ukarofi

11670 Posts
Siyasar Shekarau da Ganduje da Abba ta zo ƙarshe a Kano – Kwankwaso

Siyasar Shekarau da Ganduje da Abba ta zo ƙarshe a Kano – Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun rasa karfin siyasa a jihar. Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja, inda ya ce siyasar da aka gina bisa “cin amana” ba ta daɗewa. Ya ce rikicinsa da Ganduje ya fara ne lokacin da tsohon gwamnan ya fara ƙalubalantar tsarin siyasar da suka gina tare, yana mai cewa hakan ya janyo koma bayan siyasarsa.…
Read More
Bayan kayar da APC, goyon bayan Adeleke ga Tinubu ya raba kan magoya bayansa

Bayan kayar da APC, goyon bayan Adeleke ga Tinubu ya raba kan magoya bayansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sa’o’i kaɗan bayan tabbatar da nasarar samun wa’adin mulki na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Adeleke, wanda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, a zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Yayin da yake gode wa…
Read More
Tirka-tirkar canjin mataimakin gwamnan Jihar Kebbi

Tirka-tirkar canjin mataimakin gwamnan Jihar Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Tun bayan shari’ar da ta biyo bayan zargin takardun shaidar kammala karatun sakandare na Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Argungu, Tafidan Kabi, bayan babban zaɓen shekarar 2023, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ke adawa da shi suka yi ta ƙoƙarin ganin an sauya shi daga mukaminsa. Shari’ar ta haifar da zazzafar taƙaddama, inda ’yan jam’iyyar PDP suka kalubalanci nasarar Gwamna Malam Nasir Idris da mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Argungu. Yanzu dai rahotanni sun tabbatar da cewa an sauya Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Argungu, inda aka maye gurbinsa da Ibrahim Augie.…
Read More
Mutane 94 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Zimbabwe

Mutane 94 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Zimbabwe

Akalla mutane 94 sun mutu bayan wani jirgin ruwa mallakin gwamnatin Zimbabwe ya kife a tafkin Kariba, yayin da gwamnati ta tabbatar da cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji fiye da karfin da aka tanada masa. Jirgin ruwan ya kife ne a makon da ya gabata yayin da yake kan hanyarsa daga garin Kariba zuwa wata al'umma da ke zaune a wani yanki mai nisa na tafkin. Rahotanni sun ce guguwar ruwa mai karfi ce ta bugi jirgin, lamarin da ya sa ya kife. Gwamnatin Zimbabwe ta ce jirgin na ɗauke da kusan mutane 180 tare da kaya a lokacin…
Read More
Harin Rasha ya kashe mutane 10 a Ukraine yayin da Kiev ta kai hari kan Moscow

Harin Rasha ya kashe mutane 10 a Ukraine yayin da Kiev ta kai hari kan Moscow

Akalla mutane 10 sun mutu a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai wani ƙauye a yankin Kharkiv na Ukraine, yayin da Ukraine ita ma ta kai ɗaya daga cikin hare-haren jirage marasa matuka mafi girma kan Rasha tun bayan fara yakin. Harin na Rasha ya afkawa kauyen Pechenihy ne a ranar Talata, inda mutane 10 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 17 suka jikkata. Shugaban yankin Kharkiv ya ce fararen hula ne harin ya rutsa da su. A gefe guda kuma, Ukraine ta aika da kusan jirage marasa matuka 800 zuwa yankunan Rasha, ciki har da Moscow…
Read More
Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da kasuwanci da Iran

Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da kasuwanci da Iran

Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da dukkan harkokin kasuwanci da mu'amalar kuɗi da Iran har sai wani sabon sanarwa, matakin da ya ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu. Sanarwar ta zo ne bayan UAE ta ce ta gano makamai masu linzami guda biyu da aka harba daga Iran, waɗanda ta yi zargin cewa an nufi zirga-zirgar jiragen ruwa da su. Kasar ta ce makaman sun fada cikin teku, amma ta dauki matakin dakatar da harkokin kasuwanci saboda abin da ta kira ƙara tabarbarewar tsaron yankin.  Iran ta musanta zargin, inda kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, Esmaeil Baghaei, ya…
Read More
Jirgin helikwafta mai ɗauke da masu yawon buɗe ido ya faɗi a Kenya

Jirgin helikwafta mai ɗauke da masu yawon buɗe ido ya faɗi a Kenya

Wani jirgin helikwafta da ake zargin yana ɗauke da masu yawon bude ido ya yi hatsari a gundumar Samburu da ke arewacin Kenya. Kafofin yada labarai na cikin ƙasar, ciki har da The Star da Standard, ne suka fara kawo rahoton hatsarin a ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.  Rahoton farko bai bayyana cikakken adadin mutanen da ke cikin jirgin ko adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai kan abin da ya faru. Samburu na daga cikin wuraren da suka shahara a yawon buɗe ido a Kenya, musamman saboda namun…
Read More
Amurka da Koriya ta Kudu sun rage girman atisayen soji da suka yi niyya

Amurka da Koriya ta Kudu sun rage girman atisayen soji da suka yi niyya

Amurka da Koriya ta Kudu sun rage tsawon babban atisayen sojinsu na shekara-shekara, bayan umarnin Shugaban Amurka Donald Trump na a rage yawan atisayen. Atisayen Ulchi Freedom Shield, wanda aka fara a wannan makon, yanzu za a kammala shi bayan kwanaki biyar maimakon kwanaki 11 da aka tsara a baya. Haka kuma an rage wasu daga cikin atisayen sojin kasa.  Matakin ya zo ne bayan Trump ya nuna cewa ba ya son yawan atisayen soji da Koriya ta Kudu, yana mai cewa yana son sake buɗe ƙofar tattaunawa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.  Sai dai wasu masana…
Read More
Turkiyya ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Syria

Turkiyya ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Syria

Turkiyya ta yi kakkausar suka ga hare-haren sama da Isra'ila ta kai wani sansanin soji a Syria, tana mai cewa bayanan da Isra'ila ta bayar wajen kare matakin nata ba su da tushe. Isra'ila ta kai hare-hare takwas kan sansanin Abu al-Duhur da ke kusa da Aleppo a ranar Talata, a cewar kafafen yaɗa labaran Syria. An ce hare-haren sun shafi titin saukar jiragen sama da wasu wuraren ajiye kayan aiki, amma ba a samu rahoton mutuwar mutane ba.  Isra'ila ta ce matakin nata ya kasance ne saboda damuwar cewa Syria na shirin barin sojojin Turkiyya su yi amfani da…
Read More
Trump ya musanta tattaunawa da Iran, yayin da rikicin Hormuz ke ƙara tsananta

Trump ya musanta tattaunawa da Iran, yayin da rikicin Hormuz ke ƙara tsananta

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata tattaunawa da ke gudana tsakanin Amurka da Iran, yayin da Tehran ta ce har yanzu mashigar ruwan Hormuz a rufe take, lamarin da ya sake jefa shirin kawo ƙarshen rikicin ƙasashen biyu cikin rashin tabbas. Trump ya bayyana hakan ne ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, inda ya ce babu wata tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Washington da Tehran. Ya kuma dage cewa mashigar Hormuz a buɗe take, kuma ana iya zirga-zirgar jiragen ruwa a cikinta. Sai dai Iran ta musanta hakan, inda ta ce ba za ta buɗe mashigar ba…
Read More