ukarofi

12738 Posts
 Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

 Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

A baya-bayan nan Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama ƙwayoyin Tramadol biliyan 1.3 da kwalaben Codeine miliyan 4.4 tsakanin watan Janairun 2024 zuwa Yunin 2025. Marwa ya bayyana hakan ne a yayin wani zama na musamman a taron tattaunawa na kwana biyu kan haɗin gwiwar gwamnati da ’yan ƙasa da aka yi ranar Talata a Kaduna. Ya kuma yaba da irin gagarumin nasarorin da aka samu ga tallafin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya baiwa hukumar. “Tsakanin Janairu 2024 zuwa Yuni 2025, mun kama sama da…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta kammala titin jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Kano a shekarar 2026 – Minista

Gwamnatin Tarayya za ta kammala titin jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Kano a shekarar 2026 – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Sufuri na ƙasa, Sa’idu Alkali, ya bayyana cewa aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano zai kammala nan da shekarar 2026, inda ya bayyana cewa aikin wanda ya tsaya a kashi 15 cikin 100 kafin zuwan gwamnatin Tinubu, yanzu ya kai kashi 53 cikin 100. Ya sanar da hakan ne yayin jawabinsa a taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna. Alkali ya ce yankin Arewa na daga cikin mafi yawan waɗanda ke cin moriyar ayyukan ci gaban ababen more rayuwa na gwamnatin Tinubu…
Read More
A yi dokar da za ta hana ‘yan siyasa sauya sheƙa daga jam’iyyar da aka zaɓe su – Dankaka Bebeji

A yi dokar da za ta hana ‘yan siyasa sauya sheƙa daga jam’iyyar da aka zaɓe su – Dankaka Bebeji

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Gyaran tsarin mulki da shigar da sabbin dokoki abu ne mai kyau da ya kamata a riƙa yi lokaci lokaci saboda abubuwa na canzawa daga wani ƙarni zuwa wani. Hon. Dankaka Husaini Bebeji jigo a jam'iyyar NNPP mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara a ofishin mataimakin Gwamna ne ya bayyana hakan. Ya ce abinda aka yi a baya watakila ba zai yiwu ba a yanzu ya kamata a ce ana samun lokaci ana sake tattaunawa a sake duba irin dokokin da suka daɗe da ba su yi daidai da  zamani ba a sauya su…
Read More
Mai bai wa gwamnan Kebbi shawara ya ajiye muƙaminsa, ya canja sheƙa zuwa ADC 

Mai bai wa gwamnan Kebbi shawara ya ajiye muƙaminsa, ya canja sheƙa zuwa ADC 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Honarabul Abdullahi Hassan Tsamiya ɗaya daga cikin manyan masu bai wa gwamnan Kebbi shawara kuma jigo a siyasar ƙaramar hukumar mulki ta Argungu da ke jihar Kebbi ya ajiye muƙamin sa tare da sanar da ficewarsa daga Jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta ADC. Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sa a ranar Lahadin da ta gabata da aka raba wa manema labarai. Takardar ta bayyana cewa Honarabul Abdullahi Hassan ya ajiye mukamin sa ne bayan wani nazari da ya yi a kan rashin adalci da…
Read More
Muna farin ciki da digirin girmamawa da Jami’ar North West ta ba Marigayi Ɗantata  – Mustapha AJ

Muna farin ciki da digirin girmamawa da Jami’ar North West ta ba Marigayi Ɗantata  – Mustapha AJ

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Sakataren Maragayi Alhaji Aminu Ɗantata, Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu ya bayyana cewa su da suka kasance tare a lokacin rayuwar Maragayi shi da iyalan sa da masoyansa sun kasance suna farin ciki da wannan digirin girmamawa da Jami'ar Norhwest NWU ta bashi bayan rasuwarsa bata fasa cika alƙawarin da ta yi ba na ba shi wannan digirin tun yana raye. Ya ce wannan kyautatawa da wannan jami"a ta yi ya sake sabunta musu alhinin rashin sa da kuma farin ciki na cewa alkairinsa da mu'amalarsa da kuma yabon da wannan jami'a da sauran al'umma suke…
Read More
Mutum tara sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Mutum tara sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa. Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne. Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke ƙaramar Hukumar Taura. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis. Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin.…
Read More
Ya kamata Gwamna Abba ya dinga zama da ƙananan ƙungiyoyi – Shugaban masu shayi na Kano

