ukarofi

12467 Posts
EU na son Kanada ta zama mamba ta musamman a ƙungiyar

EU na son Kanada ta zama mamba ta musamman a ƙungiyar

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai (EU), Ursula von der Leyen, ta ce tana son a buɗe ƙofa domin Kanada ta zama ƙasa ta farko da za ta samu matsayin “mamba ta musamman” a cikin ƙungiyar, a wani sabon yunkuri na ƙara ƙarfafa alaƙar Turai da ƙasar. Von der Leyen ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da Firaministan Kanada, Mark Carney, ya halarci zaman Majalisar Tarayyar Turai a Strasbourg, inda ta gabatar da jawabin shekara-shekara kan halin da ƙungiyar take ciki. Bayan furucin nata, ‘yan majalisar sun tashi tsaye suna tafa mata, yayin da ita da Carney suka rungumi juna.…
Read More
Yadda wata uwa ke lalata da ’ya’yanta a bidiyo don samun kuɗi ta intanet

Yadda wata uwa ke lalata da ’ya’yanta a bidiyo don samun kuɗi ta intanet

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta kama wata mata mai shekaru 36, Anulika Onyeanusia, bisa zargin yin lalata da ’ya’yanta tare da amfani da hotuna ko bidiyon da aka samu daga wannan mummunan aiki wajen neman kuɗi ta intanet. Lamarin ya shiga hannun ’yan sanda ne bayan wani faifan bidiyo mai tayar da hankali ya bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa rundunar ta fara gudanar da bincike. Daga bisani, jami’an ’yan sandan sun gano inda matar take a Onitsha, inda suka kama ta tare da ceto yara huɗu da suke ƙarƙashin kulawarta. Yaran, waɗanda shekarunsu ke tsakanin…
Read More
Hukumar zaɓen Jihar Kebbi ta yi sabon shugaban riƙon ƙwarya

Hukumar zaɓen Jihar Kebbi ta yi sabon shugaban riƙon ƙwarya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ranar 18 ga wannan watan na Satumba, 2026 Sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi na riƙon ƙwarya kwarya Alhaji Muhammad Kaura Dan Hakimi Zagga ya karɓi ragamar jagorancin hukumar daga hannun Honarabul Aliyu Muhammed Mera.Da ya ke jawabi a wajen bikin barin ofis ɗin, Honarabul Aliyu Muhammed Mera mai barin gado ya bayyana cewa a tsawon zaman sa a wannan ma'aikata tun daga 2017, 2019, 2022 har zuwa 2024 an sami nasarorin aiwatar da ayyukan da aka ɗora mata tun kama daga samar da tsare-tsare na gudanarwa ilmantar da al'umma kan…
Read More
Babu dalilin da zai hana Arewa goyon bayan Tinubu a 2027 – Yari

Babu dalilin da zai hana Arewa goyon bayan Tinubu a 2027 – Yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daraktan Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Abdul’Aziz Yari, ya ce babu wani dalili da zai hana al’ummar Arewa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinsa na sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Yari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas, lokacin da ya jagoranci wasu mambobin kwamitin zuwa fadar Oba na Legas, Rilwan Akiolu. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara a zaɓen 2015 da kuma sake zaɓensa a 2019. Ya ce Tinubu…
Read More
2027: Duk da a APC nake ba zan hana mutane na su zaɓi ra’ayin su ba  — Na’Allah

2027: Duk da a APC nake ba zan hana mutane na su zaɓi ra’ayin su ba  — Na’Allah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Na’Allah, ya ce har yanzu ya na cikin jam’iyyar APC, amma zai goyi bayan duk jam’iyyar siyasar da al’ummarsa suka zaba a zaben 2027. Na’Allah ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ ranar Litinin. Tsohon Sanatan ya ce a matsayinsa na ɗan jam’iyyar siyasa kuma mai bin tsarin dimokuradiyya, ba zai tilasta wa al’ummarsa goyon bayan wata jam’iyya da ba sa so ba. Ya ce, “Ina cikin APC. Amma idan saboda wani dalili al’ummata suka yi imanin cewa…
Read More
2027: Gwamnonin APC sun yi watsi da ƙawancen Wike, sun ce ba za su goyi bayan ’yan takarar da ba na APC ba

