ukarofi

11670 Posts
Milo ya tallafa wa masu sana’ar shayi 2,000 a Kano da Jos

Milo ya tallafa wa masu sana’ar shayi 2,000 a Kano da Jos

Daga RABI'U SANUSI a Kano Kamfanin Nestlé Milo ya tallafa wa masu sana’ar sayar da shayi 2,000 a Kano da Jos ƙarƙashin shirinsa na tallafa wa kwastomomin da suka jima suna hulɗa da shi domin ƙarfafa gwiwar masu ƙananan sana’o’i. Kamfanin ya ce rabon tallafin zai kuma ƙarfafa rawar da Milo ta shafe tsawon shekaru tana takawa a matsayin mahadin shan shayi a Arewacin Najeriya. Shirin ya bai wa masu shayi kayan tallafin da suka haɗa da risho mai amfani da iskar gas, tukunyar gas, malafar kare rana, fitila mai amfani da hasken rana, kofuna da kuma sinadarin Milo. Masu…
Read More
Ƙungiyar wakilan ‘yan jaridu ta ƙaddamar da sabon ofishin ta bayan yi masa kwaskwarima a Kano

Ƙungiyar wakilan ‘yan jaridu ta ƙaddamar da sabon ofishin ta bayan yi masa kwaskwarima a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar wakilan gidajen jaridu ta Jihar Kano, wato Correspondents’ Chapel, ta ƙaddamar da sabon ofishinta da aka yi wa cikakken gyara, a wani mataki na inganta yanayin aikin ’yan jarida da ƙara ƙarfafa haɗin kan mambobinta. An gudanar da bikin ƙaddamar da ofishin ne a Sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Kano, ranar Lahadi, inda tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano kuma tsohon Shugaban NUJ na ƙasa, Muhammad Garba, ya jagoranci taron. Manyan baƙin da suka halarci taron sun yaba wa Shugaban Correspondents’ Chapel na Kano, Murtala Adewale, da kwamitin gudanarwarsa,…
Read More
Yari ginshiƙi ne wajen samun nasarar Tinubu – Sani Shinkafi

Yari ginshiƙi ne wajen samun nasarar Tinubu – Sani Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau Fitaccen jigon APC kuma jagoran siyasa, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce Sanata Abdulaziz Yari yana da darajar tsarin da ake buƙata don sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. Shinkafi ya yi gargaɗin cewa nasara a Arewa maso Yamma ta dogara ne da ɗaukar mataki mai tsauri kan 'yan ta'adda da kuma inganta samar da walwala ga 'yan ƙasa. Shinkafi ya yi wannan furucin ne a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da membobin ƙungiyar siyasarsa, "Wamban Shinkafi Democratic Front", wanda aka gudanar a gidansa da ke Gusau, Jihar Zamfara. Shinkafi…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da kayan tallafi ga al’ummar da hare haren ‘yan bindiga ya shafa

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da kayan tallafi ga al’ummar da hare haren ‘yan bindiga ya shafa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon tallafin abinci, kuɗaɗe da sauran kayan agaji ga al’ummar ƙaramar hukumar Musawa da hare-haren 'yan bindiga ya shafa. Tallafin ya samu ne da haɗin gwiwar da ɗan majalissar tarayya mai wakiltar yankin Hon. Abdullahi Aliyu (Dujiman Katsina), sun haɗa kai domin tallafa wa al’ummar yankin tare da rage musu raɗaɗin halin da suke ciki. An raba buhunan shinkafa 1,500 da buhunan taki 200, yayin da Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad (Dujiman Katsina), Ɗan Majalissar Tarayya mai wakiltar yankin, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 30…
Read More
Al’ummar Dayi a Katsina sun yi taron inganta siyasa a garinsu

Al’ummar Dayi a Katsina sun yi taron inganta siyasa a garinsu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar cigaban Dayi mazauna Katsina sun yi taron masu ruwa da tsaki don bada gudunmuwa ta ingata rayuwar al'ummarsu ta Dayi da ke karamar hukumar Malumfashi. A jawabin sa , shugaban ƙungiyar, mataimakin shugaban mai hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa mai ritaya Hamza Umar Dayi ya shaidawa mahalarta taron cewa an haɗu don a ingata siyasa ta mutanen garin Dayi. Alhaji Hamza Umar Dayi ya tuno cewa babu wani lokacin da aka samu ɗan siyasa da ya taba wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi a majalisar jiha. Yace yanzu jam'iyyar APC ta tsaida ɗan…
Read More
Shugaban NASETFUND a Nasarawa ya samu digiri na uku kan jagoranci da harkokin ilimi

