ukarofi

12738 Posts
Yadda uwargidan shugaban ƙasa ta ba da gudunmawar biliyan N15 cikin shekaru biyu

Yadda uwargidan shugaban ƙasa ta ba da gudunmawar biliyan N15 cikin shekaru biyu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A wani abin da ake ganin ya zama tarihi na karimci da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin siyasar Nijeriya, uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da gudunmawar sama da Naira Biliyan 15 ga waɗanda bala’o’i, iyalai da suka rasa matsugunansu, zawarawa, mata, da kuma tsofaffi a cikin shekaru biyu kacal ta hanyar aikin ‘Renewed Hope Initiatiɓe’ (RHI). A ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, ta sake fitowa fili yayin da ta sanar da bayar da gudunmawar Naira Buliyan 1 a jihar Benuwe, wanda aka yi niyya ga waɗanda harin Yelewata ya…
Read More
Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina

Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun riƙa kashe mazauna ƙauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa ƙauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar ɗan Marka, da Sabon Gida…
Read More
Anyi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dawo teburin tattaunawa da jami’an kiwon lafiya

Anyi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dawo teburin tattaunawa da jami’an kiwon lafiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamred Mannir Suleiman mamba na ƙungiyar jami'an kiwon lafiya na manyan makarantun harkokin lafiya ta ƙasa yayi wannan kira. Ya nuna damuwarsa game da yajin aikin na gargaɗi da yace ya jefa marasa lafiya a asibitoci na gwamnatin tarayya a Katsina da Daura cikin mawuyacin hali. Kwamred Suleiman wanda tsohon shugaban ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya reshen Jihar Katsina ya zargi gwamnatin tarayya da karya alƙawari da tayi da ma'aikatan. "Gwamnatin tarayya ta gaza biyan sabon albashi na Naira dubu 70 da ma'aikatan,mai makon haka sai ta ce dubu 40 za su biya wanda wannan rashin…
Read More
Akasarin matsalar tsaro a Katsina daga garuruwa suke faruwa, inji kwamishinan tsaro

Akasarin matsalar tsaro a Katsina daga garuruwa suke faruwa, inji kwamishinan tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a gidan Gwamnatin Katsina. Ya ce duk yawancin kayyakin da 'yan bindiga ke amfani da su wajen aikata ta'addanci daga garuruwa ake kai masu. Dr Ɗanmusa ya bada misali da man fetur da yace ana kai masu a maɓoyan su a da daji kan kowane litan mai ɗaya ana sai da masu a kan Naira 3000. Haka ma baburan hawa da suke amfani da shi,kayan abinci,lemun ƙwalba,bindigogi, harsashi, miyagun ƙwayoyi da rigar sojoji duk daga gari…
Read More
Kebbi:  Kamfanonin  haƙar ma’adanai na cin karensu ba babbaka

Kebbi:  Kamfanonin  haƙar ma’adanai na cin karensu ba babbaka

Daga JAMILU GULMA, a Kebbi  Al'ummar yankin garuruwan Libata da Lokon-Uba da Kabiriba da sauran ƙananan ƙauyuka da ke ƙaramar Hukumar Mulki ta Ngaski da ke Jihar Kebbi sun koka bisa ga yadda kamfunnan haƙar ma'adanai a yankin ke cin karen su ba babbaka yayin da aka mayar da al'ummomin yankin ’yan kallo ba tare da wani ihsani ba ko samar da abubuwan more rayuwa ba. Malam Sani Aliyu daya ɗaga cikin matasan yankin kuma mai sana'ar kabu-kabu (acaba)ya bayyana wa wakilinmu cewa, waɗannan mutanen sun daɗe suna cin karen su ba babbaka a yankin wajen haƙar ma'adanai da su…
Read More
‘Yan Majalisar Katsina sun gabatar da kuɗirin gaggawa kan matsalar tsaro a jihar

