ukarofi

12738 Posts
2027: Babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Tinubu – Gwamnan Ebonyi 

2027: Babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Tinubu – Gwamnan Ebonyi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana cewa babu wata gamayyar siyasa da za ta iya kada Bola Tinubu a zaɓen 2027. Ya buƙaci 'yan adawa da masu neman takara su haƙura da buri, su kuma goyon bayan gwamnatin da ke ci yanzu. Da ya ke jawabi a taron shugabannin jam’iyyar APC na Kudu maso Gabas da aka gudanar a Abakaliki, Gwamna Nwifuru ya ce fitowar Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a 2023 nufin Allah ne ba nufin dan Adam ba, kuma ya jaddada cewa babu wani kawance ko haɗakar ‘yan adawa da za…
Read More
Aishatu Binani ta fice daga APC zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC

Aishatu Binani ta fice daga APC zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu ɗahiru Binani, ta yanki katin jam'iyyar haɗaka ta African Democratic Congress (ADC). Blueprint Manhaja ta rawaito cewa an ga tsohuwar 'yar majalisar dattawan da ta wakilci mazaɓar Adamawa ta Tsakiya cikin wani bidiyo tana jawabin nuna goyon baya ga ADC, yayin da take zagaye da matasa. "Mu mun ɗauki jam'iyyar ADC kuma za mu yi tafiya a cikinta," inji ta. "Muna roƙon Allah ya taimake mu ya raba mu da mutanen da muke tafiya da su amma suna gurɓata jam'iyya." Bayan kammala jawabin ne kuma…
Read More
Fifita ilimin boko a kan na addini

Fifita ilimin boko a kan na addini

Duniya ina zaki damu? A haƙiƙanin gaskiya wannan rayuwa mun kai wani mataki da iyaye da kansu ke nuna wa ’ya’yansu duniya ta fi lahira. Wannan kuma ba ƙaramin ƙalubale ba ne gare mu Musulmi. Sakamakon hakan, ya sa yara za su taso da sangarta, rashin tarbiyya, ga rashin kula da addinin Allah. A haka kuma za ku ga ko sallah ma ba ta dame su ba, kuma ba su ɗauki iyayensu a bakin komai ba. Me ya jawo hakan? A wani ɓangaren kuma ku dubi amfanin ilimantar da 'ya mace. A wannan yanayin da muke ciki kashi casa’in 90%…
Read More
Har yanzu ta’addanci na ƙara zama barazana a Nijeriya

Har yanzu ta’addanci na ƙara zama barazana a Nijeriya

Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kawo ƙarshen ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijeriya a ranar 3 ga Mayu, 2022 tare da ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso ɓilla. Ya ziyarci waɗanda ta’addanci ya shafa kamar, sansanoni ’yan gudun hijira a Jihar Borno, waɗanda rikicin ta’addancin Boko Haram ya kora daga muhallan su. Guterres ya bayyana fatansa na cewa, Nijeriya na daf da samun nasara a yaƙin Boko Haram. Ya yabawa gwamnatin Buhari bisa dabarunta da suka ƙarfafawa mayaƙan Boka Haram aƙalla 37,000 kwarin gwiwar miƙa wuya tare da kai su wuraren halin gyaran hali.…
Read More
Yawan mace-macen aure: Rashin haƙuri ko rashin tarbiya?

Yawan mace-macen aure: Rashin haƙuri ko rashin tarbiya?

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a ƙasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na ƙarewa da saki. Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al'umma? Me ya kamata a yi don a rage matsalar? An yi kira ga gwamnati ta sanya darasin ilimin aure a cikin manhajar karatun sakandare da nufin rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma. Mace-macen aure matsala ne da ya yawaita a ƙasar Hausa.…
Read More
‘Yan fim za su ci gaba da cin moriyar Gwamna Abba Kabir Yusuf – Jaruma Aina’u Ade

‘Yan fim za su ci gaba da cin moriyar Gwamna Abba Kabir Yusuf – Jaruma Aina’u Ade

