina Times ta ruwaito ofishin sakataren gwamnatin Jihar Katsina ta sami tabbacin haka. A cewar kafar yaɗa labaran, Alhaji Abubakar Tsanni ya rubuta takardar ajiye mukaminsa ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2026, inda ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a cikin gwamnatinsa. A cikin takardar, Tsanni ya bayyana cewa zai ci gaba da nuna godiya da girmamawa ga gwamnatin Gwamnan Katsina bisa damar da…
Read More
Shekara 30 da kafuwa, dole Nasarawa ta fifita haɗin kai – Akabe

Shekara 30 da kafuwa, dole Nasarawa ta fifita haɗin kai – Akabe

Daga JOHN WADA a Lafia Yayin da Jihar Nasarawa ke cigaba da shirin cika shekaru 30 da kafuwa, mataimakin gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe ya yi kira ga mazauna jihar da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai da kuma ɗaukar nauyin makomar jihar tare. Akabe wanda shi ne shugaban kwamitin shirye-shiryen bikin cika shekaru 30 ɗin yayi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Lafia. Ya bayyana cewa an ƙirƙiro jihar Nasarawa a shekarar 1996 a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha kuma bikin cika shekaru 30 ɗin ya ba da damar…
Read More
Babba Kaita ya taya al’ummar Katsina murnar cika shekaru 39 da ƙirƙira

Babba Kaita ya taya al’ummar Katsina murnar cika shekaru 39 da ƙirƙira

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya taya al’ummar jihar murnar cika shekaru 39 da kafuwarta, tare da yin kira da a yi addu’ar Allah ya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro, talauci da sauran ƙalubalen da jihar ke fuskanta. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ɗan takarar Abubakar Ahmed ya fitar yayin da Jihar Katsina ke bikin cika shekaru 39 da kafuwarta, yana mai cewa duk da cewa ranar cikar jihar shekaru 39 abin farin ciki ce, akwai buƙatar yin tunani kan…
Read More
‘Yan sanda a sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Nasarawa

‘Yan sanda a sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa sun daƙile wani shiri na garkuwa da mutane tare da kama wasu mutum huɗu da ake zargi da shirya kashe wanda za su sace bayan sun karɓi kuɗin fansa. Rundunar ta kuma sanar da kama wasu mutum biyu dake da alaƙa da kisan da ya shafi ƙungiyar asiri da aka samu a Lafia da safiyar Laraba. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya aikawa Nigerian Tribune a ranar Laraba a Lafia.…
Read More
UNGA 81: Raɗɗa ya buƙaci masu zuba jari su shiga ayyukan zuba jari a Katsina

UNGA 81: Raɗɗa ya buƙaci masu zuba jari su shiga ayyukan zuba jari a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya buƙaci masu zuba jari masu zaman kansu su ƙara shiga ayyukan da za su taimaka wajen raya jihar, musamman a fannonin noma, sarrafa amfanin gona, sufuri, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi. Gwamnan ya bayyana haka ne a taron ASIS Global Action Forum da aka gudanar a New York, a wani ɓangare na taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA 81). Ya ce Katsina ta samu tallafin ayyukan raya ƙasa da dama, ciki har da sama da dala miliyan 430 daga Bankin Duniya, da kuma…
Read More
NIMC ta ƙaryata zargin kutse cikin rumbun bayanai na NIN

NIMC ta ƙaryata zargin kutse cikin rumbun bayanai na NIN

Daga USMAN KAROFI Hukumar kula da shaidar ƙasa ta Najeriya (NIMC) ta musanta wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa an yi kutse cikin rumbun bayanan lambobin shaidar ƙasa (NIN) na Najeriya. Hukumar ta bayyana ikirarin a matsayin ƙarya, tana mai cewa bidiyon wani tsohon rahoto ne da aka fitar a shekarar 2024, wanda tuni aka ƙaryata shi. NIMC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Kayode Adegoke, ya fitar tare da wallafa ta a shafin hukumar na X ranar Alhamis. Hukumar ta ce babu wata…
Read More
Mai ba gwamna shawara ya fice daga APC a Kebbi

Mai ba gwamna shawara ya fice daga APC a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Alhaji Abdulrazak Muhammed daga ƙaramar hukumar Argungu ɗaya daga cikin manyan mashawartan gwamna Malam Nasir Idris ya sanar da ajiye muƙamin sa tare da barin jam'iyyar APC.Ya bayyana haka ne a gidan sa da ke Argungu a wani taron manema labarai da ya shirya ranar Laraba ɗin nan.Alhaji Abdulrazak Muhammed wanda tsohon kwamishinan dindindin kan harkokin majalisar dokokin jihar ne ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar APC ne saboda rashin yin abinda ya kamata tun kama daga yi wa talakawa ayyukan cigaba musamman abinda ya shafi tsaro ya zuwa yin ko-oho da yan…
Read More
Me yasa rubutu ke neman sabuwar rayuwa: Abin da masana suka tattauna a taron Comic Con 2026

Me yasa rubutu ke neman sabuwar rayuwa: Abin da masana suka tattauna a taron Comic Con 2026

Daga AISHA ASAS A ranar 12 ga Satumba, 2026, ne aka gudanar da taron Lagos Comic Con a birnin Legas, wani babban taro da ya tattaro masu rubutu, masu zane, masu shirya fina-finai, masu fasahar kirkira da sauran masu ruwa da tsaki a duniyar nishaɗi da adabi. Daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a taron akwai wata tattaunawa da aka yi kan yadda labari da rubutu ke neman sabuwar rayuwa a wannan zamani, daga shafin littafi zuwa zane-zanen labari (comic), zuwa zane-zanen motsi (animation) da kuma fim. Amma me ya sa labari yake neman irin wannan sabuwar rayuwa?…
Read More