ukarofi

12738 Posts
Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar ma’aikata ƙarƙashin shirin ‘Renewed Hope’ a Hukumar NDE

Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar ma’aikata ƙarƙashin shirin ‘Renewed Hope’ a Hukumar NDE

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da mataki na biyu na ɗaukar ma’aikata ƙarƙashin shirin Renewed Hope Employment Initiatiɓe (RHEI) ƙarƙashin Hukumar Kula da Ayyukan Yi (NDE), domin rage rashin aikin yi da kuma koyar da matasa dabarun samun sana’o’i da cigaba. Shugaban Hukumar NDE, Mista Silas Agara ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shafin rajista ta yanar gizo a birnin Abuja, inda ya ce tsarin zai kasance cikin gaskiya da adalci, kuma an tsara shi ne domin bai wa kowane ɗan ƙasa dama ba tare da nuna bambanci ba. “Mun kammala mataki na…
Read More
Yaƙi da ta’addanci: Gwamnatin Tinubu ta samar da sabbin jiragen yaƙi 60

Yaƙi da ta’addanci: Gwamnatin Tinubu ta samar da sabbin jiragen yaƙi 60

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sayo jiragen yaƙi 60 domin ƙara wa rundunonin tsaro ƙarfi wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a Nijeriya. Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a wajen taron Sir Ahmadu Bello Foundation da ya gudana a Arewa House a Kaduna. A cewarsa, wannan yunƙuri na daga cikin muhimman sauye-sauye da gwamnatin ke yi don tabbatar da zaman lafiya da kuma murƙushe ‘yan ta’adda a sassan ƙasar. “Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba mu cikakken goyon baya. Za mu yi…
Read More
Bayan shekaru 11, Gwamnatin Tarayya ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ‘yan matan Chibok, Leah Sharibu

Bayan shekaru 11, Gwamnatin Tarayya ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ‘yan matan Chibok, Leah Sharibu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirinta na ganin an sako sauran ‘yan matan makarantar Chibok da Leah Sharibu, tare da tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da 'yan matan duk da shekarun da aka kwashe. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa shekaru 11 bayan sace ɗalibai 276 da ƙungiyar Boko Haram ta yi a makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno, har yanzu ana kyautata zaton ‘yan mata 87 na hannunsu. Haka kuma, Leah Sharibu, wacce aka sace a watan Fabrairun…
Read More
‘Yan siyasa na yunƙurin durƙusar da Jihar Zamfara – Dr. Sani Abdullahi Shinkafi

‘Yan siyasa na yunƙurin durƙusar da Jihar Zamfara – Dr. Sani Abdullahi Shinkafi

’ Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa masu ra’ayin son kai na shirin durƙusar da Jihar Zamfara domin cimma muradun siyasar su, yana mai cewa ba za a amince da kafa dokar ta-ɓaci a Zamfara ba. Dr. Shinkafi a wata zantawa da manema labarai a daren ranar Alhamis a Gusau, ya ce kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya a bayyane yake, waɗanda idanuwan su suke a rufe sun Kasa fahimtar me ya ƙunsa. "Jihar Zamfara sam bata cancanci a ayyana dokar ta-ɓaci ba, kamar…
Read More
Ouattara Ya sake fitowa takara: ko tarihi zai maimaita kansa a Ivory Coast?

Ouattara Ya sake fitowa takara: ko tarihi zai maimaita kansa a Ivory Coast?

Shugaban ƙasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, mai shekaru 83, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba mai zuwa, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a ƙasar. Ouattara wanda ke kan mulki tun 2011, ya ce: “Ina da cikakken lafiyar da zan ci gaba da shugabanci, kuma tsarin mulkinmu ya ba ni dama.” Ya ce ƙalubalen tattalin arziki da tsaro na buƙatar gogaggen jagora kamar sa. Sai dai wannan matakin ya ƙara raba kan al'umma, duba da yadda shahararrun 'yan adawa kamar Laurent Gbagbo, Guillaume Soro da Charles Blé Goudé ke haramta…
Read More
Ghana ta tura sojoji bayan harin da ya kashe ɗalibai a iyakar Burkina Faso

