ukarofi

12467 Posts
Ya kamata a riƙa hukunta masu tuƙin ganganci kamar yadda ake yi a kasashen ƙetare

Ya kamata a riƙa hukunta masu tuƙin ganganci kamar yadda ake yi a kasashen ƙetare

Daga UNCLE LARABI Yadda mutane ke tuƙin ganganci a Kano kai ka ɗauka a gidajen mahaukata suke zuwa a koya musu motar ko abin tuƙin, duk da kaso mai yawa na masu tuƙa motoci a Kano ‘sa giya, taka burki ne’. Ma'ana; koyo ne wajen abokansu ko kula da ƙafar direba, ba su zuwa ‘driving school’ a koya musu yadda ya kamata.  Masu adaidaita sahu idan suka ga tirela har wani shige mata suke. Idan ka yi magana sauran fasinjan cikin adaidaita sahu ɗinsu za su ɗaure wa mai tuƙin gindi kan cewar ka fiye tsoro ran nan dai guda…
Read More
Jiga jigan APC biyu makusantan ɗan takarar gwamna sun koma PDP a Gombe

Jiga jigan APC biyu makusantan ɗan takarar gwamna sun koma PDP a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe An samu sabon sauyi a fagen siyasar Gombe, yayin da wasu fitattun makusantan ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, biyu suka fice daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar PDP. Mutanen biyu, Hon. Ibrahim Adamu Muhammad, wanda aka fi sani da Uban Dawakin Gombe, da Alhaji Auwalu Alhassan, wanda aka fi sani da Chiburosi, sun kuma bayyana goyon bayansu ga takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a zaɓen gwamnan jihar na 2027. Uban Dawakin Gombe tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gombe ne, yayin da Chiburosi ya taba jagorantar ƙungiyar masu matsaran…
Read More
Uwargidan gwamnan Nasarawa ta jaddada muhimmancin tarbiyyar yara da mara wa APC baya

Uwargidan gwamnan Nasarawa ta jaddada muhimmancin tarbiyyar yara da mara wa APC baya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Uwar gidan gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullahi Sule ta yi kira na musamman ga mata a faɗin jihar da su ƙara ƙaimi wajen tarbiyyar 'ya'yansu inda tace tarbiyya mai kyau ita ce ginshiƙin zaman lafiya da cigaban al'umma. Tayi wannan kiran ne a ranar Litinin na makon da ake ciki a wani babban taron masu ruwa da tsaki na mata da aka gudanar a ɗakin taro na Banquet Hall, dake gidan gwamnati a Lafia babban birnin jihar. Taron wanda ma'aikatar harkokin mata da cigaban al'umma ta shirya tare da haɗin gwiwar ofishin uwar…
Read More
Hon Sani Liti Yan Kwani ya rasu

Hon Sani Liti Yan Kwani ya rasu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Allah yayiwa Hon Sani Liti Yan Kwani rasuwa bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya. Marigayi Sani Liti ɗan asalin ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina ya taɓa rike muƙamin shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokoki na Katsina. Haka kuma ya riƙe muƙamin shugaban jam'iyyar NNPP na Jihar Katsina kafin daga nan ya koma mai sharhi a harkokin siyasa da na yau da kullum. Ya rasu ya bar mata uku da ya'ya 26 ,tuni akayi jana'izarsa a gidansa.
Read More
Sojoji sun kama ɗan bindiga da ake alaƙantawa da kisan marigayi Janar Rabe

Sojoji sun kama ɗan bindiga da ake alaƙantawa da kisan marigayi Janar Rabe

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar soji ta Operation FANSAN YAMMA, tare da haɗin gwiwar 'yan sa-kai sun kama manyan kwamandojin wata dabar 'yan ta'adda da ta shahara wacce ke da alaƙa da sace wa tare da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a Jihar Katsina. Wani majiyar soji a Gusau, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa, aikin da aka gudanar a ranar Lahadi ya kai ga kama wasu manyan mambobin ƙungiyar da ke aiki ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Kachalla Maha. A cewar majiyar, cikin waɗanda aka kama akwai wani babban kwamanda…
Read More
Hukuma ta kashe gobara sama da 100 tsakanin Janairu da Satumba a Nasarawa

