20
Sep
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wata gobara ta tashi a harabar gidan rediyon Gombe wato Gombe Media Corporation (GMC), inda ta lalata wasu sassa na kamfanin tare da ƙone kayayyaki da wasu kadarorin ma’aikata da masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) da ke aiki a wurin. Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:50 na yammacin Asabar, inda ta shafi tsohon ɗakin shirya shirye-shiryen talabijin, sashen kula da na’urori, ɗakin adana kayan rediyo, ofishin daraktan labarai da kuma masaukin ’yan NYSC da ke aikin GMC Radio da Television. Da samun labarin gobarar, jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Gombe da ta…
