ukarofi

12738 Posts
Ƙungiyar Mata Marubuta ta shirya taron bita kan rubutun diramar radiyo

Ƙungiyar Mata Marubuta ta shirya taron bita kan rubutun diramar radiyo

DAGA MUKHTAR YAKUBU A ci gaba da ƙoƙarin tafiya da zamani cikin harkar rubutun labari, ƙungiyar Mata Marubuta ta Women of Words ta gudanar da taron bita na wuni biyu domin koyar da mambobin ƙungiyar dabarun rubutun labarin wasan kwaikwayo na rediyo. Taron dai an gudanar da shi ne a ɗakin karatu na Murtala Muhammad da ke kan titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano, inda ya samu halartar 'yan ƙungiyar daga ciki da wajen Kano. Da take yi mana bayani a kan manufar shirya taron. Marubuciya Sanah S Matazu ta bayyana mana manufar taron bitar da cewa, "To yadda…
Read More
Abin da ya sa na shirya kasuwar Bajekolin littattafai – Kabiru Jammaje

Abin da ya sa na shirya kasuwar Bajekolin littattafai – Kabiru Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU A ranar 27 ga Yunin da ya gabata ne aka ci kasuwar rana guda ta Bajekolin littattafai ko gwanjo littafai, wanda fitaccen malamin Turanci Malam Kabiru Musa Jammaje ya shirya wanda dunbun jama'a malamai da kuma ɗaliban ilimi suka halarci wajen bajekolin littattafan domin sayen littattafan wanda aka sayar da su cikin farashi mai sauƙi. Wani abin burgewa kasuwar Bajekolin littattafan ta tsawon wuni guda ce da aka shirya za a bajekolin littattafai sama da 450 domin sayarwa ga masu buƙata.  To sai dai kasuwar ta ci ta cinye a ƙasa da sa'o'i uku na fara bajekolin,…
Read More
Ƙungiyar NUJ ta Zamfara ta taya sabon Sarkin Gusau murna

Ƙungiyar NUJ ta Zamfara ta taya sabon Sarkin Gusau murna

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Zamfara ta taya Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello murnar naɗin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gusau (Sarkin Katsina Gusau) na 16. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar da sakataren ƙungiyar, Ibrahim Musa Maizare da Ibrahim Ahmad Gada. "Wannan muhimmin abu mai cike da tarihi ya nuna wani muhimmin lokaci a tarihin al'ummarmu yayin da muke murnar hawan sabon shugaba kan wannan matsayi mai daraja. Allah ya ja zamanin Sarkin Katsinan Gusau". "A matsayinka na sabon…
Read More
‘Yan sanda sun sami nasarar ceto mutane 28 a Katsina

‘Yan sanda sun sami nasarar ceto mutane 28 a Katsina

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙokarin da ta ke na yaƙi da ta'addanci, 'yan sanda sun sami nasarar ceto mutane 28 da ga hannun 'yan bindiga a ƙaramar hukumar Sabuwa. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai a Katsina. Ya bayyana cewa wani matashi ya kwarmatawa ofishin 'yan sandan yankin cewa 'yan bindiga ɗauke da mayan bindigogi sun tare hanyar Sabuwa zuwa kaya daidai kwanar Inno,inda suka tafi da mutane 14. DSP Sadiq ya ce nan take DPO da…
Read More
Wararrun ‘Yan Majalisar Zamfara za su binciki yadda gwamnatin ke cire kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Wararrun ‘Yan Majalisar Zamfara za su binciki yadda gwamnatin ke cire kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wararrun 'Yan Majalisar Jihar Zamfara ƙarkashin jagorancin Kakakinta Hon. Bashir Aliyu Gummi sun duƙufa wajen bincikar yadda ake ci gaba da cire kashi 3% daga cikin kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi 14 da aka ware domin ɗaukar nauyin kuɗin jami’ar Jihar Zamfara, dake Talata Mafara. Hon. Nasiru A. Maru ya bayyana haka a cikin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban majalisar a zamansu da aka gudanar a Gusau yau Talata. A cewar sa, cire kuɗaɗen ya haramta, kuma ya saɓawa ƙa’ida, yana mai cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomin an basu ne domin samar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta fara bayar da maganin zazzaɓin ‘typhoid’ kyauta

