ukarofi

11670 Posts
Shugaban ‘yan wasan gargajiya na Kebbi ya rasu

Shugaban ‘yan wasan gargajiya na Kebbi ya rasu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Da safiyar ranar Lahadin nan gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da rasuwar Alhaji Garba Muhammed Kola da aka fi sani da Kanga. Alhaji Garba Muhammed Kola ya rasu a garin Birnin Kebbi bayan ya yi fama da rashin lafiya.Kafin rasuwar da shi ne shugaban sashen tsare-tsaren wasannin al'adun gargajiya a ma'aikatar yaɗa labarai ta jihar Kebbi. Ya rasu ya bar mata uku da yaya da dama.An kuma yi jana'izar sa a garin Birnin Kebbi kamar yadda shari'ar musulunci ta tanada. Kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi da babban Sakatare Alhaji Alkasim Salihu Gunabi…
Read More
Matasan malaman Zamfara sun yi addu’o’i ga Tinubu da Yari a matsayin shugaban kamfen na 2027

Matasan malaman Zamfara sun yi addu’o’i ga Tinubu da Yari a matsayin shugaban kamfen na 2027

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Reshen Jihar Zamfara na ƙungiyar malamai matasa don wa'azi da faɗakarwa, (Zamfara United of Youth Scholars for Preaching and Guidance) yau Lahadi sun gudanar da zaman addu'o'i na musamman don samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nasarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a matsayin darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027. An gudanar da zaman addu'o'in, a zauren taro na Maryam Multi-Purpose Hall da ke Gusau, babban birnin jihar. Taron ya samu halartar malamai da ɗalibai daga faɗin jihar. Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ƙungiyar, Malam Naziru Ibrahim…
Read More
Magidanci ya zuba wa matarsa fetur ya banka mata wuta saboda riga

Magidanci ya zuba wa matarsa fetur ya banka mata wuta saboda riga

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kogi ta kama wani mutum mai shekaru 33, Jacob Irewa, bisa zargin banka wa matarsa wuta a lokacin da suka samu saɓani a gidansu. Lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 14 ga Agusta, a Oworo Estate da ke Felele, Lokoja, babban birnin jihar Kogi, kamar yadda Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Afusat Saliu, ta bayyana. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Lokoja, Saliu ta ce matar, mai suna Berida Irawo, ta samu raunuka kuma ana duba lafiyarta a Asibitin Honey Gold da ke Felele. Ta ce, jami’an Sashen B…
Read More
Amarya ta saka wa angonta guba a abinci kwana 40 da aurensu

Amarya ta saka wa angonta guba a abinci kwana 40 da aurensu

An kama wata sabuwar amarya mai shekaru 19, Aisha Musa, bisa zargin sanya wa mijinta guba a cikin abincinsa a ƙauyen Gwamna, ƙaramar Hukumar Bauchi ta Jihar Bauchi. An ce lamarin ya faru ne kwanaki 40 kacal da auren ma’auratan. Rahotanni sun ce bayan mijin ya ci abincin ya fara fama da rashin lafiya. An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, inda yake karɓar magani. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kama matar da ake zargi da hannu a lamarin. Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru…
Read More
Gajerun wasannin kwaikwayo sun fara jan hankalin Hollywood

Gajerun wasannin kwaikwayo sun fara jan hankalin Hollywood

Daga AISHA ASAS  Masana'antar fina-finan Hollywood na fara ƙara karkata zuwa wani sabon salo na shirye-shiryen bidiyo gajeru da ake kallo kai tsaye ta wayar salula, yayin da masu shirya fina-finai ke neman sabbin hanyoyin samun masu kallo a zamanin TikTok. Rahoton Reuters ya bayyana cewa wannan salo, wanda ake kira 'microdramas', ya ƙunshi jerin shirye-shirye masu gajeren lokaci, inda kowane sashe zai iya ɗaukar tsakanin daƙiƙa 45 zuwa mintuna biyu. Asalin wannan salo ya samo asali ne daga Chana, amma yanzu ya samu babbar tagomashi a Amurka. Waɗannan shirye-shiryen suna amfani da labarai masu saurin tafiya, rikice-rikicen soyayya da…
Read More
Jarumar ‘Heroes’ Hayden Panettiere ta rasu tana da shekaru 36