Hukuma ta kashe gobara sama da 100 tsakanin Janairu da Satumba a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Hukumar kashe gobara ta tarayya reshin jihar Nasarawa tace ta amsa kira sama da 100 na gaggawa tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2026 kaɗai. Shugabar hukumar ta jihar Mrs. Eno Nwachukwu ce ta bayyana hakan a ƙarshen makon da ya gabata a Lafiya babban birnin jihar yayin wani gangamin wayar da kai da aka shirya gabanin watannin Ember. Gangamin wanda aka yi da taken “Tsaron Gobara, ƙaura a lokacin gaggawa da horon yadda ake kashe gobara da ba da agajin gaggawa,” an shirya shi ne domin ilimantar da jama’a kan hanyoyin kariya…
Read More
Gwamnatin Nasarawa ta nemi shawarar al’umma don tabbatar da adalci a kasafin kuɗin 2027

Gwamnatin Nasarawa ta nemi shawarar al’umma don tabbatar da adalci a kasafin kuɗin 2027

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi kira ga mahalarta taron shawarwari kan kasafin kuɗi da su bayar da shawarwari masu amfani wajen tantance ayyuka da shirye-shiryen da ya kamata a bai wa fifiko a kasafin kuɗin shekarar 2027. Kwamishinan ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki a jihar Alhaji Ahmed Yakubu Mohammed ne yayi wannan kiran a yayin taron tattaunawa na musamman da al'umma kan kasafin kuɗin 'yan ƙasa na 2026 wato Citizens Budget a turance wanda aka gudanar a ɗakin taro na hukumar bunƙasa zuba jari ta Jihar Nasarawa (NASIDA) da ke kan titin…
Read More
Yadda tsoron saki da abin da mutane za su ce ke tura wasu mata mahalaka

Yadda tsoron saki da abin da mutane za su ce ke tura wasu mata mahalaka

Daga AISHA ASAS  Akwai wata kalma da kusan kowace mace mai aure ta taɓa ji a rayuwarta, musamman a lokacin da wani abu ya rikice a tsakaninta da mijinta: “Ki yi haƙuri.” Wataƙila mahaifiyarta ce ta faɗa mata, ko ƙawarta, ko wata dattijuwa da take ganin ta fi ta sanin rayuwar aure. Wataƙila ma malami ne ya ce mata haka. Kuma a mafi yawan lokuta, ba a faɗi kalmar da mugun nufi ba. Ana faɗarta ne saboda an san cewa aure yana buƙatar haƙuri, domin babu gidan da yake tafiya ba tare da kuskure, sabani da lokutan da ake buƙatar…
Read More
Mun shirya tunkarar zaɓen 2027 – Mansur Gulma

Mun shirya tunkarar zaɓen 2027 – Mansur Gulma

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban yaƙin neman zaɓen karamar hukumar Argungu a ƙarƙashin jam'iyyar ADC Alhaji Mansur Adamu Gulma ya bayyana cewa sun shirya tsaf don tinkarar zaɓe mai zuwa na shekarar 2027. Ya yi wannan bayanin ne a wani taron matasa da aka gudanar a garin Argungu ƙarshen makon da ya gabata. Alhaji Mansur ya ce a fagen siyasa yanzu ba wanda zai sake yaudarar matasa in sha Allahu saboda a baya ana yaudarar mutane musamman matasa da sunan za a taimaka masu wajen samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar su, kuma daga baya a mayar…
Read More
CSACEFA ta yaba wa gidauniyar MISILLI kan sa yaran da ba sa zuwa makaranta

CSACEFA ta yaba wa gidauniyar MISILLI kan sa yaran da ba sa zuwa makaranta

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ƙungiyar Civil Society Action Coalition on Education for All (CSACEFA) reshen Jihar Gombe, ta yaba wa Gidauniyar ci gaban al’umma ta Misilli bisa ƙoƙarin da take yi wajen shigar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin karatu. Mai kula da CSACEFA a jihar, Hajiya Halima Ahmed Mahdi, ta bayyana hakan a wata hira da wakilinmu a Gombe, yayin bikin cika shekaru huɗu da kafuwar gidauniyar da aka gudanar a unguwar Dawaki. Mahdi ta ce ayyukan gidauniyar na taimakawa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, musamman waɗanda suka fito daga iyalai…
Read More