ukarofi

11670 Posts
Ibrahim Masari hadimin Tinubú da gwamnan Yobe sun bai wa ƙungiyar Izala ta Sheikh Jingir tallafin N600m

Ibrahim Masari hadimin Tinubú da gwamnan Yobe sun bai wa ƙungiyar Izala ta Sheikh Jingir tallafin N600m

Daga UMAR GARBA a Katsina Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Masari da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, sun yi alƙawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 600 domin gina Jami’ar Fortune da JIBWIS ke ginawa a Jihar Bauchi. Masari da Buni za su bayar da Naira miliyan 300 kowannensu. Sai dai gudummawar ta zo ne a lokacin da ake ta muhawara kan alaƙar siyasa da addini, musamman bayan Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya fito fili yana goyon bayan Shugaba Tinubu da sake zaɓensa a 2027. Jaridar Daily Trust ta…
Read More
2027: Ishaq Elayo zai ceto Nasarawa ta Kudu – Ibrahim Osabwa

2027: Ishaq Elayo zai ceto Nasarawa ta Kudu – Ibrahim Osabwa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hon. Ibrahim Osabwa darakta janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓe ta Injiniya Ishaq Dauda Elayo wato ɗan takarar kujerar sanata na Nasarawa ta Kudu ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress ADC yace ubangidan na sa shi ne ɗan takara da ya dace da zai bai wa mutanen yankin mazaɓar Kudancin jihar wakilci nagari mai ma’ana da magance matsalolin cigaba da ke fuskantar yankin. Osabwa ya bayyana haka ne a wata hira na musamman da ya yi da 'yan jarida a Keana. Yace Injiniya Elayo ya amsa kiran al’ummar yankin da suka daɗe suna kira gare…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta umarci sarakunan gargajiya su gabatar da ra’ayoyin jama’arsu kan kasafin kuɗin 2027

Gwamnatin Zamfara ta umarci sarakunan gargajiya su gabatar da ra’ayoyin jama’arsu kan kasafin kuɗin 2027

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta Jihar Zamfara ta ƙaddamar da shirye-shirye don kimanta kasafin kuɗi na shekarar 2027 tare a taron masu ruwa da tsaki, inda ta yi kira ga majalisun masarautu da sarakunan gargajiya da su gabatar da ra'ayoyin al'ummar su a ranar Juma'a ko kafin Juma'a, 4 ga Satumba, 2026. Taron, wanda aka gudanar a ranar Talata a kwalejin fasaha da kimiyya (ZACAS) da ke Gusau, an yi masa taken "Shirye-shirye a yau, gina Zamfara mai albarka gobe." Da yake buɗe taron, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Farfesa Yahaya Zakari, ya ce…
Read More
Ranar Hausa ta duniya: Kano za ta zama cibiyar bikin Hausawa a gobe

Ranar Hausa ta duniya: Kano za ta zama cibiyar bikin Hausawa a gobe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Yayin da ake saura wasu sa'oi a gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2026, an yi kira ga ɗaukacin al’ummar Hausawa da su fito domin nuna kishin harshensu, tarihinsu da al’adunsu. Za a gudanar da bikin ne a gobe Laraba, 26 ga Agusta 2026, a fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya, Amb. Alh. Sani Adamu Geza Garkuwan Hausawan duniya, a Kano. Shugaban majalisar masarauta ta Arewar mu duniyar mu African Chiefdom and Council, Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, shi ne ya yi kiran, inda ya bayyana bikin a matsayin wata muhimmiyar dama ta…
Read More
ADC da CSO na Gwamnan Katsina suna hannun jami’an tsaro a Abuja