Ghana ta tura sojoji bayan harin da ya kashe ɗalibai a iyakar Burkina Faso

Gwamnatin Ghana ta ɗauki matakin gaggawa na tura sojoji zuwa garin Bawku da ke kan iyakar ƙasar da Burkina Faso, bayan harin da ya yi sanadin mutuwar dalibai uku. Feliɗ Kwakye Ofosu, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya ce gwamnati ta canza matsayinta daga “tsare zaman lafiya” zuwa “tilasta zaman lafiya” saboda ƙara tsanantar rikicin. Garin Bawku na fama da rikicin sarauta da ke tsakanin ƙabilun Mamprusi da Kusasi, kuma ana fargabar rikicin zai buɗe ƙofa ga ‘yan jihadi daga yankin Sahel. Ghana ta ce, ana ci gaba da sintiri a makarantun yankin tare da kakaɓa wa yankin dokar…
Read More
Shugaban Jamus ya yi ta’aziyya ga iyalan Laura Dahlmeier

Shugaban Jamus ya yi ta’aziyya ga iyalan Laura Dahlmeier

Fitacciyar ‘yar wasan biathlon ta ƙasar Jamus kuma zakarar zinare a Olympics, Laura Dahlmeier, ta rasu bayan faɗuwa daga wani dutse a arewacin Pakistan yayin da take hawa Laila Peak da ke tsaunin Karakoram, inji mai magana da yawun gwamnatin Gilgit-Baltistan, Faizullah Faraƙ, ranar Laraba. An bayyana cewa, ƙoƙarin ceto Dahlmeier ya ci tura saboda tsananin hadari da ya hana masu ceto isa wurin. Abokin tserenta, Marina Eva, ta tsira daga haɗarin bayan ta turo da siginar neman agaji a ranar Litinin, wanda hakan ya tayar da tawagar ceto. A ƙarshe dai an tabbatar da mutuwar Laura ranar Laraba, amma…
Read More
Za mu goyi bayan kafa ƙasar Falasdinu a Satumba, idan Isra’ila ba ta dakatar da yaƙi ba – Britaniya

Za mu goyi bayan kafa ƙasar Falasdinu a Satumba, idan Isra’ila ba ta dakatar da yaƙi ba – Britaniya

Rikicin Gaza na ƙara tsananta, yayin da ƙasashen duniya ke sake ɗaukar matsayi mai ƙarfi a kan buƙatar ƙirƙirar ƙasar Falasdinu. Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa, ƙasarsa za ta amince da kafa Falasdinu a watan Satumba matuƙar Isra’ila ba ta ɗauki matakin kawo sauƙi ga halin da Gaza ke ciki ba. Wannan sanarwa ta janyo martani mai zafi daga gwamnatin Isra’ila, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ya zargi Birtaniya da “sakar wa ‘yan ta’adda mara da ƙarfafa Hamas.” Alhalin haka, hukumar kula da yunwa ta duniya ta yi gargaɗi cewa yunwar da ke ci gaba da ƙamari a Gaza…
Read More
Abubuwa 34 da aka tanada na harajin VAT a sabuwar dokar haraji

Abubuwa 34 da aka tanada na harajin VAT a sabuwar dokar haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A watan Yunin 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurorin gyaran haraji guda huɗu. Waɗannan dokokin sun haɗa da Dokar Haraji ta Nijeriya (NTA), Dokar Gudana da Haraji ta Nijeriya (NTAA), Dokar Kafa Hukumar Haraji Kuɗi ta Nijeriya (NRSA), Dokar Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji (JRBA). A cewar fadar shugaban ƙasa, sababbin dokokin za su daidaita tsarin gudanar da haraji, haɓaka samar da kuɗaɗen shiga, inganta yanayin kasuwanci, da kuma jawo hankalin masu saka hannun jari na cikin gida da na waje. Dokar ta yi wa tsarin harajin Nijeriya garambawul domin bunƙasa tattalin…
Read More
Arewa ku farka, ku tashi ku tabbatar da muradun yankinku – Abdulaziz Bako

Arewa ku farka, ku tashi ku tabbatar da muradun yankinku – Abdulaziz Bako

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da Majalisar Dokokin Nijeriya ke ci gaba da nazarin sauye-sauye fiye da 80 cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, yankin Arewa na ci gaba da zama cikin shiru da rashin damuwa. Sauye-sauyen da ka iya gurgunta tattalin arziki, zamantakewa da siyasar yankin, saidai abin takaici suna ƙoƙarin wucewa cikin shiru. A cewar wani mai rajin kare muradun Arewa, Abdulaziz Bako, mafi yawan sauye-sauyen na da illa kai tsaye ga Arewa. “Wannan ba magana ce ta jam’iyya ko ƙabila ba, magana ce ta makomar yanki gaba ɗaya,” inji shi. Daga cikin batutuwan da ya fi tsorata da…
Read More