11
Oct
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina a ƙarƙashin sabon shugabancinta, ta fitar da sabbin umarni da suka shafi amfani da muƙaman aiki, tantance jami’anta da kuma hana yaɗa bayanan sirri na hukumar a kafofin sadarwa ba tare da izini ba. A cikin wata takardar sanarwa wanda darakta mulki na hukumar Malam Bello Gatari Barau ya aika wa kwamandojin hisbah na ƙananan hukumomi 34 na jihar, Hukumar ta buƙaci a tabbatar da bin ƙa’idojin aiki tare da ɗaukar matakan ladabtarwa kan duk wanda ya saɓa. Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa jami’an hisbah ɗaukar, amfani da…
