22
Sep
Daga RABI'U SANUSI a Kano Kamfanin Nestlé Milo tare da haɗin gwiwar tsohon kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Ahmed Musa, sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta yara ’yan ƙasa da shekaru 13 a Kano.Kamfanin ya ce ya shirya gasar ce da nufin zaƙulo zaƙaƙuran yara masu baiwar ƙwallon ƙafa a faɗin Arewacin Najeriya.Ya ce maƙasudin shirya gasar ta kusan tsawon mako uku shi ne domin a horar da yaran sannan a koya musu muhimmancin jajircewa, sadaukarwa da kuma fito da baiwar da suke da ita.Da yake jawabi a lokacin buɗe gasar, wakilin kamfanin na Milo, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya…
