ukarofi

12738 Posts
Indonesia da Jamus sun haɗa kai kan batun kafa ƙasar Falasɗinu

Indonesia da Jamus sun haɗa kai kan batun kafa ƙasar Falasɗinu

Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul, ya yi kira ga tsagaita wuta nan take a Gaza da sakin fursunonin da Hamas ke riƙe da su. Ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Indonesia, Sugiono, a birnin Jakarta. Wadephul ya jaddada cewa, mafita guda ɗaya ce ta iya kawo ƙarshen rikicin: wato mafarkin ƙasa biyu da za a cimma ta hanyar tattaunawa. Indonesia, wadda ita ce mafi yawan musulmi a duniya, ta jima tana mara baya ga Falasɗinu kuma ba ta amince da Isra’ila ba. Dukkan ministocin biyu sun tattauna game da ƙalubalen siyasa na duniya da…
Read More
Ranar Agajin ɗan Adama: Caritas ta buƙaci ƙasashen duniya su kai ƙarshen tashin hankali

Ranar Agajin ɗan Adama: Caritas ta buƙaci ƙasashen duniya su kai ƙarshen tashin hankali

A yayin bikin Ranar Agajin Bil-Adama a ranar 19 Agusta, ƙungiyar Caritas Internationalis, wacce ita ce reshen agaji na cocin Katolika, ta yi kira ga shugabannin duniya da su kawo ƙarshen tashin hankali da rikice-rikice da ke addabar al’umma. Caritas ta tuna da mutuwar ma’aikatan agaji 22 a harin bam da aka kai ofishin Majalisar ɗinkin Duniya a Baghdad a 2003, wanda ya zama dalilin kafa wannan rana ta tunawa. A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa, sama da ma’aikata 380 aka kashe a fagen agaji a shekara ta 2024 a ƙasashe daban-daban, kuma lamarin na ƙara ta’azzara a 2025.…
Read More
Saudiyya ta ƙaddamar da sabon tsarin Umrah don sauƙaƙe ziyara

Saudiyya ta ƙaddamar da sabon tsarin Umrah don sauƙaƙe ziyara

A ranar 20 ga Agusta 2025, gwamnatin Saudi Arabia, ta hannun Ma’aikatar Hajj da Umrah, ta ƙaddamar da wani sabon tsarin zamani mai suna “Nusuk Umrah”, wanda ya shafi dukkan musulmi da ke son gudanar da ziyarar Umrah daga ko ina a duniya. Sabon tsarin yana bai wa masu niyyar zuwa Umrah damar yin rajista da neman visa ta yanar gizo kai tsaye, tare da haɗa shi da sauran sabis na balaguro da masauki a Makkah da Madina a wuri guda. Wannan yana nufin cewa, ba sai mutum ya riƙa bi ofis-ofis daban-daban ba, dukkan ayyukan za a yi su…
Read More
 Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza

 Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza

Sakatare-Janar na Majalisar ɗinkin Duniya (MDD), António Guterres, ya fitar da sanarwa a jiya Alhamis 21 ga Agusta 2025 inda ya yi kira da a dakatar da dukkan hare-hare a Gaza nan take, musamman bayan da hukumomin Isra’ila suka bayyana aniyarsu ta ƙaddamar da sabon babban farmaki a Gaza City. Guterres ya bayyana cewa, duk wani sabon farmaki a wannan lokaci zai zama mummunar barazana ga rayukan fararen hula, musamman la’akari da cewa Gaza ta riga ta kasance cikin halin ƙunci da yunwa bayan watanni na tashin hankali da kullen da Isra’ila ta yi. Sakatare-janar ɗin ya kuma yi kira…
Read More
2027: Gargaɗin INEC game da fara yaƙin neman zaɓe

2027: Gargaɗin INEC game da fara yaƙin neman zaɓe

A kwanakin baya ne Hukumar Zaɓe Mai Zamanta Kanta ta Nijeriya (INEC) ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji fara yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓukan 2027, inda ta bayyana hakan a matsayin karya dokar zaɓe. Gargaɗin na INEC ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar tarukan siyasa a faɗin ƙasar, da sanya allunan hotunan ‘yan takara a allunan talla. Duk da cewa fara yaƙin neman zaɓe da ‘yan siyasar Nijeriya ke yi ba sabon abu ba ne, amma lamarin ya ƙara ta’azzara a siyasar da ke faruwa a halin yanzu da ayyukan gamayyar jam’iyyar…
Read More
 Ɗaurarre a gidan yari ya lashe zaɓen cike-gurbi na majalisa a Jihar Enugu 