Ya kamata Gwamna Abba ya dinga zama da ƙananan ƙungiyoyi – Shugaban masu shayi na Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An bayyana cewa da a ce Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai ɓullo da tsarin zaɓo ƙananan ƙungyoyi na ƙasa waɗanda suke tare da jama'a 20 duk wata a zauna da su ko da wata uku ne a ce ana gayyato ƙungiyoyi daban-daban a ba su dama su bai wa gwamnatin shawara a basirar su da tunaninsu hakan zai kawo cigaba domin ɗan ƙanƙanin lokaci an zauna da ƙungiyoyi masu yawa har ma da manyan in ta kama duk da yake su ban sani ba ko ana zama da su amma dai ƙungiyoyi irin…
Read More
Koyi da Gwamna Abba ya sa muke kiran Ciyaman ɗin Fagge gatan ilimi – Hon. Ibrahim Sallau

Koyi da Gwamna Abba ya sa muke kiran Ciyaman ɗin Fagge gatan ilimi – Hon. Ibrahim Sallau

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Malam Ibrahim Sallau Ibrahim, ya bayyana cewa yadda shugaban ƙaramar hukumar fagge Hon Salisu Usman masu ke yin koyi da gwamna Kano Abba Kabir wajen bunƙasa ilimi a kowani mataki shi ne yasa muke cewa shugaban ƙaramar Hukumar Mista Education ko kuma Gatan Ilimi domin kuwa makarantu firamare 246 da kuma ƙananan makarantun sakandare 51 na ƙaramar hukumar ba wacce bata san gwamna Abba yazo ba haka kuma babu wacce bata san Hon Salisu Usman Masu ne shugaban ƙaramar hukumar Fagge wannan kuma na da alaƙa ne da…
Read More
Wajibi ne kowannen mu ya yi iya ƙoƙari wajen kare martabar Ma’aikin Allah – Da’iratuh Shurafa’u

Wajibi ne kowannen mu ya yi iya ƙoƙari wajen kare martabar Ma’aikin Allah – Da’iratuh Shurafa’u

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban ƙungiyar Da'iratuh Shurafa'u  Malam Sharu Aminu Salga wanda akafi sa ni da Baba Sharu  ya bayyana cewa wajibi ne alummar musulmi ko da ga wacce ƙungiya kake ko fahimta ta addini to wajibi ne ka fito ka bayyana goyan bayanka wajen kare martabar maaikin Allah Annabi Muhammadu Alahimmusalatu Wassalam domin kuwa wajibi ne mu akan mu mu kare martabar maaikin Allah da ahalinsa wanda bazamu yadda wasu mutane su dinga maganganu akan maaikin Allah ba yadda suka gadama ba kuma abin takaici shi ne anyi irin wannan a Bauchi wanda wani yace baya neman…
Read More
Utomi ya buƙaci a soke rukunin Band A na lantarki

Utomi ya buƙaci a soke rukunin Band A na lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Masanin Tattalin Arziki na Siyasa, Farfesa Pat Utomi, ya ce ya kamata Nijeriya ta sake inganta dabarun samar da wutar lantarki na Band A, yana mai cewa tsarin yana "tsotse" ’yan Nijeriya. Masanin tattalin arzikin ya kuma shawarci majalisar dokokin ƙasar da ta mayar da hankali kan dokokin da za su ciyar da ’yan Nijeriya gaba fiye da ayyukan sa ido. Utomi, wanda kuma shi ne Mai Gudanar na Big Tanti, ya yi wannan kiran a taron manema labarai na ƙungiyar kan "yanayin ƙasa" a ranar Litinin a Legas. Band A yana nufin rukunin abokan cinikin…
Read More