ukarofi

12418 Posts
Gwamnatin Tarayya ta buɗe damar bayar da lasisin haƙo mai na 2026

Gwamnatin Tarayya ta buɗe damar bayar da lasisin haƙo mai na 2026

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta buɗe zagayen bayar da lasisin haƙo albarkatun man fetur na shekara ta 2026, inda ta fitar da filayen haƙar mai 40 da suka haɗa da na tsandaurin ƙasa, ruwa maras zurfi da kuma ruwa mai zurfi domin jawo sabbin masu zuba jari cikin harkar haƙo mai da iskar gas. Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ce ta sanar da fara zagayen lasisin a ranar Talata, inda Babbar Daraktar Hukumar, Oritsemeyiwa Eyesan, ta ce an ɗauki matakin ne bayan samun amincewar Shugaban ƙasa Bola Tinubu da Ministan…
Read More
Dangote na fuskantar matsin lamba a Kenya yayin da ’yan adawa ke buƙatar a fayyace komai

Dangote na fuskantar matsin lamba a Kenya yayin da ’yan adawa ke buƙatar a fayyace komai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan adawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a ƙasar Kenya sun ƙara matsa wa gwamnatin Shugaba William Ruto lamba kan abin da suka bayyana a matsayin rashin cikakken bayani da gaskiya game da shirin gina matatar mai da masana’antar sinadaran man fetur ta Dangote a Lamu. Ana ƙiyasta darajar aikin da kusan Sh2 tiriliyan, kwatankwacin dala biliyan 16. Shirin haɗin gwiwar da ɗan kasuwar Nijeriya, Aliko Dangote, da Shugaba Ruto suka ƙaddamar a ranar 30 ga Satumba, 2026, ya jawo cece-kuce kan tsarin mallakar kamfanin da zai gudanar da aikin a Kenya, kaso da gwamnatin Kenya ke…
Read More
Dangote ya dakatar da sayar da fetur ga masu shigo da shi

Dangote ya dakatar da sayar da fetur ga masu shigo da shi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar Man Fetur ta Dangote ta dakatar da sayar da man fetur ga manyan ’yan kasuwar man fetur da ke shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya, lamarin da ya ƙara tsananta taƙaddamar da ke tsakanin matatar da masu shigo da fetur. Wani jami’in matatar ya tabbatar da matakin, inda ya ce matatar ba za ta cigaba da sayar da fetur ga ’yan kasuwar da ke haɗa man Dangote da fetur da suka shigo da shi daga ƙasashen waje ba. “Ba ma sayar da fetur ga waɗanda ke shigo da shi, saboda suna…
Read More
Kano Film Village: Abdullaziz Dansmall ya gina sabuwar mafita ga Kannywood

Kano Film Village: Abdullaziz Dansmall ya gina sabuwar mafita ga Kannywood

Daga AISHA ASAS Samar da Kano Film Village na ƙara jan hankalin masana’antar fina-finan Hausa, bayan wani sabon rahoto da ya sake bayyana irin ci gaban da cibiyar ke samu a Kano. Wurin da aka samar domin sauƙaƙa wa masu shirya finafinai wajen samun wuraren ɗaukar shirye-shirye, an gina shi ne a hankali karkashin jagorancin ɗan fim kuma tsohon mai watsa shirye-shirye, Abdullaziz Dansmall. Rahoton City People da aka wallafa ranar 5 ga Oktoba ya bayyana cewa, Film Village da aka tsara a Kano a shekarar 2016 ba gwamnatin tarayya ce ta samar da shi ba, wanda daga baya aka…
Read More
Amitabh ya nemi gafarar Madhuri a KBC

Amitabh ya nemi gafarar Madhuri a KBC

Daga AISHA ASAS Fitaccen jarumin Bollywood, Amitabh Bachchan, ya sake ɗaukar hankalin masoyan fina-finan Indiya bayan wani yanayi na ban dariya da ya faru tsakaninsa da jarumar Bollywood, Madhuri Diɗit, a shirin Kaun Banega Crorepati (KBC) na kakar 18. A wani shiri na musamman, Bachchan ya tuna yadda ya taɓa kwaikwayon wani salon rawa da Madhuri ta yi a fim ɗinta na 'Tezaab', inda ya yi amfani da salon daga waƙar “Ek Do Teen”. Daga baya ya nemi gafararta a bainar jama’a, yana mai cewa ya yi “babban kuskure”.  Sai dai lamarin bai kasance wata rigima ba, domin komai ya…
Read More
CANEX 2026: Nijeriya na yunƙurin juya basirar ’yan ƙasa zuwa kuɗi da ayyukan yi – Hannatu Musawa

