ukarofi

12738 Posts
Mun tafka asarar biliyan N92 na kuɗaɗen waje a 2024, inji BUA

Mun tafka asarar biliyan N92 na kuɗaɗen waje a 2024, inji BUA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kamfanin Siminti na BUA, Abdul Samad Rabiu a ranar Litinin ya bayyana cewa kamfanin ya yi asarar kuɗaɗen waje na Naira Biliyan 92 a shekarar 2024. Shugaban kamfanin simintin na BUA, wanda ya bayyana haka a taron shekara-shekara na kamfanin a Abuja, ya bayyana cewa an afka asarar ne sakamakon faɗuwar darajar Naira. Rabiu, ya ce an samu sauƙin lamarin sosai a bana. A cewar BUA, a cikin 2023, kamfanin ya yi asarar kuɗaɗen waje na Naira Biliyan 63. AbdulSamad Rabiu ya danganta hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arzikin duniya, sai dai ya nuna…
Read More
Za a rasa ayyuka idan Dangote ya fara raba fetur kai-tsaye – NOGASA

Za a rasa ayyuka idan Dangote ya fara raba fetur kai-tsaye – NOGASA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Dillalan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NOGASA) ta nuna rashin amincewa da shirin da matatar Dangote ta yi a baya-bayan nan na samar da man fetur kai-tsaye ga masu amfani da shi, tare da kaucewa tsarin da aka saba da shi. Shugaban NOGASA, Benneth Korie, ya bayyana damuwarsa cewa wannan matakin na iya kawo cikas ga masana'antar mai da iskar gas, tare da jefa dubunnan ayyuka al'umma cikin haɗari da kuma kawo cikas ga tsarin kasuwanci na masu samar da kayayyaki a duk faɗin ƙasar. Idan za a iya tunawa, matatar man Dangote…
Read More
Yan bindiga sun yi wa mutum 35 yankan rago a Zamfara

Yan bindiga sun yi wa mutum 35 yankan rago a Zamfara

' Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Aƙalla mutane 35 da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda dake Jihar Zamfara 'yan ya'adda suka halaka bayan sun karɓi sama da Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa. Wani mazaunin yankin a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja mai suna Lawali Muhammad Banga, ya bayyana cewa ‘yan ta'addan sun yi garkuwa da mutane 53 a ƙauyen su watannin baya inda suka buƙaci Naira miliyan ɗaya ga kowane mutum a matsayin kuɗin fansa domin su sako mutanen nasu. A cewarsa, mutane 18 ne kawai…
Read More
Gwamnatin Gombe ta nemi taimakon masarautar Gombe wajen aiwatar da dokar hana cin zarafi

Gwamnatin Gombe ta nemi taimakon masarautar Gombe wajen aiwatar da dokar hana cin zarafi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe A yunƙurin da gwamnatin Jihar Gombe ke yi na magance cin zarafin mata da yara, ma’aikatar harkokin mata ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi (GBV) ga mai martaba sarkin Gombe, Alhaji Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun cikakken goyon bayan sarakunan gargajiya wajen tabbatar da aiwatar da dokar a ƙasa. Taron da aka gudanar a zauren ƙaramar hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don ganin an kawar da duk wata ɗabi'a…
Read More
Manoma sun koka kan tsadar taki a Nijeriya

Manoma sun koka kan tsadar taki a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni daga jihohin da ke samar da yawancin kayan amfanin gona sun tabbatar da cewa manoma na barin shukan masara da shinkafa saboda tsadar takin zamani. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke cewa ta raba takin zamani kyauta ga manoma. Manema labarai sun tattauna da manoma da sauran masu ruwa da tsaki domin jin halin da suka shiga kan tsadar taki a bana. Wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa, yanzu haka ba za su iya sayen buhun taki ba saboda hauhawar farashin sa wanda ya kai sama da N50,000 a…
Read More
NAPTIP ta gargaɗi iyaye kan barin ’ya’ya sakaka