ADC da CSO na Gwamnan Katsina suna hannun jami’an tsaro a Abuja

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An tsare babban dogarin Gwamnan Katsina (ADC) da kuma babban jami’in tsaron gwamnan (CSO) a hedikwatar ’yan sanda da kuma ta hukumar DSS da ke Abuja kamar yadda jaridar “Katsina Times ta bayyana. Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an biyu suna hannun jami’an tsaro domin amsa tambayoyi. Rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne bayan lalata wasu manyan allunan tallace-tallacen siyasa da ke kan hanyar shatale-talen Modoji zuwa gidan Gwamnatin Katsina. Wasu daga cikin allunan na ɗauke da hotunan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan ’yan siyasa, ciki har da mai bai…
Read More
Zuwa ga masu shirin aure (III)

Zuwa ga masu shirin aure (III)

Assalamu alaikum. Abu na uku da na ke son nuni da shi, shi ne muhimmancin sassauci da yafe wa juna, duk da cewa sassauci ba abu ne da ke da kyau a dukkan lokuta ba na rayuwa ba, to amma mafi kyawun sassauci da yafuwa akan yi shi ne a rayuwa ta aure. Don kuwa, a matsayinku na sabbin amare da angwaye, za su ci daba da fahimtar junanku da kuma ɗabi'un juna kusan kullum. To lalle kada irin waɗannan sabbin abubuwa su kashe muku gwiwa, don kuwa babu wani mutum a duniyan nan (a halin yanzu) da ya cika…
Read More
2027: Abin da ya sa zan dawo da tallafin fetur idan na ci zaɓe – Atiku

2027: Abin da ya sa zan dawo da tallafin fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba, inda ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur a farko ba, amma matsalar ita ce yadda gwamnati ta yi amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin. Ya ce ya kamata kuɗin da aka samu daga…
Read More
Mambayya sai mai nazari

Mambayya sai mai nazari

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Malam Aminu Kano bai gina gidansa “Mambayya” a 1968 don taron ranar zallawa ba. Wallahi ko sunan gidan ba su iya rubutawa daidai ba! maimakon Mam-bayya sai su ka maka Man-bayya. ƙarshe na ga Zallawa sun bayyana inda za su yi taron ranarsu ta zallanci da fakewa da wai ranar Hausa a gidan MAMBAYYA inda su ka rubuta MANBAYYA da “N” maimakon “M” don dama ’yan arufta ne ba sa iya rubutu ko magana da Hausa tiryan-tiryan sai sun wurga Turanci. Hausa ba layinsu ba ne sam. MAMBAYYA gidan marigayi Malam Aminu Kano ne da ya…
Read More
Yadda ’yan siyasa ke jefa matasa bangar soshiyal midiya

Yadda ’yan siyasa ke jefa matasa bangar soshiyal midiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ana ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa a ƙasar nan, yayin da ake ƙara kusantar Babban Zaɓe na shekarar 2027. 'Yan siyasa, musamman sabbin yanka masu neman a san da su da gwamnoni masu neman tazarce suna ta ƙoƙarin sauyin sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Mun ga yadda jihohi irin su Kano, Filato, Adamawa, Taraba da Zamfara gwamnoninsu suka yi sauyin jam'iyya zuwa babbar jam’iyya mai mulki ta APC. Matakin da wasu ke kallo a matsayin wayon a ci ne, wato kowa ƙoƙari yake yi a dama da shi a siyasar tarayya, a…
Read More
Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina

Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sojojin 17 Bridge sun sami nasarar kama ƙasurgumin ɗan bindiga Sunusi Mai Gilas a yayin da sojojin suka kai samame a ƙaramar hukumar Kurfi. Mai gilas na ɗaya daga kwamandan 'yan bindigan a dajin Danmusa wanda dama rundunar sojoji ke neman sa bisa zargin aikata ta'addanci da manyan laifuka a yankin na Ɗanmusa. Wannan kame ya nuna nasarar da rundunar sojoji ke samu a ƙoƙarin da suke na tarwatsa sansanonin 'yan bindiga da hana su kai wa da komowa a tsakankanin al'umma. Yanzu jami'an tsaro sun fi mayar da hankali wajen gano wurare da dazuka…
Read More