CANEX 2026: Nijeriya na yunƙurin juya basirar ’yan ƙasa zuwa kuɗi da ayyukan yi – Hannatu Musawa

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta ce taron Creative Africa Neɗus (CANEɗ) na 2026 da Najeriya za ta karɓi baƙuncinsa a watan Nuwamba ba zai tsaya kan baje kolin basirar ’yan ƙasar ba, domin an tsara shi ne domin samar da jarin kuɗi, ayyukan yi da sabbin haɗin gwiwar kasuwanci a masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire. Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arziƙin ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musa Musawa, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai na ministoci kan shirye-shiryen Najeriya na karɓar CANEɗXWKND 2026. Musawa ta ce CANEɗ wani dandali ne da aka tsara domin haɗa masu fasaha da ’yan…
Read More
Jarumi Femi Adebayo ya buɗe katafariyar cibiyar finafinai

Jarumi Femi Adebayo ya buɗe katafariyar cibiyar finafinai

Daga AISHA ASAS Nollywood ta ƙara samun wata muhimmiyar cibiyar samar da finafinai da sauran abubuwan da suka jiɓinci nishaɗi bayan jarumi kuma furodusa Femi Adebayo ya ƙaddamar da Euphoria 360 Hub a Oregun da ke Legas. An ƙaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, 6 ga Oktoba, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Legas, Dr Kadri Obafemi Hamzat, ya jagoranci bikin. Cibiyar ta ƙunshi wuraren shirya finafinai masu inganci, ɗaukar bidiyon waƙoƙi, samar da abubuwan cikin gida, aikin gyaran sauti da hoto bayan ɗaukar fim, da kuma wasu ayyukan da masu sana’ar nishaɗi ke buƙata. Amma abin da ya sa aikin…
Read More
An dakatar ba basarake bisa zargin shiga harkokin siyasa a Kebbi

An dakatar ba basarake bisa zargin shiga harkokin siyasa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Karamar hukumar Kalgo da ke jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Alhaji Kabir Usman daga matsayin sa na magajin garin Nayilwa. Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙaramar hukumar Kalgo Umar Faruk Sama'ila a madadin shugaban ƙaramar hukumar ranar 11 ga wannan watan na Oktoba. Takardar ta bayyana cewa an dakatar da basaraken ne bisa ga zarge-zargen tsunduma a cikin harkokin siyasa da ya saɓa wa dokar masarauta.Har wa yau takardar ta bayyana cewa an naɗa kwamitin bincike kan wannan lamarin kafin ɗaukar mataki na gaba.Wakilin…
Read More
Hollywood ta shiga sabon zamani bayan Paramount ta kammala sayen Warner Bros

Hollywood ta shiga sabon zamani bayan Paramount ta kammala sayen Warner Bros

Daga AISHA ASAS Hollywood ta shiga wani sabon babi bayan Paramount Skydance ta kammala yarjejeniyar sayen Warner Bros Discovery a wata babbar mu’amala da darajarta ta kai kusan dala biliyan 110, inda aka haifi sabon katafaren kamfanin nishaɗi mai suna Skydance. Haɗewar ta tattaro wasu daga cikin manyan sunayen Hollywood a ƙarƙashin kamfani guda, ciki har da gidajen finafinai da ke bayan Mission: Impossible, Harry Potter da DC Studios, tare da manyan dandamali da kafafen yaɗa labarai kamar Paramount+, HBO Maɗ, CBS da CNN. David Ellison ne zai jagoranci sabon kamfanin, yayin da aka tsara rage wasu daga cikin kuɗaɗen…
Read More
Hollywood ta yi bankwana da Eva Saint, jarumar da ta yi suna tun zamanin Marlon Brando

Hollywood ta yi bankwana da Eva Saint, jarumar da ta yi suna tun zamanin Marlon Brando

Daga AISHA ASAS Hollywood ta yi rashin fitacciyar jaruma Eva Marie Saint, wadda ta rasu tana da shekara 102, bayan ta shafe sama da shekaru sittin tana taka rawar gani a finafinai da talabijin. Saint ta shiga tarihin Hollywood tun daga fim ɗinta na farko, 'On the Waterfront', na shekarar 1954, inda ta fito tare da Marlon Brando kuma ta lashe lambar yabo ta Oscar saboda rawar da ta taka. Daga bisani ta ƙara samun shahara bayan ta fito a 'North by Northwest' na Alfred Hitchcock tare da Cary Grant. A tsawon rayuwarta, ta yi aiki tare da wasu manyan…
Read More