2027: Gwamnonin APC sun yi watsi da ƙawancen Wike, sun ce ba za su goyi bayan ’yan takarar da ba na APC ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) sun yi watsi da duk wani ƙawancen siyasa ko tsarin da suke ganin zai iya yin barazana ga damar jam’iyyar da ’yan takararta a zaɓen 2027. Gwamnonin sun ce ba za su shiga, goyi bayan ko amincewa da duk wani tsarin siyasa da zai iya raunana APC, yin illa ga ’yan takarar jam’iyyar ko kuma kawo cikas ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Shugaban ƙungiyar Gwamnonin APC, kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana matsayar gwamnonin yayin da yake…
Read More
Oba na Benin ya buƙaci ’yan Nijeriya su sake zaɓar Tinubu a 2027

Oba na Benin ya buƙaci ’yan Nijeriya su sake zaɓar Tinubu a 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Martaba Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa ya kamata a ba shi damar kammala ayyukan da yake yi. Oba Ewuare II ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake karɓar tawagar Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa ta Jam’iyyar APC, wadda Darakta-Janar ɗinta, Abdulazeez Yari, ya jagoranta zuwa fadarsa da ke Benin, Jihar Edo. Sarkin ya ce idan shugaba yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, ya dace a ba…
Read More
2027: ADC ta buƙaci masu zaɓe su kare ƙuri’unsu

2027: ADC ta buƙaci masu zaɓe su kare ƙuri’unsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga masu zaɓe da su guji sayar da kuri’unsu, tare da kare su daga duk wani nau’in magudi a zaɓen shekarar 2027. Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a yayin da take gabatar da ’yan takararta a mazabar Sanata ta Daura, waɗanda za su fafata a zaɓen 2027. An gabatar da ’yan takarar ne a hedikwatar jam’iyyar da ke TBO Kwanar Dabo a Daura, inda shugabannin jam’iyyar, ’yan takara da magoya baya daga sassa daban-daban na jihar suka halarta. Wakilin jam’iyyar a wajen taron, Mataimakin ɗan…
Read More
Bayan doguwar jinya: Yadda Céline Dion ta dawo fagen waƙa

Bayan doguwar jinya: Yadda Céline Dion ta dawo fagen waƙa

Daga AISHA ASAS Wani lokaci rayuwa kan tilasta wa mutum ya tsaya a inda bai shirya tsayawa ba. Ba don ya gaji ba, ba don ya daina son abin da yake yi ba, sai dai saboda jiki ya ce masa ya dakata. Ga mawaƙi ko mawaƙiya, wannan dakatarwar ba abu ce mai sauƙi ba. Murya ba kawai hanyar samun abin yi ba ce; ita ce sana’a, suna, tarihi da kuma hanyar da mutum yake sadarwa da miliyoyin mutane. Don haka, idan cuta ta fara shafar abin da mutum ya gina rayuwarsa a kai, tambayar da ke tasowa ba ita ce…
Read More
Jarumi Olu Jacobs: Ba rabo da gwani ba

Jarumi Olu Jacobs: Ba rabo da gwani ba

Daga AISHA ASAS Wasu jarumai suna fitowa a fim ne domin su ba da labari, amma wasu kuma sukan kai wani matsayi da rayuwarsu a fagen wasan kwaikwayo ta zama wani ɓangare na tarihin masana’antar da suka yi wa hidima. A irin wannan matsayi ne za a iya kallon marigayi Sir Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda duniya ta fi sani da Olu Jacobs, wanda rasuwarsa a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, ta rufe wani babi mai tsawo a tarihin wasan kwaikwayo da fina-finan Najeriya. Olu Jacobs ya rasu yana da shekara 84, kuma ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da…
Read More