ukarofi

12418 Posts
Bollywood: Kiara Advani da Sidharth Malhotra sun haifi ɗansu na biyu

Bollywood: Kiara Advani da Sidharth Malhotra sun haifi ɗansu na biyu

Daga AISHA ASAS Fitattun ma’auratan Bollywood, Kiara Advani da Sidharth Malhotra, sun sake faranta ran masoyansu bayan sun sanar da cewa suna jiran haihuwar ɗansu na biyu. Ma’auratan sun bayyana hakan ne a ranar Laraba, 7 ga Oktoba, ta hanyar wani saƙo da suka wallafa tare a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana farin ciki da godiyarsu kan sabon ɗan da suke jira. Kiara da Sidharth sun yi aure a shekarar 2023, sannan suka samu ɗiyarsu ta farko, Saraayah, a watan Yuli na 2025. Sanarwar haihuwar ta biyu ta jawo saƙonnin taya murna daga abokan aikinsu da sauran fitattun mutane…
Read More
AICWA ta nemi a hukunta masu laifi a gobarar Film City

AICWA ta nemi a hukunta masu laifi a gobarar Film City

Daga AISHA ASAS Wata gobara da ta tashi a Film City da ke Mumbai a ranar Litinin, ta jefa masana’antar fina-finan Indiya cikin damuwa, bayan wutar ta kama wani set ɗin Pati Patni Aur Panga 2 tare da bazuwa zuwa wani wurin da ake shirya Hustle 5. Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 4 na yamma a wani set da ke Prime Focus Studio, Goregaon, kafin ta bazu zuwa wani set da ke kusa. Duk da girman wutar, babu rahoton mutuwar mutum ko wani rauni, yayin da aka kwashe ma’aikata daga wuraren da ke cikin haɗarin. Amma lamarin…
Read More
Malamai sama da 1,000 sun yi taro a Kano don sukar manufofin Tinubu 

Malamai sama da 1,000 sun yi taro a Kano don sukar manufofin Tinubu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sama da malamai 1,000 daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya sun gudanar da wani taro a Kano, inda suka tattauna kan halin da ƙasar ke ciki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma zaɓen 2027. Taron mai taken “Nazari kan Halin da ƙasa ke Ciki a Zamanin Shugaba Tinubu da Zaɓen 2027”, ƙungiyar Ko Da Naka ce ta shirya tare da haɗin gwiwar AFAƙ Educational Foundation a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026. ƙungiyar Ko Da Naka, wadda Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid ke jagoranta, ta ce ba ta jingina kanta da wata…
Read More
2027: Ministan Ilimi ya yi alƙawarin kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 10

2027: Ministan Ilimi ya yi alƙawarin kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 10

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce bangaren ilimi na da burin tattara kuri’u miliyan 10 domin sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Alausa ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron farko na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai kula da Wayar da Kan Bangaren Ilimi, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su faɗaɗa ayyukan wayar da kai daga makarantu zuwa al’ummomi daban-daban a faɗin ƙasar. Ministan ya ce yawan ɗalibai, malamai, malaman jami’o’i, masu gudanar da makarantu, majalisun gudanarwa, ƙungiyoyin ƙwararru…
Read More
Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilun jihar Legas — Sarkin Hausawan Ladiboye

Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilun jihar Legas — Sarkin Hausawan Ladiboye

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin Hausawan Unguwar Ladiboye da ke ƙaramar Hukumar Ikorodu Central a Jihar Legas, Alhaji Adamu Haladu Mohammed, ya bayyana cewa Hausawa mazauna yankin na ƙara samun zaman lafiya da kyakkyawar fahimta tare da sauran ƙabilun da ke zaune a yankin. Alhaji Adamu, wanda kuma ɗan kasuwa ne kuma shugaban Kasuwar Ladiboye da ke Ikorodu, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wasu wakilan kafafen yaɗa labarai kan yadda zaman takewar al’ummar Hausawa da sauran ƙabilun da ke zaune a Unguwar Ladiboye da Ƙaramar Hukumar Ikorodu ke gudana. Sarkin ya bayyana jin daɗinsa kan…
Read More
Yadda ƙungiyar kawo cigaban ’Yan Arewa mazauna Ikorodu ta gudanar da taro a kasuwar Igbodu

Yadda ƙungiyar kawo cigaban ’Yan Arewa mazauna Ikorodu ta gudanar da taro a kasuwar Igbodu