Gwamnatin Katsina za ta fara bayar da maganin zazzaɓin ‘typhoid’ kyauta

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai da al'adu Dr Bala Salisu Zango ya bayyana cewa an zaɓi cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar da aka keɓe za a fara bada maganin. Cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar da aka zaɓa sune babban asibitin Katsina, babban asibitin ƙwararru na Amadi Rimi Katsina, asibitin Turai Yar’adua , babban asibitin Jibia, da babban asibitin Funtua. kwamishinan ya bayyana cewa hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya ta Jihar Katsina, ta sanar da cewa cutar typhoid ya fi tsananta a ƙananan hukumomin Katsina, Kaita, Batsari, Jibia, da Funtua.…
Read More
Ambaliyar Adamawa: Adadin wanda suka rasu ya kai 23

Ambaliyar Adamawa: Adadin wanda suka rasu ya kai 23

Daga USMAN KAROFI a Abuja Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da mutuwar mutane 23 sakamakon ambaliya da ta faru a ranar Lahadi a wasu sassan jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin bayan isa filin jirgin sama na Yola da misalin ƙarfe 1:45 na rana, inda ya wuce kai tsaye zuwa yankunan da ambaliyar ta fi shafa a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu. A wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa wadanda suka rasa muhallansu a sansanin wucin gadi da ke makarantar firamare ta Yelewa, Gwamna Fintiri ya nuna alhini matuka tare da tabbatar musu…
Read More
An buƙaci samar da kason kuɗi a kasafi domin kula da makarantun addini na Katsina

An buƙaci samar da kason kuɗi a kasafi domin kula da makarantun addini na Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Babban Jojin Jihar Katsina, mai Shari’a Musa Ɗanladi Abubakar, ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina da ta samar da doka da za ta tanadi wani kaso na musamman a cikin kasafin kuɗin kowace shekara domin kula da makarantun koyar da ilimin addinin Musulunci a faɗin jihar. Ya faɗi haka ne a yayin bikin walimar saukar Alƙur’ani mai girma da ɗaliban makarantar "Al-Ilham Islamic College" suka gudanar, makarantar da aka kafa bisa gudummawar dattijo kuma mai kishin addini, Alhaji Usman Sarki, a unguwar Ƙofar Guga cikin garin Katsina. Mai Shari’a Musa Ɗanladi ya jaddada cewa…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da rabon gidan sauro da magunguna

Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da rabon gidan sauro da magunguna

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wani babban yunƙuri na yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro a faɗin jiha.An ƙaddamar da magunguna da gidan sauro a fadar hakimin Mashi da ke garin Mashi. Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya , Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana gamsuwarsa da irin yadda ake ci gaba da ƙoƙari wajen daƙile cutar a sassa daban-daban na jihar. Gwamnan ya kuma yabawa ƙoƙarin gwamnatin sa wajen inganta lafiyar al’umma da kare dukiyoyinsu. Shugaban ƙaramar hukumar Mashi, Hon. Salisu Kallah, a jawabinsa na maraba, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka…
Read More
Gwamna Dauda ya naɗa sabon Sarkin Gusau

Gwamna Dauda ya naɗa sabon Sarkin Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon sarki kuma Sarkin Masarautar Gusau. Da yake sanar da hakan, sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa shawarar kwamitin naɗi da sarakunan masarautar Gusau suka bayar, bisa ga tsarin al'ada da kuma dokokin da suka dace. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Gusau na 16, bayan rasuwar mahaifin sa, Mai Martaba Dokta Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025, bayan shafe shekaru…
Read More