ukarofi

12738 Posts
Shugabancin Kantin Kwari na tare da gwagwarmayar shugaban ‘yan tebura Aminu Dan Falke 

Shugabancin Kantin Kwari na tare da gwagwarmayar shugaban ‘yan tebura Aminu Dan Falke 

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An bayyana cewa shugabanci na riƙo na ƙunigyar kasuwar Kantin Kwari Kano na tare da shugaban ƙungiyar 'yan tebura wanda gwamnatin baya ta karɓe musu wurare ba ta mayar musu ba, kuma yanzu wannan gwamnati ta Alhaji Abba Kabir Yusuf mai sauraron ƙorafi da taimaka musu domin taimakawa al'umma wannan abu da suke yi abu ne na ljmana ba na tashin hankali ba kuma neman haƙƙi ta hanyar lumana da bin doka abu ne mai kyau, don haka shugabanci ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari na riƙo na tare da wannan yunƙuri wanda munsan gwamna mai jin…
Read More
Muna jin daɗin yadda ɗalibai ke kiran makarantar Tropical gidan gyaran hali – Daneji

Muna jin daɗin yadda ɗalibai ke kiran makarantar Tropical gidan gyaran hali – Daneji

Daga MUHAMMADU MUJITABA KANO Malam Idris Daneji Babban Daraktan Makarantar Tropical College Of Health Science And Technology ya bayyana cewa dalilin tsayawar mu tsayin daka na ganin sai mun koyar da ilimin kula da lafiya da kuma cikakkiyar tarbiyya a makarantar koyon kula da kiwon lafiya ta Kwalejin Tropical da ke Kano ya sa har ɗalibai ke kiran makarantar da gidan gyaran hali, inda wannan yana faranta mana rai kuma yana bamu ƙwarin gwiwa na cewa ɗalibin da ba zai yadda ya samu kyakkyawar tarbiyya to ba shakka da kan shi zai kori kansa mu huta da shi ya huta…
Read More
Fadar Shugaban ƙasa ta caccaki ADC kan sukar sigar jana’izar Buhari

Fadar Shugaban ƙasa ta caccaki ADC kan sukar sigar jana’izar Buhari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban Nijeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama'a. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna. ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi al’umma kan yaɗuwar wasu manyan cututtuka

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi al’umma kan yaɗuwar wasu manyan cututtuka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), Dokta Jide Idris, ya yi gargaɗin cewa an gano ɓullar cututtuka kamar zazzaɓin dengue, shawara, kwalara, mashaƙo da kuma Mpox zai haifar da mummunar illa ga al’ummar Nijeriya fiye da yadda aka saba gani a baya. Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a shirin The Morning Brief a ranar Litinin, Dokta Idris ya bayyana damuwar cewa yawancin masu fama da zazzaɓin Dengue ana kuskuren sa da zazzaɓin cizon sauro, wanda ke haifar da tsaiko wajen magance cutar da kuma rashin ɗaukar matakan da suka…
Read More
APC na daf da samun kashi biyu bisa uku a Majalisar Dattawa

APC na daf da samun kashi biyu bisa uku a Majalisar Dattawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Adadin sanatocin jam’iyyar APC mai mulki ya kusan haura 73 wanda shi ne kashi 2 cikin 3 na dukka sanatoci 109 da ake da su a Majalisar Dattawa. Jam’iyyar wadda ta samu zaɓaɓɓun sanatoci 50 a farkon zaman majalisar dattawa ta 10 a watan Yunin 2023, ta haura zuwa 68 a yanzu, saboda ficewar sanatoci daga PDP, Labour Party da NNPP zuwa jam’iyyarta, na baya-bayan nan daga cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da Sanata Olubiyi Fadami Fayose da kuma Sanata Olubiyi Fagge. Sanatocin da suka sauya sheƙar zuwa APC daga PDP sun haɗa da…
Read More
Gwamnatocin Tarayya, jihohi da ƙananan hokumomi sun raba kuɗaɗen shiga na tiriliyan N1.818 a Yunin 2025

