ukarofi

12418 Posts
Yadda ’yan bindiga a ƙauyen Nasarawa suka rufe hanyar Gusau-Sakkwato, suka yi  garkuwa da matafiya

Yadda ’yan bindiga a ƙauyen Nasarawa suka rufe hanyar Gusau-Sakkwato, suka yi  garkuwa da matafiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun mamaye yankin Nasarawa da ke cikin al’ummar Damba, a wajen birnin Gusau na Jihar Zamfara, inda suka kai hari kan mazauna yankin tare da yunkurin satar dabbobi. Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne cikin daren Litinin, inda suka mamaye wurare daban-daban masu muhimmanci domin hana yiwuwar samun taimako daga wasu al’ummomin da ke kusa. Wata mata da ta tsira daga harin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa jaridar cewa ’yan bindigar sun kai farmaki yankin Nasarawa da misalin ƙarfe 1:00…
Read More
Biyan kuɗin fansa na ƙara wa ‘yan bindiga ƙarfi – Gwamna Lawal

Biyan kuɗin fansa na ƙara wa ‘yan bindiga ƙarfi – Gwamna Lawal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga na kara musu karfin gwiwa tare da ba su damar sayen manyan makamai. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channel,  inda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘yan bindiga domin biyan fansa ba. Ya ce, “Matsayina tun daga farko shi ne ba za mu yi sulhu da ‘yan bindiga ba, kuma har yanzu ina kan wannan matsayar.” Lawal ya ce satar mutane domin neman kudin fansa ta zama tamkar sana’a ga…
Read More
Gwamnan Bauchi ya yaba wa Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da samar da tsaro 

Gwamnan Bauchi ya yaba wa Tinubu kan gyare-gyaren tattalin arziki da samar da tsaro 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yabawa jagorancin  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da tsare-tsaren tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa sun kawo sakamako mai kyau da tasiri a fadin Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin Ministan Kudi da Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, tare da Ministan kula da Kiwon Lafiya da Jin Dadin Jama'a, Dr. Muhammad Ali Pate, wadanda suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnati da ke Bauchi. Yayin da yake…
Read More
Atiku ya buƙaci bayani kan tiriliyan N11.2 na NNPC, ya tambayi kuɗaɗen kamfen ɗin Tinubu na 2027

Atiku ya buƙaci bayani kan tiriliyan N11.2 na NNPC, ya tambayi kuɗaɗen kamfen ɗin Tinubu na 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya buƙaci Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC) da ya yi cikakken bayani kan Naira tiriliyan 11.2 da aka rubuta a cikin bayanan kuɗinsa na shekarar 2025 a matsayin kuɗin da gwamnatin tarayya ke binsa. Atiku ya kuma buƙaci Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana duk wani tallafin kuɗi ko na kayan aiki da ’yan kwangilar gwamnati suka bai wa ayyukan yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027. Atiku ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa…
Read More
JAMB za ta kafa cibiyar rubuta jarrabawar UTME a ƙasar Canada a 2027

JAMB za ta kafa cibiyar rubuta jarrabawar UTME a ƙasar Canada a 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta ce tana shirin kafa cibiyar gudanar da jarabawar shiga jami’a ta UTME a Ottawa da ke ƙasar Kanada, wadda ake sa zai fara aiki a shekarar 2027. JAMB ta ce cibiyar za ta bai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a Kanada da sauran sassan Arewacin Amurka damar rubuta jarabawar UTME ba tare da sun dawo domin rubuta jarabawar ba. Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Litinin. Ta ce shirin zai ƙara damar samun…
Read More
Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kotu bisa ƙin bayyana rahoton kwamitin bincikensa

Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kotu bisa ƙin bayyana rahoton kwamitin bincikensa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shigar da ƙara kan Gwamnatin Jihar Sakkwato kan zargin ƙin miƙa masa rahoton Kwamitin Bincike na Shari’a da aka kafa domin binciken ayyukan gwamnatinsa. Tambuwal, wanda a yanzu yake wakiltar Mazaɓar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya mulki jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023. A cikin ƙarar mai lamba SS/133/2026, wadda aka shigar a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato, reshen mai lamba 6, tsohon gwamnan na neman kotu ta umarci gwamnatin jihar ta ba shi kwafin rahoton kwamitin. Tambuwal ya shigar da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta biya bashin albashin watanni takwas da SSANU ke bi

Gwamnatin Tarayya ta biya bashin albashin watanni takwas da SSANU ke bi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗaɗen albashin watanni takwas da mambobin ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU), domin daƙile barazanar shiga yajin aikin da ƙungiyar ke yi. Kwanan nan SSANU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14, inda ta buƙaci a gaggauta biyan sauran bashin albashin da ya taso sakamakon aiwatar da yarjejeniyar FGN/SSANU ta shekarar 2026. ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan Gwamnatin Tarayya ba ta cika buƙatunta cikin wa’adin da ta bayar ba, za ta tilasta mata fara “cikakken yajin aiki mara iyaka” ba tare da ƙarin sanarwa ba. Da yake magana…
Read More
Ya kamata a samar da tsarin bai-ɗaya na cigaban Arewa – Gwamna Uba Sani ga manya yankin

Ya kamata a samar da tsarin bai-ɗaya na cigaban Arewa – Gwamna Uba Sani ga manya yankin

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga jiga-jigan siyasar Arewa da su fi mayar da hankali wajen samar da wani tsari na bai-ɗaya da zai magance matsalolin da yankin ke fuskanta, maimakon mayar da hankali kan neman karɓe iko a matakin tarayya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello suka kai masa ziyarar ban-girma a ranar Laraba, a zauren Majalisar Zartarwa na Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna. Ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa yadda take jan hankalin ’yan siyasar Arewa da masu riƙe da muƙaman gwamnati kan…
Read More
An kama direban da ya kashe ɗan achaɓa ya gudu a Kebbi

An kama direban da ya kashe ɗan achaɓa ya gudu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jami'an 'yan sanda sun sami nasarar kama wani direba da ba a bayyana sunan sa ba wanda ya buge wani mai babur a hanyar Birnin Kebbi zuwa Argungu da ke jihar Kebbi. Ganau Malam Abdullahi Muhammed Dagwaya ya bayyanawa wakilin mu da cewa sun tsaya Sallah a ƙauyen Gidan Hamani ne wannan babbar motar ta zo ta wuce, bayan sun gama Sallah suka fara tafiya, sun kusa shigowa garin Argungu sai suka tarar da wannan motar a gaban su ta ture wannan mai babur ɗin kuma ta ja shi ƙasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar…
Read More
2027: Kwamitin Abdulsalami ya gargaɗi Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan siyasa kan rikici a yaƙin neman zaɓe

2027: Kwamitin Abdulsalami ya gargaɗi Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan siyasa kan rikici a yaƙin neman zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Samar da Zaman Lafiya na ƙasa, wanda tsohon Shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ke jagoranta, tare da Babban Limamin Cocin Katolika, Most Reɓ. Matthew Kukah, a matsayin mai gudanar da shi, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan siyasa kan yin kamfen mai ɗauke da kalaman tayar da hankali ko tunzura jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan rahoton samun wasu al’amura 60 da suka shafi zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar cikin wata guda, ciki…
Read More