23
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), Dakta Farouk Rabiu Mudi, ya sake jaddada cikakken goyon bayan ƙungiyar ga Ajandar Sabonta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a ƙasar. Mudi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya ce AFAN, a matsayinta na babbar ƙungiyar da ke haɗa manoma, ƙungiyoyin kayan amfanin gona, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma da sauran hukumomi masu alaƙa da noma, ta ƙuduri aniyar yin aiki tare da gwamnatin yanzu domin magance matsalar ƙarancin abinci tare da…
