ukarofi

11670 Posts
Majalisar Dokokin Nijeriya ce majalisa mafi yawan ma’aikata a duniya — Magatakarda

Majalisar Dokokin Nijeriya ce majalisa mafi yawan ma’aikata a duniya — Magatakarda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dokokin Tarayyar Nijeriya na da ma’aikata sama da 14,000, ban da ’yan majalisar tarayya 469 da kuma ɗimbin baƙi da ke ziyartar majalisar, lamarin da ya sanya ta zama ɗaya daga cikin majalisun da suka fi yawan ayyuka a duniya. Magatakardar Majalisar Dokokin Nijeriya (CNA), Kamoru Ogunlana, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron ƙarshe na shirin ƙara wa mataimakan ’yan majalisa ƙwarewa a Majalisa ta 10. Ogunlana ya ce, yawan ma’aikatan majalisar, ’yan majalisa da kuma baain da ke ziyartar majalisar a kullum ya sa gudanar da ayyukan majalisar tarayya ya kasance…
Read More
AI zai taimaka wa ƙanana ’yan kasuwa rage kashe kuɗaɗe – Bincike

AI zai taimaka wa ƙanana ’yan kasuwa rage kashe kuɗaɗe – Bincike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani sabon bincike ya nuna cewa amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI na iya taimaka wa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa a Nijeriya wajen inganta aiki, rage kashe kuɗaɗen gudanarwa da kuma ƙara musu damar gogayya a kasuwa. Binciken, wanda Dr Ayodeji Idowu ya gudanar kuma aka wallafa a International Journal of Comparative Studies in International Relations and Development, ya ce ci gaban fasahar ajiyar bayanai a ma'adana, wato cloud computing, dandamalin zamani masu sauƙin amfani da kuma API ya rage wahalar da ƙananan kamfanoni ke fuskanta wajen rungumar fasahar AI. Masanin ya bayyana cewa ƙananan…
Read More
Sarrafa amfanin gona a gida ne ginshiƙin wadatar abinci a Nijeriya – Tajudeen

Sarrafa amfanin gona a gida ne ginshiƙin wadatar abinci a Nijeriya – Tajudeen

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kakakin Majalisar Wakilan Tarayyar Nijeriya, Hon. Abbas Tajudeen, ya sake jaddada aniyar Majalisar Dokokin Tarayya na samar da cikakken goyon baya da kariya ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na cikin gida da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa masana’antu da samar da kayayyaki a Nijeriya. Kakakin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin ƙaddamar da sabuwar masana’antar Simkay Foods Limited da za ta riƙa sarrafa masara tare da samar da garin masara da kuma abubuwan da suka shafi masara na masara a yankin Zazzau Industrial Park and Industries (ZIPI) da ke Zariya,…
Read More
Naira ta ƙara ƙarfi yayin da asusun waje ya haura Dala biliyan 52.5 — CBN

Naira ta ƙara ƙarfi yayin da asusun waje ya haura Dala biliyan 52.5 — CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kimar Naira na ci gaba da samun tagomashi, yayin da tazarar farashinta tsakanin kasuwar hukuma da ’yan canjin kuɗi ta ragu zuwa ƙasa da kashi biyu cikin 100. A halin da ake ciki, Asusun Ajiyar ƙasar Waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 52.5 zuwa ranar 17 ga Yuli, 2026, matakin da ya kai mafi girma cikin shekaru 17, tare da zarce burin shekara-shekara da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanya. CBN ya ce, wannan ƙaruwa ta samu ne sakamakon ci gaba da shigowar kuɗaɗen waje cikin ƙasar da kuma sake farfaɗowar amincewar masu zuba jari…
Read More
Cin kifi mai guba ya yi sanadin mutuwar almajirai huɗu a Kano

Cin kifi mai guba ya yi sanadin mutuwar almajirai huɗu a Kano

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Almajirai huɗu sun rasu a Jihar Kano bayan sun kamu da matsananciyar rashin lafiya sakamakon cin wani kifi da ake zargin ya gurɓata, yayin da wani ɗalibi ya tsira bayan ya dakatar da cin kifin tun kafin ya kammala. Mamatan sun haɗa da Abdulfatah Mohammed, mai shekaru 15; Yusuf Nuhu, 16; Buhari Iliyasu, 14; da Ibrahim Muhammad, mai shekaru 22. Dalibi na biyar, Auwalu Surajo, mai shekaru 18, ya tsira bayan ya ƙi ci gaba da cin kifin, kuma a halin yanzu yana karɓar magani. Daliban suna karatu a wata makarantar Tsangaya ta koyar da Alƙur’ani…
Read More
Tinubu ya naɗa Famadewa ya jagoranci Ribaɗu da Musa a kwamitin shirya tsaron ƙasa

