ukarofi

12467 Posts
Caine Prize: Labaran Afirka biyar da suka tsaya cak a gaban duniyar adabi

Caine Prize: Labaran Afirka biyar da suka tsaya cak a gaban duniyar adabi

Daga AISHA ASAS A duniyar rubutu, ba kowane labari ne yake iya sa mutum ya tsaya daga abin da yake yi ya karanta shi ba. Wasu labarai sukan zo su wuce kamar yadda aka saba, wasu kuma sukan kama wani abu na rayuwa da mutane suke gani kullum amma ba sa samun kalmomin da za su bayyana shi. Sai marubuci ya zo da alkalami, ya duba abu daga wata kusurwa, sannan ya sa abin da aka saba gani ya zama abin da ba za a iya mantawa da shi ba. Wataƙila wannan ne ya sa ake ci gaba da kallon…
Read More
Gombe 2027: A kawo muƙabala, Gwamna na nan a shirye – Shawai

Gombe 2027: A kawo muƙabala, Gwamna na nan a shirye – Shawai

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya ce ɗan takaransa a shirye yake ya fuskanci sauran ’yan takarar gwamna a muƙabalar bainar jama’a gabanin zaɓen 2027. Shawai ya ce duk wanda ke kiran a gudanar da muƙabalar ya sanya rana da wurin da za a yi ta, domin a cewarsa, Gwamna “a shirye yake kowace rana, a kowane lokaci.” Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce muƙabalar za ta ba ’yan takarar damar gabatar…
Read More
NCDC ta ƙara jan kunne kan annobar Ebola a ƙasar Kongo

NCDC ta ƙara jan kunne kan annobar Ebola a ƙasar Kongo

Daga USMAN KAROFI Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar da sabon shawarwarin lafiya dangane da annobar cutar Ebola da ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC). Hukumar ta ce Najeriya na ƙara matakan shiri domin kare ƙasar daga duk wata barazanar da ka iya tasowa daga annobar. NCDC ta shawarci matafiya da ke shigowa Najeriya daga ƙasashen da ake samun yaɗuwar Ebola da su cike takardar bayanan lafiya (Health Declaration Form), a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa sa ido da gano masu yiwuwar kamuwa da cutar. Sai dai hukumar ta ce a…
Read More
Jihar Katsina ta cika shekara 39 da kafuwa

Jihar Katsina ta cika shekara 39 da kafuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jihar Katsina wanda tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙirƙira da Jihar Bayelsa a rana guda yau ta cika shekara 39 da ƙirƙira A saƙon sa ga al'ummar Jihar Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al’ummar jihar murnar cika shekaru 39 da kafuwar jihar, yana mai cewa Katsina na ci gaba da tafiya bisa manufofin ci gaba, tare da gina tubalin samun ingantaccen tsaro, wadata da ƙaruwar tattalin arziki A cikin saƙon da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar 23 ga Satumba 2026, Gwamna Raɗɗa ya…
Read More
Ban ta taɓa ganin shugaban da ya fi Tinubu kyawawan tsare-tsare ba – Masari

Ban ta taɓa ganin shugaban da ya fi Tinubu kyawawan tsare-tsare ba – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce a kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa, bai taɓa ganin shugaban Najeriya mai kyawawan tsare-tsaren farfaɗo da ƙasar fiye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Masari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wasu mata a wani taro da aka gudanar a Kaduna. Masari ya kuma soki masu cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi komai ba, yana mai cewa irin wannan suka ya taɓa faruwa a gwamnatocin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan. Tsohon gwamnan, ya buƙaci masu wa’azi mata da su yi amfani…
Read More
An buƙaci ma’aikatu na gwamnatin Katsina su yi aiki da sabon kwamitin abinci mai gina jiki

An buƙaci ma’aikatu na gwamnatin Katsina su yi aiki da sabon kwamitin abinci mai gina jiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar dokokin jihar Katsina ta buƙaci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kasafin kuɗin su ya ƙunshi shirye-shiryen inganta samar da abinci mai gina jiki, da su riƙa aiki tare da sabon kwamitin majalisar da aka kafa domin kula da harkokin abinci mai gina jiki. Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Lawal Yaro, ya bayyana hakan ne yayin da ma’aikatar lafiya da hukumomin da ke ƙarƙashinta suka bayyana gaban kwamitin domin kare ƙiyasin kasafin kuɗin shekarar 2027. Hon. Lawal ya bayyana damuwa kan yadda a wasu lokuta ake samun sauye-sauye a tsare-tsare da manufofin gwamnati,…
Read More
Tarihin takardar kuɗi ta farko da aka yi amfani da ita a Nijeriya (I)

Tarihin takardar kuɗi ta farko da aka yi amfani da ita a Nijeriya (I)

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kafin a fara amfani da takardun kuɗi irin waɗanda ake gani a yau, al’ummomin da ke zaune a yankin da daga baya ya zama Nijeriya sun yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen gudanar da kasuwanci da musayar kayayyaki. Daga ƙananan wuri na teku zuwa manila, gishiri da musayar kaya da kaya, tsarin kuɗi ya sha sauye-sauye kafin takardar kuɗi ta fara samun matsayi a ƙasar. To, yaushe aka fara amfani da takardar kuɗi a Nijeriya? Wace hukuma ce ta fara fitar da ita? Kuma ta yaya ta zama hanyar biyan kuɗi a ƙasar? Labarin ya fara…
Read More
Kar Arewa ta ce za ta karɓi mulki a 2027 – Nigeria Forward

Kar Arewa ta ce za ta karɓi mulki a 2027 – Nigeria Forward

Dag ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata ƙungiyar siyasa mai suna Nigeria Forward, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar Arewacin Najeriya da kada su yi watsi da tsarin karɓa-karɓa na shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudu. Ƙungiyar ta ce ya kamata Arewa ta mutunta fahimtar da aka cimma tun bayan komawar dimokuradiyya a 1999, ta hanyar bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas kafin a nemi dawo da shugabancin ƙasa Arewa. Mataimakin jagoran ƙungiyar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda shi ne kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, ya…
Read More
Yaƙin neman zaɓe: Gwamnatin Zamfara ta hana bangar siyasa

Yaƙin neman zaɓe: Gwamnatin Zamfara ta hana bangar siyasa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana duk wani nau'in bangar siyasa a lokacin yaƙin neman zaɓen da ke tafe a Jihar. Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa Hon. Nura Sani Abdullahi ya yi wannan kalamai a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishin sa a Gusau yau Talata. A cewar sa, tuni ofishin sa ya yi wani zama na musamman da shugabannin jam'iyyun siyasa 22 da ke jihar don faɗakar da juna yadda za a gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen cikin kwanciyar hankali. Hon. Nura Sani Abdullahi ya bayyana cewar ofishin…
Read More
Gwamnatin Kano za ta tabbatar da yi wa Malam Abduljabbar adalci – Garo

Gwamnatin Kano za ta tabbatar da yi wa Malam Abduljabbar adalci – Garo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da bibiyar shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, tare da ƙoƙarin tabbatar da an yi adalci a lamarin. Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau yayin taron Maulidin Annabi Muhammad (SAW) da Jami’atu Sankwari ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Bazullahi Kabara, inda ya yi tsokaci kan shari’ar Sheikh Abduljabbar. “Insha Allah, Gwamnatin Jihar Kano tana bibiyar shari’ar, kuma Insha Allah Gwamnatin Jihar Kano za ta tsaya ta tabbatar an yi adalci, wanda duk ‘yan’uwa da al’ummar Musulmi za…
Read More