22
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruk Joɓe, ya ce a lokacin da gwamnatin Dikko Radda ta kama aiki a shekarar 2023, hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun yi ƙamari a kusan ƙananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar. Jobe ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake wakiltar gwamna Radda a taron rubu’i na biyu na shekarar 2026 na daraktocin hukumomin tsaro na jihohin Arewa maso Yamma wanda aka gudanar a shalkwatar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da ke Katsina. Taron, mai taken “Haɗa Kai Don Yaƙar Ta’addanci”, ya…
