12
Oct
Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano Daya daga cikin matasa ’yan kasuwa kuma shugaban kamfanin Yammusa da ke Kano, Alhaji Ashiru Yammusa, ya bayyana cewa addu’a da burinsu shi ne ganin Nijeriya, wadda ta samu ’yancin kai a shekarar 1960, ta zama ƙasa mafi tsaro da zaman lafiya tare da tarin arziki. Ya ce burinsu shi ne ganin an samu ƙasa da za a rasa masu kwana da yunwa, a rage yawan matasa marasa aikin yi, a samu ingantaccen tsarin kiwon lafiya, bunƙasar noma da kiwo, ingantaccen tsarin sadarwa da zirga-zirga, da kuma tituna da hanyoyi masu kyau ba tare da…