‘Yan Majalisar Katsina sun gabatar da kuɗirin gaggawa kan matsalar tsaro a jihar

' Daga UMAR GARBA a Katsina ‘Yan majalisar dokokin Katsina sun bayyana damuwa kan ƙaruwan ayyukan ‘yan bindiga a yankuna da dama na jihar, duk kuwa da sulhun da aka yi dasu. Majalisar dokokin Katsinan ce ta bayyana damuwa kan yadda tsaron ke ƙara taɓarɓarewar a zamanta na Larabar nan, wanda shugabanta Hon. Nasir Yahaya-Daura ya jagoranta. Yayin zaman ne, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma, Alhaji Muhammad Abubakar Khamis ya gabatar da ƙudirin da ke buƙatar ɗaukar mataki na gaggawa. Abubakar Khamis ya yi kira ga gwamnatin jihar a kan ta ƙara zage damtse wajen yaƙi da matsalar…
Read More
Ambaliyar ruwa ta sake mamaye Maiduguri

Ambaliyar ruwa ta sake mamaye Maiduguri

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri Wani ruwan sama mai kama da bakin-ƙwarya, wanda ya ɗauki sama da awanni uku ya na sauka a birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, yayin da hakan ya jawo ambaliyar ruwa, wanda ya tilasta jama'a da dama a wasu unguwanni ƙauracewa matsugunansu. Wasu daga cikin unguwannin da al'amarin ya fi shafa sun haɗa da Damboa road, Moduganari, Ngomari, haɗi da wasu sassa a birnin, wanda sakamakon haka su ka bar gidajensu tare da neman mafaka a gidajen dangi da abokai. Wani mazaunin unguwar Damboa Road; bayan gidan Indimi, ya bayyana cewa suna cikin fargabar yuwuwar…
Read More
ZAWFOG ta ƙaddamar da kamfen na shuka bishiyoyi da jan kunnen al’umma kan sare itatuwa

ZAWFOG ta ƙaddamar da kamfen na shuka bishiyoyi da jan kunnen al’umma kan sare itatuwa

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Gidauniyar Zakka da Waqf ta Jihar Gombe (ZAWFOG) ta ƙara azama wajen yaƙi da sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba, inda ta ƙaddamar da kamfen na shuka bishiyoyi karo na bakwai a ƙauyen Majidadi, ƙaramar hukumar Shongom. Shugaban gidauniyar, Dakta Abdullahi Abubakar Lamido, ya bayyana sare bishiyoyi ba tare da sake dasu ba a matsayin “mummunar ɓarna ga muhalli” wadda ke haifar da ambaliya, zaizayar ƙasa da sauyin yanayi. “Sare bishiya ba tare da sake shuka ba, laifi ne ga halittar Allah. Musulunci ya koyar da mu mu kula da muhalli, kuma kowace bishiya…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta amince da sabuwar dokar masarauta

Majalisar Dokokin Katsina ta amince da sabuwar dokar masarauta

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Amincewa da dokar ya biyo bayan yima dokar karatu na uku, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin ta Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura. Majalisar ta fara karanta ƙudirin ta yin dokar karatu na farko dana biyu a zaman majalisar, wanda majalisar ta ɗauki tsawon wuni tana tafka mahawara kan dokar, kafin daga bisani ta amince da ita. Dokar wadda ɓangaren zartarwa na jihar ya buƙaci majalisar tayi ta shafi sa ke fasalin harkokin masarautar Katsina da kuma sa ke fasalin majalisar sarakuna na Jihar Katsina. A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta kai wa…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 23.8 wajen ayyukan raya ƙasa

Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 23.8 wajen ayyukan raya ƙasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar zartarwa ta Jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da ayyukan raya ƙasa na sama da Biliyan N23.8 a fannin lafiya, tsaro, hanyoyi, da otel-otel. Majalisar ta amince da ɗaukaka matsayin cibiyar kiwon lafiya ta Mai'adua a Ƙaramar hukumar Mai'adua zuwa babban asibiti (General Hospital) a kan kuɗi Naira biliyan 1.3. Kwamishinan ayyuka da gidaje, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Malam Farouk Lawal Joɓe wanda gwamna Dikko Raɗɗa ya halarta ta yanan Gizo. Haka kuma kwamishinan…
Read More