 Ɗaurarre a gidan yari ya lashe zaɓen cike-gurbi na majalisa a Jihar Enugu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, INEC,  ta bayyana wani ɗan gidan yari, Bright Ngene na jam'iyyar Labour da aka ɗaure saboda satar naira miliyan 15, a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar Enugu ta Kudu da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata. Mai magana da yawun hukumar a jihar, Sam Olumekun ya gabatar da sakamakon, bayan soke wanda aka yi a 2023. RFI ya rawaito cewa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara alƙali ya ɗaure Ngene shekaru 7 a gidan yari, saboda samunsa da laifin satar Naira miliyan…
Read More
Ƙungiyar Mar’atussaliha ta ziyarci gidan gyaran hali da ke Argungu 

Ƙungiyar Mar’atussaliha ta ziyarci gidan gyaran hali da ke Argungu 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Shugabar ƙungiyar Mar'atussaliha mai rajin kare mutuncin marayu da zawarawa da ke reshen ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Hajiya Mariya Muhammad Mera ta yi kira ga 'yan uwa da ke zaman fursuna da su ɗauki zaman a matsayin jarrabawa daga Allah. Ta yi wannan kiran ne a yayin wata ziyara da ƙungiyar ta kai gidan gyaran hali da ke garin Argungu makon da ya gabata. Hajiya Mariya Muhammad Mera ta yaba wa ma'aikatan hukumar bisa ga buɗe makarantar Islamiyya da kuma koyon sana'o'in hannu domin koyon sana'o'i daban-daban da za su riƙe bayan kammala wa'adin…
Read More
Akwai buƙatar iyaye su rinƙa ziyarar makarantun ‘ya’yansu – Shugaban makarantar sakandaren Daneji                  

Akwai buƙatar iyaye su rinƙa ziyarar makarantun ‘ya’yansu – Shugaban makarantar sakandaren Daneji                  

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano  Malam Amin Abdullahi shi ne shugaban makarantar sakandare da ake kira Daneji Amintacciya da ke uguwar Daneji wadda tsohon A.G na ƙasa Ahmed Idris ya gina wa al'umma a ƙaramar hukumar birnin Kano da kewaye. Shugaban Makarantar Malam Aminu ya ce akwai buƙatar iyayen ɗalibai a ko'ina su riƙa kai ziyara makarantun 'ya'yansu don ganin yadda yaransu ke ɗaukar darasi wanda hakan zai ƙarfafawa malamai da ɗalibai gwiwa a makarantu, inda kuma ya shawarci iyaye kansu su bai wa hukumar makaranta da ƙungiyar iyaye da malaman makaranta haɗin kai ta hanyar biyan kuɗin PTA domin…
Read More
’Yan Nijeriya miliyan 31 na fama da ƙarancin abinci — MDD

’Yan Nijeriya miliyan 31 na fama da ƙarancin abinci — MDD

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar kula da ayyukan jinƙai ta Majalisar ɗinkin Duniya, ta nuna damuwa kan yadda matsalar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Nijeriya. Hukumar ta ƙiyasta cewa sama da mutane miliyan 31 na fama da ƙarancin abinci a faɗin Nijeriya. Hukumar ta ƙara da cewa akwai yara ƙanana sama da miliyan 10 ’yan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. Wannan bayani ya fito ne a wani taro da Gwamnatin Tarayya tare da hukumar suka shirya a Abuja, domin bikin Ranar Jinƙai ta Duniya…
Read More
NAHCON ta jaddada tsayuwarta kan gaskiya da riƙon amana a yayin jita-jitar binciken almundahana

NAHCON ta jaddada tsayuwarta kan gaskiya da riƙon amana a yayin jita-jitar binciken almundahana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa tana nan akan tsarin gaskiya da riƙon amana kamar yadda dokokin da suka kafa ta suka gindaya tare da buɗe kofofinta ga fayyace gaskiya da kuma nesanta daga duk abinda zai tozarta ayyukan hukumar. Hukumar NAHCON ta fidda sanarwar yin kira ga ‘yan Nijeriya da mutane bakiɗaya da su yi watsi da duk wani rahoto da ke yin cin fuska ga hukumar da zarge-zarge game da yyukan hukumar har sai sun samu tabbacin rahoto daga hukumomin da ke bincike akan duk wata badaƙala da ake zargin…
Read More