ukarofi

12738 Posts
Al’ummar garin Mai’adua na godiya ga Gwamna Raɗɗa bisa mai da asibitin garin zuwa babban asibiti

Al’ummar garin Mai’adua na godiya ga Gwamna Raɗɗa bisa mai da asibitin garin zuwa babban asibiti

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwanan baya ne gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da mai da wasu ƙananan asibitocin zuwa manya asibitoci a jihar. Asibitin garin Mai'adua na ƙaramar hukumar Mai'adua na ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗaga darajar su zuwa babban asibiti. Kan haka al'ummar yankin suka miƙa godiyar su ga gwamna Dikko Raɗɗa bisa wannan abin alheri da yayi masu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, tsohon kakakin majalisar dokoki RT Hon Ya'u Gwajo Gwaji ya bayyana wannan matakin da gwamnan ya ɗauka, "ya nuna irin damuwarsa da ƙudirin sa na inganta harkokin kiwon…
Read More
Hare-haren ta’addanci na raguwa a Katsina lokacin Tinubu – Wazirin Katsina

Hare-haren ta’addanci na raguwa a Katsina lokacin Tinubu – Wazirin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wazirin Katsina, Ibrahim Idah, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindinga sun ragu matuƙa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman a Jihar Katsina. Wazirin Katsina ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wurin taron haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin Arewa, Idah ya ce Tinubu ya cika alƙawarin yaƙi da bazuwar makamai, wanda hakan ke haifar da raguwar hare-hare idan aka kwatanta da shekarun baya kamar yadda jaridar Premium Times ta sanar. Ya kuma buƙaci a ƙarfafi rundunar tsaron sa-kai da makamai masu ƙarfi domin ƙarfafa tsaro, sai dai shugaban NDLEA, Buba Marwa,…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya ki ke. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a ƙirga don sanar da ke tawa damuwa saidai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi min mummunar fahimta. Wallahi tun 'last year' mahaifiyar 'best friend' ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita. tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauke ni duk lokacin da babu karatu, ko mu je 'hotel' ko ta kai ni wani gida. To…
Read More
Gaza ga albarusai ga yunwa

Gaza ga albarusai ga yunwa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Yayin da albarusan sojojin Isra’ila ke dira a kan al’ummar Gaza a gefe guda kuma yunwa na ragargazar mazauna yankin. Kimanin mata da yara dubu 100 ke fama da mawuyacin yanayi na ƙarancin abinci. Babban jami’in hukumar samar da abinci da duniya Ross Smith ya ce Gaza na gab da aukawa mummunan yanayin ƙarancin abinci ko kai tsaye a ce yunwa. Smith ya ce baa bun da ke tafiya a Gaza don ba batun kasuwanni ko a ce wata hada-hada ga shi an takaita hanyoyin isar da kayan agaji. A nan jami’in ya nuna haƙiƙa abun…
Read More
Sha’iran Gombe sun karrama shugaban ƙaramar hukumar Gombe

Sha’iran Gombe sun karrama shugaban ƙaramar hukumar Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe A wani biki mai cike da tarihi da nishaɗi, ƙungiyar sha'irai ta Jihar Gombe ta gudanar da gagarumin taro inda ta karrama shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmadu Haruna, bisa namijin ƙoƙarinsa wajen tallafawa addini da kuma bunƙasa harkar sha'irai a faɗin jihar. An gudanar da wannan biki a babban zauren ƙungiyar, inda manyan malamai, shugabannin addini, fitattun mawaƙa da ɗaruruwan mambobin ƙungiyar suka taru domin nuna farin ciki da girmamawa ga jagoran wanda ya zama ginshiƙin ci gaban al’umma. Shugaban ƙungiyar sha'irai, Malam Salisu Awadatu, yayin gabatar da lambar yabo ya bayyana…
Read More
Sanatocin Arewa sun yi allawadai da kisan mutane a Zamfara

Sanatocin Arewa sun yi allawadai da kisan mutane a Zamfara

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu fararen hula 35 a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara. Cikin wani saƙon jaje da ƙungiyar ta aike ranar Laraba a Abuja, shugaban ƙungiyar Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, sanatan Katsina ta tsakiya, ya jajanta wa al'ummar yankin musamman iyalan waɗanda lamarin ya shafa. A farkon makon nan ne 'yan bindiga suka yi wa wasu mutanen yankin yankan rago duk kuwa da biyan kuɗin fansa da aka ce iyalansu sun yi domin kuɓutar da su. Jihar Zamfara na daga cikin…
Read More
Kotu ta yanke hukuncin kisa kan waɗanda suka kashe tsohon kwamishina a Katsina

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan waɗanda suka kashe tsohon kwamishina a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Babbar Kotun Jihar Katsina mai lamba 9, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a I.I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu da aka samu da laifi a kisan gilla da aka yi wa tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Katsina, marigayi Rabe Nasir, a shekarar 2021. Kotun ta tabbatar da cewa Shamsu Lawal tsohon mai gadin marigayin da Tasi’u Rabi’u wanda ke kuku a gidan mamacin sun bai wa Rabe Nasir abinci mai guba wanda ya kashe masa jiki don ya gaza komai sai yanda akai da shi, wanda ya janyo mutuwarsa, bayan an samu damar…
Read More
An buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a jihar

An buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokokin Katsina ta nemi gwamnati ta gina hanyar ruwa a Mara-Zamfarawa, Ɗanmusa. Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga ɓangaren zartarwa da ta gina hanyar ruwa a yankin Mara-Zamfarawa da ke cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa, domin kare hanyar daga ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa da wanda ke haddasa lalacewar hanya da kawo cikas ga zirga-zirgar jama'a da ababen hawa. Wannan kira ya biyo bayan ƙuduri da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗanmusa, Hon. Aminu Garba, ya gabatar, inda ya nemi majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa na gina hanyar…
Read More
Majalisar Dokokin Zamfara ta buƙaci Gwamna Lawal ya dakatar da shugaban ZAROTA

Majalisar Dokokin Zamfara ta buƙaci Gwamna Lawal ya dakatar da shugaban ZAROTA

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tattauna tare da amincewa da a dakatar da shugaban hukumar ZAROTA. Sanarwar na ƙunshe ne a wata takarda da sakataren hulɗa da ƴan jaridu Bello Madaro ya rattaɓa wa hannu a yau Laraba. Sanarwar ta bayyana cewar, Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara a zamanta na yau Laraba ta tattauna tare da kira ga gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya dakatar da shugaban hukumar ZAROTA na jihar MB Musa bisa zargin rub da ciki da kuɗaɗen hukumar. Hakan ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da ɗa"a na majalisar ƙarƙashin…
Read More
Bayan rubutu Ina faɗakarwa da sasanta tsakanin masoya – Sakina Isma’il

Bayan rubutu Ina faɗakarwa da sasanta tsakanin masoya – Sakina Isma’il

(Ci gaba daga makon jiya) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  MANHAJA: Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu akai, kuma wanne lokaci ne ki ka fi jin daɗin yin rubutu? SAKINA ISMA'IL: Ta hanyar yin tunani da nazari kan al'amuran da ke faruwa a inda nake, sai in zauna in tsara labarin cikin basirar da Allah ya bani.  Wanne alheri ki ka taɓa samu a dalilin rubutu? Gaskiya babu wani abu da na taɓa samu muhimmi daga rubutun da nake yi, sai arziƙin jama'a da masoya da kullum suke sa min albarka da addu'o'in fatan alheri, bisa yadda…
Read More