ukarofi

11670 Posts
Gwamnatin Kano ta ƙaryata zargin Tracka kan aikin ilimi na miliyan N235.4

Gwamnatin Kano ta ƙaryata zargin Tracka kan aikin ilimi na miliyan N235.4

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da wani rahoto da ƙungiyar Tracka ta wallafa, wanda ya yi zargin cewa an ware Naira miliyan 235.4 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 domin gina ajujuwa a Government Girls Secondary School, Massu, da ke ƙaramar Hukumar Sumaila. Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin mai ɓatarwa kuma wanda ba shi da cikakkiyar hujja. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a zauren taro na…
Read More
Dalilin da ya sa El-Rufai ya maka ICPC a kotu

Dalilin da ya sa El-Rufai ya maka ICPC a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya maka Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin hana shi ganin iyalansa yayin da yake tsare a hannun hukumar. A cikin ƙarar da lauyansa, Ubong Akpan, ya shigar a ranar 13 ga Agusta, 2026, El-Rufai ya ce ICPC ta hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa. Tsohon gwamnan ya ce matakin ya tauye masa haƙƙin samun kulawa da hulɗa da iyalansa yayin da yake tsare. Ya kuma yi zargin cewa hana shi hulɗa da…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi a manyan makarantu

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi a manyan makarantu

Daga RABIU SANUSI a Kano Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta haɗa kai da manyan makarantun gaba da sakandare domin faɗaɗa shirin dasa bishiyoyi da inganta kiyaye muhalli a faɗin jihar. Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya ƙaddamar da shirin a Kwalejin Musulunci da Ilimin Shari’a ta Mallam Aminu Kano, wato Legal, inda mahukuntan makarantar da wakilan ɗalibai suka nuna goyon bayansu ga shirin. Sun kuma yi alƙawarin kula da bishiyoyin da aka dasa tare da tabbatar da an kare su daga lalacewa. A ƙarƙashin shirin,…
Read More
Babu shugaban da ya sauya tarihin Nijeriya kamar IBB — Tinubu

Babu shugaban da ya sauya tarihin Nijeriya kamar IBB — Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa da ya taka rawa wajen sauya tarihin Nijeriya kamar tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya). Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙonsa na taya tsohon shugaban ƙasar murnar cika shekaru 85 da haihuwa. A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Babangida a matsayin fitaccen shugaba, wanda ƙwarewarsa a aikin soja ta kai ga zama shugaban ƙasa bayan juyin mulkin 1985. Shugaban…
Read More
Matsalar hare-haren ‘yan bindiga ta ragu sosai a lokacin Raɗɗa – Joɓe

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga ta ragu sosai a lokacin Raɗɗa – Joɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruk Joɓe, ya ce a lokacin da gwamnatin Dikko Radda ta kama aiki a shekarar 2023, hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun yi ƙamari a kusan ƙananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar. Jobe ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake wakiltar gwamna Radda a taron rubu’i na biyu na shekarar 2026 na daraktocin hukumomin tsaro na jihohin Arewa maso Yamma wanda aka gudanar a shalkwatar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da ke Katsina. Taron, mai taken “Haɗa Kai Don Yaƙar Ta’addanci”, ya…
Read More
Tsadar kayan masarufi ta ƙaru a watan Yuli

Tsadar kayan masarufi ta ƙaru a watan Yuli

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farashin kayayyakin masarufi ya ƙaru a watan Yuli a Nijeriya, duk da matakan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka domin bunƙasa samar da kayayyaki a cikin gida da rage kuɗin sarrafa su, da nufin sauƙaƙa wa ’yan ƙasa halin tsadar kayan abinci. Hauhawar farashin ta haifar da damuwa game da tasirin matakan da gwamnati ke ɗauka domin samar da sauƙi a farashin kayan abinci. Sabbin alƙaluman da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 20.31 cikin 100 cikin watanni 12 da suka gabata. Rahoton ya…
Read More
Ya kamata gwamnatin Kano ta sake tunani kan shiga kasuwancin sufurin jiragen sama — Abbati Baƙo

Ya kamata gwamnatin Kano ta sake tunani kan shiga kasuwancin sufurin jiragen sama — Abbati Baƙo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Masanin kimiyyar siyasa da tattalin arziki, Abbati Baƙo, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya sake duba shirin kafa kamfanin jirgin saman da gwamnatin jihar za ta mallaka. Abbati Baƙo ya yi wannan kiran ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya aikewa Gwamnan Kano, inda ya bayyana cewa jihar na buƙatar mayar da hankali kan muhimman abubuwan more rayuwa da jin daɗin al’umma, maimakon gwamnati ta shiga harkar gudanar da kasuwancin sufurin jiragen sama. Ya ce Kano za ta iya samun ci gaba sosai, amma ya kamata ta…
Read More
Kwastom ta miƙa bindiga 399 da aka ƙwace ga ofishin Ribadu

Kwastom ta miƙa bindiga 399 da aka ƙwace ga ofishin Ribadu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta miƙa bindiga guda 399 da aka ƙwace tare da tarin wasu muhimman kayayyakin bindigogi, ga Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, bayan kammala bincike kan wani katafaren makaman da aka tare a tashar jiragen ruwa ta Tsibirin Tincan da ke Legas. Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce an kammala haɗa bindigogin da aka tarwatsa tare da gudanar da cikakken bincike kan kayayyakin da aka kama. A cewarsa, binciken ya tabbatar da cewa kayan…
Read More
Kotu ta umarci bankuna 71 su rufe asusun da aka ajiye kuɗaɗen damfarar bankin Access

Kotu ta umarci bankuna 71 su rufe asusun da aka ajiye kuɗaɗen damfarar bankin Access

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta umarci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi guda 71 da su sanya takunkumin fitar da kuɗi daga wasu asusu da ake zargin an yi amfani da su wajen adana wani kaso na Naira biliyan 1.34 da aka karkatar ba bisa ƙa’ida ba daga asusun wasu kwastomomin Bankin Access, ta hanyar manhajar bankin ta intanet mai suna Access SME App. Mai shari’a Akintayo Aluko ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin, bayan lauyan Bankin Access, Ifeoma E. Enyinnaya, ta shigar da buƙatar gaggawa a gaban kotun ba tare…
Read More
Majalisar NSDC ta jawo jarin Dala biliyan ɗaya don Nijeriya ta daina dogaro da sukarin waje

Majalisar NSDC ta jawo jarin Dala biliyan ɗaya don Nijeriya ta daina dogaro da sukarin waje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Bunƙasa Masana’antar Sukari ta ƙasa (NSDC) ta ƙara ƙaimi wajen jawo jarin masana’antar sukari, inda ta ƙulla haɗin gwiwar zuba jari na Dala biliyan 1 da kamfanin SINOMACH na ƙasar Chana, domin hanzarta samar da sukari a cikin gida da rage dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje. Haɗin gwiwar na daga cikin shirin Asusun Hanzarta Ayyukan Sukari na Naira biliyan 10, wanda NSDC ta kafa tare da Bankin Masana’antu a ƙarƙashin Shirin Haɗa Samar da Kayayyaki a Cikin Gida (BIP). Babban Sakatare kuma Babban Daraktan NSDC, Kamar Bakrin, ne ya bayyana hakan a…
Read More