Jarumar ‘Heroes’ Hayden Panettiere ta rasu tana da shekaru 36

Daga AISHA ASAS  Jarumar Hollywood Hayden Panettiere, wadda aka fi sani da rawar da ta taka a shirin Heroes da Nashville, ta rasu tana da shekaru 36. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Amurka sun tabbatar da mutuwar jarumar a ranar 16 ga Agusta 2026, kwanaki kaɗan kafin ta cika shekaru 37. Wakilinta ne ya tabbatar da mutuwar, yayin da labarin ya jawo alhini a tsakanin 'yan uwanta da masu sha'awar fina-finanta. Panettiere ta fara fitowa a fina-finai tun tana ƙarama, inda daga baya ta samu gagarumar shahara bayan ta taka rawar Claire Bennet, wata yarinya mai ƙarfin warkar da…
Read More
Burna Boy da Shakira na ci gaba da jagorantar jadawalin Billboard tsayin makwani biyar 

Burna Boy da Shakira na ci gaba da jagorantar jadawalin Billboard tsayin makwani biyar 

Daga AISHA ASAS  Waƙar 'Dai Dai' ta mawaƙin Najeriya Burna Boy da fitacciyar mawaƙiya 'yar Colombia Shakira ta ci gaba da riƙe matsayi na ɗaya a jadawalin Billboard Global 200, inda ta shafe mako na biyar a jere tana kan gaba. Billboard ta bayyana cewa waƙar, wadda ta kasance waƙar gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, ta ci gaba da samun gagarumar karɓuwa duk da cewa an kammala gasar tun kusan wata ɗaya da ya wuce. A jadawalin da aka sabunta a ranar 18 ga Agusta, Dai Dai ta ci gaba da kasancewa a matsayi na ɗaya. Bayanan Luminate…
Read More
Funke Akindele ta fitar da jerin jaruman sabon fim ɗinta

Funke Akindele ta fitar da jerin jaruman sabon fim ɗinta

Daga AISHA ASAS  Fitacciyar jarumar Nollywood kuma mai shirya fina-finai, Funke Akindele, ta bayyana jerin fitattun jaruman da za su fito a sabon fim ɗinta mai suna 'The Four: No One Fights Alone'. Fim ɗin, wanda za a fara nuna shi a gidajen sinima a faɗin duniya ranar 11 ga Disamba 2026, ya haɗa manyan sunaye daga Nollywood, ciki har da Funke Akindele, Bisola Aiyeola, Chioma Akpotha, Waje, Richard Mofe-Damijo, Timini Egbuson, Lateef Adedimeji, Ali Nuhu, Uzor Arukwe, Ronke Oshodi-Oke da Wunmi Toriola. Haka kuma fim ɗin zai kunshi fitattun mawaƙa da masu nishaɗi, ciki har da Waje da Shoday,…
Read More
Neche ta fice daga BBNaija a daidai lokacin da ta ke jagorantar gidan

Neche ta fice daga BBNaija a daidai lokacin da ta ke jagorantar gidan

Daga AISHA ASAS  Gidan Big Brother Naija Season 11 ya gamu da wani sabon sauyi bayan ɗaya daga cikin masu takarar shirin, Neche, ta yanke shawarar ficewa daga gasar da kanta. Masu shirya shirin sun bayyana cewa Neche ta ɗauki matakin ne saboda wasu matsalolin kanta da suka buƙaci kulawarta, lamarin da ya sanya ta bar gidan ba tare da an fitar da ita ta hanyar ƙuri'ar masu kallo ba. Neche ta sanar da ficewarta ne a ranar Lahadi, 16 ga Agusta, abin da ya ba sauran 'yan gidan mamaki, musamman ganin cewa a lokacin tana riƙe da mukamin Head…
Read More
Auren Adam Zango na takwas ya ƙara tayar da ƙura 

Auren Adam Zango na takwas ya ƙara tayar da ƙura 

Daga AISHA ASAS  Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure a Jamhuriyar Nijar, kwanaki kaɗan bayan kawo ƙarshen aurensa da jaruma Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty. Rahotanni sun ce an ɗaura sabon auren ne a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, da wata ’yar ƙasar Jamhuriyar Nijar. Zango ya tabbatar da sabon auren ta hanyar wallafa hotonsa tare da sabuwar amaryarsa, inda ya bayyana farin cikinsa da wannan sabon babi na rayuwarsa. A cikin saƙon da ya wallafa bayan auren, jarumin ya nemi masoyansa da su ci gaba da yi masa addu’ar samun…
Read More