Daga DAUDA USMAN a Legas Kungiyar Arewa Development Association Ikorodu, wato ƙungiyar Kawo Cigaban ’Yan Arewa Mazauna ƙaramar Hukumar Ikorodu, ta gudanar da wani taro a yankin Igbodu Market da ke ƙaramar Hukumar Ikorodu a Jihar Legas. An gudanar da taron ne a ranar Juma’a da ta gabata, ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar, Mai Martaba Sarkin Hausawan Igbodu Market, Alhaji Bello Sale, domin ƙara haɗa kan mambobin ƙungiyar tare da neman shawarwarinsu kan hanyoyin tunkarar matsalolin da ka iya fuskantar al’ummar Arewa mazauna yankin. Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar da mambobinta daga sassa daban-daban na ƙaramar Hukumar Ikorodu, da kuma…
Read More
Matawalle ya bayar da mota ɗaya da babura goma ga magoya bayansa a Zamfara

Matawalle ya bayar da mota ɗaya da babura goma ga magoya bayansa a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙaramin ministan tsaro Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya bayar da kyautar mota ɗaya da babura goma ga ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke goyon bayansa a Jihar Zamfara. An bayar da tallafin ne ga ƙungiyar da Alhaji Salisu Dawa ke jagoranta a ƙarƙashin Matawalle Political Standing Committee (MPSC). A cikin wata sanarwar ga manema labarai da sakataren yaɗa labarai na kwamitin, Yusuf Idris Gusau, ya fitar yau Asabar, Ministan ya ce wannan taimako wani ɓangare ne na shirinsa na ci gaba da ƙarfafa magoya bayansa masu yawa a jihar. Matawalle, wanda Shugaban tafiyar siyasar sa…
Read More
Zargin badaƙalar kuɗi: Farfaganda da baƙin ciki ne – Shugabar NAWOJ ta Nasarawa

Zargin badaƙalar kuɗi: Farfaganda da baƙin ciki ne – Shugabar NAWOJ ta Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida ta ƙasa (NAWOJ), reshen Jihar Nasarawa, Kwamared Mercy Tazan Zabadi, ta bayyana zargin da ake yi mata na karkatar da kuɗaɗe da kuma gudanar da ƙungiyar ita kaɗai a matsayin farfaganda da baƙin ciki. Zabadi ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da jaridar Manhaja a Lafia, yayin da take mayar da martani kan zargin da wasu mambobin zartarwarta suka yi mata. A cewarta, zargin ba shi da tushe balle makama kuma an yi shi ne da nufin ɓata mata suna da kuma na zartarwarta a…
Read More
Naɗin Ali Ado Dagacin ƙaura Goje abu ne na farin ciki ga al’ummar Gama da ƙaura Goje — Danjummai

Naɗin Ali Ado Dagacin ƙaura Goje abu ne na farin ciki ga al’ummar Gama da ƙaura Goje — Danjummai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Alhaji Abdullahi Sulaiman, wanda aka fi sani da ɗanjummai, ɗaya daga cikin amintattun abokan sabon Dagacin ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, ya bayyana naɗin da abokinsa ya samu a matsayin wata ni’ima da ta cancanci godiya ga Allah, kasancewar lamari ne mai tsohon tarihi wanda ya gangaro tun daga iyaye da kakanni. Danjummai ya bayyana haka ne yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan gagarumin ci gaba mai muhimmanci da aka samu a yankin. A cewarsa, daga cikin waɗanda suka bayar da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da wannan naɗi akwai Shugaban ƙaramar Hukumar Nassarawa,…
Read More
Majalisar ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta yi garambawul a shugabannin zartaswanta 

Majalisar ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta yi garambawul a shugabannin zartaswanta 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar ƙolin Shari’a ga Harkokin Addinin Musulunci ta ƙasa (NSCIA) ta ce ta yi wa Majalisar Zartarwarta ta ƙasa (NEC) garambawul tare da faɗaɗa ta, domin ƙarfafa tsarin gudanarwa da ayyukanta. Jami’in hulɗa da jama’a na majalisar, Abbas Jimoh, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan wasu shawarwari da aka cimma a Babban Taron Majalisar (General Assembly) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026. Ya ce taron ya samu halartar shugabannin Musulmi, ciki har da sarakunan gargajiya Musulmi da manyan…
Read More