02
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Nijeriya na shirin fara amfani da fasahohi irin – ƙirƙirarriyar basira ta AI, geospatial analytics, da bayanan tauraron ɗan adam domin magance ƙarancin abinci a ƙasar da kuma sa ido kan yadda ake noman abinci, haɗa manoma da kasuwa, da kuma rage asarar bayan girbi. Shettima ya bayyana haka ne a wajen buɗe taron hada-hadar hannayen jari na tsarin samar da abinci ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNFSS+4), a Addis Ababa, ranar Litinin. Taron na da nufin samar da makoma mai ɗorewa wadda ke ginuwa kan yalwa, daidaito da mutuncin…