NAPTIP ta gargaɗi iyaye kan barin ’ya’ya sakaka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugabar Hukumar Yaƙi da Fataucin Bil Adama ta ƙasa (NAPTIP), Binta Adamu Bello, ta gargaɗi iyaye da su guji barin yara a hannun mutanen banza, makwabta marasa amana, inda ta ce irin waɗannan na iya sanya yara cikin mawuyacin hali na fataucin mutane da sata. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta haɗa wata yarinya ’yar shekara biyar da aka yi safararta mai suna Rahama Ibrahim da iyayenta a Damaturu, jihar Yobe, ranar Juma’a. Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, ɓincent Adekoye, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugabar ta samu wakilcin Saleh Zakar,…
Read More
Sama da mutum miliyan 3.7 ke fuskantar yunwa a Arewa maso Gabashin Nijeriya – ICRC

Sama da mutum miliyan 3.7 ke fuskantar yunwa a Arewa maso Gabashin Nijeriya – ICRC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Ba Da Agaji ta ƙasa da ƙasa ta Red Cross ta koka kan ƙaruwar yunwa a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda sama da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar ƙarancin abinci a halin yanzu. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce, yawancin waɗanda abin ya shafa manoma ne da a da su ke ciyar da al’ummarsu amma a yanzu su na fafutukar rayuwa. Rikicin da aka kwashe shekaru ana yi ya raba iyalai da muhallansu, da rashin samun filayen noma, da kuma kawo cikas ga samar da abinci a…
Read More
Dalilan da suka sanya za mu yi Tinubu a 2027 – Sarkin Daura 

Dalilan da suka sanya za mu yi Tinubu a 2027 – Sarkin Daura 

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Sarkin Daura a Jihar Katsina, Umar Faruƙ-Umar, ya ce zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya ya yi tazarce a 2027 saboda girmamawar da shugaban ya yi wa masarautar Daura da kuma Jihar Katsina ta hanyar yi wa wanda ya gada, tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, jana'izar ban-girma. Sarkin ya bayyana goyon bayansa ne a fadarsa da ke Daura a ranar Asabar yayin da ya tarbi tawagar matan gwamnonin Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Uwargidar Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu. A yayin ziyarar ta Remi Tinubu a fadar da, Sarkin, wanda ya gode wa shugaban kasa bisa girmamawar…
Read More
Za mu ƙaurace wa zaɓen 2027 idan ba a saki Kanu ba – Gargaɗin matasan Ibo ga Tinubu

Za mu ƙaurace wa zaɓen 2027 idan ba a saki Kanu ba – Gargaɗin matasan Ibo ga Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Matasan ‘Yan ƙabilar Ibo, wata ƙungiyar masu matsa lamba, ta yi gargaɗin cewa matasan Igbo za su ƙaurace wa zaɓen 2027 matuƙar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙi sako jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Chinedu Obilor, ya ce ƙungiyar ta janye zanga-zangar da ta shirya yi kan wannan batu bayan tattaunawar da suka yi da mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu. Ya ce Kalu ya tabbatar wa taron cewa ana ci gaba da tattaunawa da shugaban ƙasa kan sakin shugaban ƙungiyar ta IPOB. "Mun yi imanin shugaban ƙasa zai…
Read More
2027: Gwamnan Osun na PDP ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu

2027: Gwamnan Osun na PDP ya ayyana goyon bayansa ga Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu don zaɓen 2027. A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya bayyana goyon bayan su ga Shugaba Tinubu domin sake tsayawa takara a 2027, yana bayyana shi a matsayin ɗan jihar da ya cancanta. Sanarwar ta ce: “Jiya na gana da jagororin jam'iyyar PDP a Osogbo bayan makonni na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a faɗin Jihar Osun daga sarakunan gargajiya da ma’aikatan gwamnati zuwa shugabannin kasuwa da ’yan jam’iyya a matakin ƙasa. “Ina farin cikin sanar da matsayar…
Read More