Tinubu ya naɗa Famadewa ya jagoranci Ribaɗu da Musa a kwamitin shirya tsaron ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwamitin Duba Barazanar Tsaron ƙasa (National Threat Assessment) da kuma Tsarin Ayyukan Tsaron ƙasa na Shekaru biyar, domin inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, leƙen asiri da rundunonin sojin Nijeriya. Shugaban ya kuma naɗa Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa, a matsayin wanda zai jagoranci aikin tare da samar da sakatariyar kwamitin mutum 11 da aka kafa domin tsara sabon tsarin tsaron ƙasar. An bayar da umarnin ne ranar Laraba yayin taron Majalisar Zartarwa ta ƙasa…
Read More
Shugaban SDP na Nasarawa ya nesanta kansa da Adamu da ’yan majalisar da suka sauya sheƙa

Shugaban SDP na Nasarawa ya nesanta kansa da Adamu da ’yan majalisar da suka sauya sheƙa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a Jihar Nasarawa kuma shugaban Inter-Party Advisory Council (IPAC) na jihar, Hon. Danlami Mohammed Musa, ya nesanta kansa da sauya sheƙar wasu ’yan Majalisar Dokokin Jihar ta Nasarawa zuwa jam’iyyar, yana mai cewa ba a bi ƙa’idar da ta dace ba wajen shigar da su jam’iyyar. ’Yan majalisar da abin ya shafa sun haɗa da Jacob Kudu mai wakiltar Nasarawa Eggon East da Mohammed Adamu Omadefu mai wakiltar Keana, waɗanda suka fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Kakakin Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya sanar da sauya…
Read More
Ma’aikatan jin ƙai sun yaba wa Dakta Margaret kan magance matsalar ambaliya

Ma’aikatan jin ƙai sun yaba wa Dakta Margaret kan magance matsalar ambaliya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar ma’aikatan ayyukan jin ƙai wato Social Workers a turance ta Najeriya reshen jihar Nasarawa ta yaba wa Gimbiya Dr. Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa bisa jajircewarta wajen magance matsalolin muhalli da gaskiya da ƙarfin gwiwa musamman ambaliyar ruwa a yanzu da damina ta yi nisa. Ƙungiyar ta gabatar da wannan yabo ne yayin ziyarar girmamawa da shugabannin reshen jihar suka kai wa kwamishinan a ofishinta da ke Lafia babban birnin jihar. Da yake jawabi shugaban ƙungiyar a jihar Nasarawa Prince Ogiri Gambo Adamu ya ce manufar ziyarar tasu ita ce…
Read More
‘Yan sanda sun ƙaddamar da yaƙi da bangar siyasa a Katsina

‘Yan sanda sun ƙaddamar da yaƙi da bangar siyasa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda sun ƙaddamar da yaƙi da bangar siyasa da laifuka ta amfani da yanar gizo da sauran manyan laifuka a Katsina. Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Katsina CP Ali Umar Fage ya sanar da haka a lokacin da yake buɗe taron ranar matasa na duniya a Katsina. Kwamishinan wanda mataimakin kwamishinan 'yan sanda na sashin bincike DCP Aminu Gusau ya wakilta yi gargaɗi duk wanda aka samu yana ɗaukar nauyi ko amfani da matasa wajen bangar siyasa,"zamu yi bincike,mu kama da gurfanar da duk wanda muka kama a gaban kuliya. CP Ali Umar…
Read More
An karrama Dakta Margaret da lambar yabo ta kwamishiniya mafi hazaƙa a Nijeriya

An karrama Dakta Margaret da lambar yabo ta kwamishiniya mafi hazaƙa a Nijeriya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An karrama kwamishiniyar muhalli da albarkatun ƙasa na gwamnatin jihar Nasarawa gimbiya Dr. Margaret Elayo da lambar yabo na musamman wato kwamishiniya wace tayi zarra a ƙwarewa da aiki tuƙuru da kuma hidima na musamman ga mutane. An bai wa kwamishiniyar wannan karramawar ne a wani babban taro da Arewa Media Publications ta shirya a ranar Alhamis na makon da ake ciki inda kuma har aka ba ta lambar yabo na International Merit Award for Excellence in Leadership a turance ta shekarar 2026. Wato dai hakan na nufin kamar yadda ake ce wa ne…
Read More