Daga MUKHTAR YAKUBU A kwanakin baya ne mai bai wa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf shawara Hajiya Aina'u Ade ta gudanar da taron bayar da tallafi ga mabuƙata musamman dattawan cikin Kannywood, in da a wajen taron aka ga ta bayar da wani ƙunshin kuɗi ga mahalarta taron, baya ga haka kuma aka bi waɗansu har gida wato marassa lafiya aka kai musu, wasu kuma suka je ofishinta suka karbi nasu. Ganin yadda rabon kuɗin ya kasance ne wakilinmu ya ji ta bakin Aina'u Ade dangane da wannan rabon kuɗin da ta yi. Don haka sai ku biyo mu…
Read More
San’insa tsakanin Naziru da Rarara: Rashin alƙiba ne ke kawo irin wannan cece-kucen – Malam Khalid Musa

San’insa tsakanin Naziru da Rarara: Rashin alƙiba ne ke kawo irin wannan cece-kucen – Malam Khalid Musa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  A abinda ya bayyana na rikici da san'insa da ke wakana tsakanin Naziru M. Ahmad da aka fi sani da Naziru Sarkin Waƙa da Adamu Dauda Kahutu Rarara, abin ya yi ƙamari ne a shekarar 2023 inda a wata hira da tashar DCL ta yi da Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana cewa, an bashi miliyan 150 da motar mliyan 80 don ya bar tafiyar Atiku Abubakar, inda Rarara ya fito ya ƙaryata Naziru a kan wannan furuci inda ya nuna cewa wannan ba abu ne mai yiwuwa ba sam. Wanda daga bisani Naziru ya fusata…
Read More
Ƙalubalen kafa ’yan sandan jihohi ga magance rikice-rikice

Ƙalubalen kafa ’yan sandan jihohi ga magance rikice-rikice

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU An fara muhawarar samar da ’yan sandan jihohi a ƙasar nan, kimanin shekaru 20 ko fiye da haka, sakamakon ƙalubalen tsaro da aka riƙa fuskanta a wasu jihohi, musamman a Jihar Filato. Tun da aka fara samun rikicin addini da ƙabilanci a Jihar Filato a shekarar 2001, batun samar da ’yan sandan jihohi ya fara bayyana. Saboda barazanar da gwamnoni a lokacin suka fara samu ta rashin samun ƙarfin iko kan ’yan sanda da jami'an soja, game da yadda za a bi tsarin da suke so wajen kama masu laifi ko waɗanda ake zargi da haddasa…
Read More
MEDCI ta yabi Gwamnatin Yobe kan gina hanyoyin karkara

MEDCI ta yabi Gwamnatin Yobe kan gina hanyoyin karkara

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu Shugaban ƙungiyar Media and Disability Care Initiative (MEDCI), mai zaman kanta, Rajab Mohammed Isma’il, ya yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Yobe bisa ayyukan gina hanyoyin raya karkara da birane a faɗin jihar. Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, a garin Potiskum, yayin da yake jagorantar tawagar ’yan jarida don ziyarar gani da ido dangane da ayyukan hanyoyin da gwamnatin jihar ta kammala da waɗanda ke gudana a jihar. Ayyukan hanyoyin sun haɗa da hanyar Potiskum zuwa Ngojin mai nisan kilomita 2.5, hanyar Fadawa zuwa Daya mai nisan kilomita 5, a ƙarƙashin kulawar ma’aikatar…
Read More
Dikko Raɗɗa ya taya Barista Murtala Aliyu murnar samun muƙamin lauyan APC na ƙasa

Dikko Raɗɗa ya taya Barista Murtala Aliyu murnar samun muƙamin lauyan APC na ƙasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan na ƙunshe ne a wata takardar sanar da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Muhammad kaula ya sanya wa hannu ya kuma aike wa manema labarai. Gwamnan ya bayyana wannan nasarar a matsayin abin alfahari da kuma shaida ta yadda jam’iyyar ke girmama ƙwarewa, gaskiya da ingantaccen shugabanci a fannin shari’a. A cewarsa, wannan naɗin ya zo a kan gaɓa, musamman a daidai lokacin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da gina dimokuraɗiyya mai inganci a cikin gida. Ya ce Barista Kankia mutum ne da ya shafe shekaru a fagen hidimar jama’a…
Read More