Shugaban NASETFUND a Nasarawa ya samu digiri na uku kan jagoranci da harkokin ilimi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban asusun kula da Ilimi na gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira NASETFund a turance Abubakar Adamu Idris ya samu digiri na uku a fannin jagoranci da ilimin harkokin ilimi daga jami’ar Atlantic International University. Wannan ya zo ne bayan ya samu nasarar kare rubutunsa na digiri ɗin ƙarƙashin kulawar manyan malamai da aka san su a faɗin duniya. A cikin wani bidiyo da aka fitar kwanan nan shugaban NASETFund din Abubakar Adamu Idris ya bayyana nasarar a matsayin sakamakon hakuri ta cikin ƙalubalen rayuwa da na karatu da kuma tsarin karatun digiri na…
Read More
Ƙungiyar haɗin kan Agatu don Wadada za ta ƙaddamar da ƙungiyar yaƙin neman zaɓe a Nasarawa

Ƙungiyar haɗin kan Agatu don Wadada za ta ƙaddamar da ƙungiyar yaƙin neman zaɓe a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar haɗin kan al'ummar ƙabilar Agatu ta jihar Nasarawa don Wadada wato Agatu United For Wadada a turance ta kammala shirye-shiryen ƙaddamar da wata ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ta domin goyon bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress APC a babban zaɓen 2027 wato sanata Ahmed Aliyu Wadada. Kodinetan ƙungiyar a jihar kwamaret Godspower Ede ne ya bayyana haka a cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin mu a Lafiya ranar Litinin na makon da ake ciki. Ede yace taron ƙaddamarwar da aka tsara za a yi a ƙarshen…
Read More
Kallamu ya buƙaci haɗin kan APC gabanin zaɓen cike gurbi a Gombe

Kallamu ya buƙaci haɗin kan APC gabanin zaɓen cike gurbi a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, Injiniya Dakta Usman Maijama’a Kallamu, ya yi kira ga sauran ’yan takarar da suka fafata da shi, shugabannin jam’iyya da magoya baya da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen da za a gudanar ranar 19 ga Satumba, 2026. Kallamu ya yi wannan kira ne bayan ya samu tikitin jam’iyyar a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Malam Sidi, hedkwatar ƙaramar hukumar Kwami ta Jihar Gombe. A zaɓen fidda gwannin, Kallamu ya samu ƙuri’u 27, inda…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane biyar a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane biyar a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga sun kashe mutane biyar a ƙaramar hukumar Dutsinma ta Jihar Katsina. A hira da wata kafar sadarwa na JBC ta yi da mazaunin garin Dutsinma, 'yan bindigan sun shiga garin Karofi inda suka kashe wani matashi mai suna zaharaddeen,suka jikkata wasu tare da kwashe Dabbobi. Haka kuma sun shiga ƙauyen Dage Lawal nan ma suka kashe mutane uku ciki har da wani tsohon Kansila da ɗan sa. Mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunnan sa, ya bayana cewa mutanen garurruwan sun nemi ɗauki daga jami'an tsaro na karamar hukumar amma saboda rashin…
Read More
Funmilayo Ransome-Kuti: Matar da ta buɗe wa mata ƙofar da ba a so su shiga ba

Funmilayo Ransome-Kuti: Matar da ta buɗe wa mata ƙofar da ba a so su shiga ba

Macen Afirka ba ta jiran sai an ba ta — Funmilayo Ransome-Kuti Daga AISHA ASAS Akwai wasu mata da tarihinsu yake sa ka tsaya ka tambayi kanka irin duniyar da suka rayu a cikinta. Domin abubuwan da suka yi a yau za su iya zama kamar abubuwan da kowa zai iya yi, amma idan aka mayar da kai shekaru ɗari baya, sai ka fahimci cewa abin da suka yi ba ƙaramin ƙalubale ba ne. A lokacin da mace ke da ƙarancin damar yin karatu, balle ta shiga harkokin siyasa ko ta tsaya a gaban dubban mutane tana neman a saurare…
Read More