Gwamnatocin Tarayya, jihohi da ƙananan hokumomi sun raba kuɗaɗen shiga na tiriliyan N1.818 a Yunin 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomi sun raba jimillar Naira Tiriliyan 1.818, na kuɗaɗen shiga daga asusun tarayya a watan Yunin 2025. Sanarwa da Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya fitar ranar Asabar a Abuja, bayan taron kwamitin ya bayyana cewa, kuɗaɗen shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.818 sun haɗa da kuɗaɗen shiga da aka ƙayyade na doka na Naira Tiriliyan 1.018, kuɗaɗen shiga na haraji ɓAT na biliyan N631.507. A cewar FAAC, jimillar kuɗaɗen shiga na Naira Tiriliyan 4.232 ya kasance a cikin watan Yunin 2025. Jimillar kuɗaɗen da aka cire na…
Read More
Hukumar KASSAROTA a Katsina ta buɗe sashen sauraren ƙorafe-ƙorafen al’umma

Hukumar KASSAROTA a Katsina ta buɗe sashen sauraren ƙorafe-ƙorafen al’umma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar kiyaye haɗurra ta Jihar Katsina (KASSAROTA)ta ƙirƙiro sashen kula da ƙorafe-ƙorafen al'umma. Sashen wanda yake ƙarƙashin ofishin jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, zai yi aiki don karɓar ƙorafe-ƙorafen al'umma da suka shafi yadda jami'an hukumar suke gudanar da ayyukansu. Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Abubakar Marwana ya sanar da haka a wata takarda ɗauke da sa hannun sa wanda aka rabawa manema labarai a Katsina. Ya bayyana cewa ƙorafe ƙorafe akan matsalolin cin hanci da rashawa, amfani da ƙarfi ko matakan da basu dace ba na tursasawa al'umma, ko rashin bin ƙa'idojin…
Read More
Shugaban ƙasar Gambiya Adama Barow ya kawo ziyarar ta’aziyar Buhari Katsina

Shugaban ƙasar Gambiya Adama Barow ya kawo ziyarar ta’aziyar Buhari Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙasar Gambiya Adama Barrow tare da Uwargidansa sun kawo ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Muhammadu Buhari a gidansa dake garin Daura Barow ya bayyana rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi bama a ƙasashen Afrika ba harma da duniya baki ɗaya. "Duniya tayi rashin shugaba adali mai son zaman lafiya da daidai a tsakanin ƙasashen Afrika da sauran manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziki,"inji Adama Barow. Ya ce ƙasar Najeriya da ƙasashen Afirka zasu rinka tunawa da marigayi Muhammadu Buhari bisa aƙidar ta tabbatar da gaskiya da riƙon amana…
Read More
Hukumar NIS ta ƙwace fasfon Sanata Natasha a filin jirage na Abuja

Hukumar NIS ta ƙwace fasfon Sanata Natasha a filin jirage na Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) da ke filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Jami'an na hukumar shige da ficen sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne da safiyar ranar Alhamis. Lamarin ya afku ne lokacin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta ke ƙoƙarin shiga jirgin British Airways zuwa birnin Landan. Ganau a filin jirgin sun bayyana cewa Sanatar ta iso tashar jirgin na ƙasa da ƙasa ne tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan, amma sai jami’an shige da fice suka dakatar da…
Read More
EndSAS: Kotu ta umarci ’yan sanda su biya diyyar miliyan N10

EndSAS: Kotu ta umarci ’yan sanda su biya diyyar miliyan N10

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta umurci Sufeto-Janar na ‘Yan sanda da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas da su biya diyyar Naira Miliyan 10 ga wasu gungun masu zanga-zangar #EndSARS bisa take haƙƙinsu. Mai shari'a Musa Kakaki, wanda ya yanke hukuncin, ya gano cewa an ci zalin masu zanga-zangar EndSARS karo na huɗu da aka gudanar a ranar 20 ga Oktoba, 2024, domin nuna adawa da zalunci da harbe-harben da aka yi a ƙofar shiga Lekki a shekarar 2020. A cikin hukuncin da ya yanke, alƙalin ya jaddada cewa, yayin da jami'an tsaro ke da…
Read More